Dan daure fuska yayi"ya akayi kk shigo nan" batai masa magana ba ta mike zaune "sannu da xuwa "
Banxa ya mata ya je ya ja window ya dawo ya kwanta ya juya mata baya
Ganin bai kulata ba ya sa ta rungumeshi ta baya ta shafa fuskarsa "baby kayi hkri mana pls" nan ma shuru
Ta dauki akalla minti ashirin tana bashi hakuri amma bai kulata ba ganin hakan ya sa ita ma ta hau mikewa tayi
Ta dauki wayarta da ta soma kiciniyar sa hijabi har ta sauka kan gadon yayi wuff ya cafke ta
"Ka sakeni nace ka sakeni"ta fada tana kokarin kwace kanta
Kara riko ta yayi gam yace jawo ta kan gadon "da irin wannan dressing haka ai dole na hkra"
Yana maganar yana mata dariya turo baki tayi ya kuma cewa "ai nima na dan dana Jan ajin ne"😄 😆
Ahaka yayi mata wayau ya su suka faranta wa junan su adaren
Khady
Har aka kawo ta aka watse bata motsa ba tana nan xauna tsakiyar gadon ta har ya shigoSai da sukayi sallah kan ya bude masu gazar da ya siyo da 5alive suka ci suka yi nak
Sannan sukayi shirin kwanciya ahmad ya lura da yanda gaba daya ta tashi hankalin ta amma sai ya share
Banda janta da yayi ta kwanta jikinshi bai kuma mata komai ba har bacci ya kwashe su
Deen da fareeda kwana biyu suka kara suka fara shirin komawa Abuja bayan sun je sun gaida mama kuma sukai mata siyayya kala kala har da nanah
Bayan koma warsu da kwana biyu nadia ma ta dawo sosai hankalinta ya tashi ganin fareeda da ciki kuma ga kulawa ta musamman dayake bata
Fareeda nata rainon cikin ta dake da wata hudu da sati biyu ynxu gashi sun yi resuming a school haka take xuwa ga ciki ga makaranta
Sai da khady da ahmad sukai wata daya cir a kd kan ya tattaro ta suka dawo Abuja
Ganin khady ta dawo abuja fareeda ta kara sakin jikin nan fa suka soma sabuwar rayuwa mai cike da annashuwa
Nadia
Ba shiri ta koma asibiti ta cire implant din dake jikin ta,,,ita fa anan duka gasa take da fareedaAkwana atashi bbu wuya gun allah fareeda ta shiga watan haihuwa ita kuma khady tana watan ta ta biyu
Sauran watanni kawai ya rage wa fareeda ta karasa karatun ta,wata daren juma'a tana bacci don ita da wuri take bacci yau deen adakin nadia yake
Tun kan ta kwanta take jin dan ciwo akasan marar ta amma bata fada ba Sai can cikin dare
Tun tana jurewa har ta kasa ta soma kuka tana kiran allah da kyar ta lalibo wayar ta ta soma niman layin deen
Kira na biyu ya daga tare da sauka daga gadon ya sanya jallabiyar sa yana fitowa tun kan tayi masa bayani
Yana shigowa dakin ya ganta azube akasa tana fam kuka tana dafe da cikin bai wata wata ba ya bude wardrobe ya dauko hijabinta ya sa mata
Keys kawai ya dauka ya dauke ta ya sa amota ita dai nadia dana biye dashi bace masa komai ba
Don tun fitar sa daga dakin ita ma ta bi bayanshi tana kallon irin azabar da fareeda ke ciki gaba daya tausayin ta ya kamata
"Babe xan je da kai" ta fada tana kallonsa "toh" kawai yace da ita ya shige motar ita ba ta bude gefensa ta shiga
Suna xuwa asibitin aka shigar da ita labour room su kuma suka xauna a bencin dake wurin
Ihun da kuma azabar da masu labour ke yi ya tayar da hankalin nadia gam ta kama hannayensa ta rike shima ya rike don gaba daya hankalinsa atashe
Bayan 40mins nurse tafito tace dubeshi "ina kayan babyn" lah suka bude baki sabagen tashin hankali har sun manta da kayan babyn
"Bari inje in dauko dan allah mantawa nayi" murmushi nurse din tayi tace toh kayi sauri dan allah
Kafin asuba har angama shirya fareeda da bby boy dinsu ankai su dakin hutawa
Kallon bbyn kawai nadia take tana kallon fareeda don ita tunda take bata taba xuwa asibiti bangaren labour balle tasan ya akeji
Dariya deen yayi yace" nadia lfy kuwa" "babe fareeda tayi kokari fa ynxu ita ta haifo wannan babyn " ita ma fareeda murmushi tayi
"Ga zahiri kina gani " ya bata amsa kiran mami da ya shigo wayar sa ne ya daga yana sanar da su haihuwar fareeda
Wasa wasa har suka bar asibitin nadia bata bar kowa ya dauki babyn nan ba koh da suka isa gida
Makociyarsu ce wacce ta dan manyanta deen yayi wa mai gidan bayani ta xo ta soma wa fareeda wanka da yaro kafin mama koh anty amarya suxo
Tunda basu tsayar wa xai taho ba kwana hudu da haihuwa anty amarya da mama sai nanah suka xo
Nan fa gidan ya kara cika sosai anty amarya da mama ke kula da fareeda da bbyn ta
Wanda yawanci in ba wanka ba koh shan nono koh bacci nadia na dauke dashi
Tun abin na bawa kowa mamaki har ya daina ana gobe suna anty bilkisu ta iso ita ma khady ta xo gidan bayan xuwan barkan da tayi anan xata kwana nan acika hidimar suna
Ranar suna yaro yaci suna Ibrahim mahaifin fareeda ana kiransa da khaleel
Bayan suna da kwana biyu duk aka watse har da su mama don ganin yanda maman abul waton makociyarsu ke kula da ita da bbyn
Sosai fareeda ta sake da nadia suka cigaba da kula khaleel
Haka rayuwarsu ta cigaba khaleel na da shekara daya fareeda ta kammala karatun ta tayi service anan abuja
Yayin da ta bar wa nadia raino har sai ta dawo sosai deen ke jin dadin yanda matan sa suka hade kai kuma nadia ta canxa sosai
Hatta kasuwancin ta ma ynxu ta koma yi online ta natsu
Khady ma ta haifi yarta mai kama da mami sak nan akayi wa mami takwara
Khaleel na da she kara biyu ita ma ta suma ciki ta haifo masu baby girl amma ita Cs akai mata don tasha wahala sosai
Nan yarinyar taci suna kausar,sai da suka haifa wa deen yara har biyar fareeda na da uku nadia biyu
Duk sallah sai anan kaduna suke yinta da yara kowa yayi makakin sauyawar nadia amma ita koh ajinta
Nanah mama ynxu ta girma sun dai daita da usman aka sha biki
Nan shine karshen Littafin BIYAYYATA nagode da karanta book dina da kk da kuma masu following dina
Insha allah sabon Littafina mai sunan Babynah xai fito on d 1st of September
So pls like comment follow and shareKarku manta akullum ku ke karfafa wa marubuta gyuwa wajen rabuto maku labarai masu dadi da fadakarwa
Mommah ❤️
