10

58 0 0
                                    

Washe gari bayan sallah asuba su fareeda basu koma bacci ba,wanka tayi aka fara make up,mama kuma da khady don agidan ta kwana suka hada komai na fareeda wuri daya har da lefenta,
Yau atamfa tasa dikin borno da straight sket aciki ya mata kyau sosai yau din ma gyale ce navy blue mai sequence khady ta dauko mata "amma ba dai dashi xani Abuja ba koh" fareedah ta tambayeta "dashi xaki fa don duk mun hada kayan wuri daya bbu halin ciro hijabi" khady ta bata amsa tana bude kulolin abinci da mami ta aiko dashi fareeda xata kara magana mama ta leko "kuyi sauri ku gama karyawa mami wai xata aiko adauke ku" duk da ba haka fareeda taso ba amma ta hakura ta yafe gyalen haka,suna kan karyawa salman ya shigo da anty bilkisu bayan su gama gaisawa da mama salman ya fara fita da kaya yana sawa a boot mama ce ta kalli fareeda "toh mama na allah ya bada sa'a kuma ya baku xaman lfy don allah kiyi masa BIYAYYA fiye da yanda kk mani yi nayi bari na bari,karatun da kk sa gaba inkinje makarantar dan allah kiyishi duk da nasan baki da wasa amma ki kara kula shikenan tashi ku tafi Allah ya tsare ya kuma maki albarka" banda kuka bbu abinda fareeda take har mama ta gama maganarta rungume mama tayi ta kara fashewa da sabuwar kuka shafa bayanta mama tayi"its okay mana kar kuma ki bata kwalliyar ta mami ta Zane ki" turo baki tayi ta fara murmushi nana ma ta rungumeta tana kuka da kyar mama ta rabasu suka masu salllama sai gidan mami

Amota ma bata dai na kukar ba tun khady na gyara mata make up din ta daina har suka isa gidan bbu kowa awaje sai motar da deen yaxo dashi jiya awaje,parking salman yayi gefen motar sukuma suka fito anty amarya na rike da hannun fareeda salman kuma ya bude boot yana sauke kayan yana maidawa na deen din,
Tsakar gidan ma bbu kowa bangaren mami suka nufa suna shiga aka fara buda yan uwan ne da abokan arziki mata xasu kai su gama banda mami,anty amarya da kuma matar ahmad wacce aka gayyata ita ma sai su da suka shigo ynxu kan fareeda akasa har suka karaso kan cafet ta xauna mami tayi saurin dago ta ta maida ta kan kujera tsakiyarta da anty amarya sai da aka mata komai na buden kai kan aka watse falon ya dawo daga mami,anty amarya anty bilkisu khady sai hafsat matar ahmad,,,,,khady na kwashe kudin da turaren da akayi liki dashi deen ya shigo da ahmad,nadia na biye dasu,
bayan sun gaisa mami tace "toh ga amana nan,ka xamo mai adalci da hakuri, babba ya kama girmansa karami kuma ya ba babba girman sa" ta karisa maganar tana kallon nadia wacce ita bata fahimci ma inda maganarta ya dosa ba,,,,,,,"toh anty amarya gareki" mami ta kuma fada tana kallon anty amarya "ai mami kin gama fadin komai sai dai fatan mu allah ya bada xaman lfy" duk suka amsa da ameen

Deen ne ya dubi agogon hannunsa ya mike "mami xamu tafi kar muyi dare ahanya " nadia ma ta mike " toh kuje  ga ta nan xuwa" cewar anty amarya tana Jan fareeda kitchen su kuma suka fita su mami da anty bilkisu suka rakasu har mota

"Shanye ki ban kofin" tana mika mata cup din bbu halin musu ta amsa kawai ta shanye ta bata kofin "yauwa fareeda na sa maki wasu a handbag dinki xaki gani kuma pls kiyi using dinsu kinji" daga mata kai kawai tayi "toh muje" sukayi hanyar waje nan ma su kawai ake jira deen ke kan driver seat sai ahmad gefen sai nadia a baya saitin deen ita kuma aka bude mata baya saitin ahmad kanta akasa har anty bilkisu ta rufe mata kofar suna daga masu hannu ya ja masu motar
Ahanya bbu wanda yayi magana har suka bar garin kaduna suka shiga zaria nan ne ma ahmad ya tambayeta in xata ci wani abu tace aa nadia banda danna wayarta bbu abinda ta ke sai bacci,

Ahankali deen ke leka fareeda ta madubi tun idon ta biyu har ta fara bacci murmushi ya dan yi ya cigaba da tuki sai da sukayi nisa ahmad ya amshi tukin basu isa Abuja ba sai bayan la'asar agajiya suka karasa gida bayan sun sauke ahmad horn yayi mai gadi ya bude masu gate sai da yayi parking duk suka fito
nadia ce tai gaba sai Fareeda wacce ta tsaya abakin kofar shiga falon don bata san inda xata ba,sai da deen ya gama magana da mai gadi kan ya shigo da kayansu kan ya karaso gun ta "shiga mana" tura kofar tayi shima ya bi bayanta cikin falon ta tsaya shi kuma ya haura sama sai daya kai karshe ya juyo dan bai ji alamunta a bayanshi ba,,,,,a can kasa ya hango ta "come up" yafada yana kallonta ahankali ta hauro sai ta ya nuna mata dakin dake gefen hagun nashi yace "dis is ur room,kiyi wanka kiyi sallah xan kawo abinci ynxu" daga masa kai kawai tayi ya rufe kofar.

Akan gadon ta cire kayanta bayan ta aje Jakarta ta shiga wanka daga nan ta dauro alwala koh data fito ta ga duk an shigo mata da kayanta
doguwar riga ta sa sai hijabi ta tada sallah tana kan sallaya yayi sallama ya shigo aje mata leda yayi kawai ya juya ya fita, mikewa tayi don tun karin safe bata ci komai ba take away ne mai dauke da fried rice and chicken sai ruwan gora da 5alive na gora sai data ci ta koshi ta kwashe ledar ta saka hijabinta ta sauka kasa ,,,, gefen dining da hangi wata kofa ta nufa alamar nan ne kitchen din koh data bude kitchen din bbu datti sai dai kurar da baxa arasa ba nan ta sa ledar a dustbin ta dau tsintsiya ta fara share kitchen din sai data gama gyara kitchen din ta fito nadia ta gani a falon ta na shan ice cream kallo daya ta mata ta haura sama  "ki xo ki yi clearing wurin nan it's a bit dirty" ta jiyo muryar nadia bata tsaya ba ta cigaba da tafiya har ta shige dakin ta baki bude nadia ta bita da kallo har ta bace mata

Deen ne ya shigo falon alamar daga masallaci yake dan sanye yake da jallabiya milk "babe wai I don't understand y u took dis girl upstairs bayan ga daki anan kasa" zama yayi gefen ta
"I don't understand why would she b down here" ya tambayeta "kenan matsayinta daya da mu kenan ace ina matar gida ita kuma maid amma ina sama tana sama gskya I don't like it" tayi maganar tana sounding serious dan murmushi yayi yace"shes also matar gida fa nadia" kallon banxa ta masa "matar gida kuma when did dat one happen" "ai abin da ya kai mu kd kenan" yana fadin haka ya mike saurin riko rigar shi tayi"hey u r joking right" "no am not" ya buge hannunta ya haura sama dakin shi ya shiga bai kai ga rufe kofar ba ita ma ta shigo "aw take anything but not sharing u in bed wid her" ta fada tana shafa shi bai ce mata komai ba sai cire rigarsa da yake rungume shi tayi tace" kaji babe " daga mata kai kawai yayi ya kwanta kan gadon kashe hasken dakin tayi ta haye kanshi
Washe gari Monday koh da fareeda tayi sallar asuba bata koma ba kasa ta sauka ta gyara gidan tasa turare ta dafa shayi ta kuma soya dankali da kwai wanda duk a store din kitchen din ta gani

Sai 7am daidai ta gama bayi ta shiga tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga ta atamfa sai hijabin ta kasa ta sauka falon bbu kowa xama tayi kan dinning din tana tunanin wat to do next bata jima da xama ba taji footsteps alamar mutum na saukowa daga sama deen ne sanye cikin yaji mai laushi sky blue yayi kyau sosai agogon hannunsa yake dubawa bai ma kula da ita ba "ina kwana " tace dashi "lfy uhm get ready muje school din " yace da ita yana duba wayarsa mikewa tayi "nayi abinci " ta furta ahankali kallon kan dinning din yayi karaso wa yayi don dama abincin xai je ya siyo su karya kamin su tafi "u cooked dis yourself " daga masa kai tayi Jan kujera yayi ya xauna ta fara xuba masa ita ma ta xuba suka fara ci,
sosai ya ci abinci kan ya mike" ki shirya ki sameni a mota" kallon kanta tayi "jakata kawai xan dauko xai papers dina" kallonta yayi daga sama har kasa "u are going out like dis" ya nuna ta kallon kanta tayi again "bai yi bane " "go change and don't waste my tym" ya juya ya fita sama ta haura rasa kayan da zata sa tayi daga karshe ta dauko abaya ta saka ta yafe veil din tayi kyau duk da hoda kawai ta shafa sai lip glows papers dinta tasa ajakarta ta fito

Mommah ❤️

BIYAYYATA Where stories live. Discover now