19

95 1 0
                                    

BIYAYYATA

Deen
Tuki yake cikin nishadi sosai yake jin dadin wannan sabuwar yanayin ya tsinci kansa ashe auren yake da dadi shi bai sani ba sai yau

Har ya isa kasuwa parking kawai yayi ya soma shiga gun ahmad

Ganin yana meeting da staff dinsa ya daga masa hannu alamar in ya gama yana office dinsa

Yana xaune a office din ya ciro wayarsa ya nimi layin hajiyar sa waton anty amarya bugu daya ta daga

"lallai son daga baka yarinya sai muka jika shiru kamar anyi ruwa an dauke"

Dariya yayi har tana iya jiyoshi "hajia ina kwana " " bazan amsa ba watan ma dariya na baka koh"

"No kawai dai amma ayi hkri a amsa gaisuwata" yafada cikin magiya

"Naji antashi lfy ya iyalin" "lfy lau alhamdulillah ya kowa da kowa"

"Duk muna lfy toh ya ina yarinyar mu take"

"Tana lfy" ya bata amsa kai tsaye

Duk da ba hakan ta soji ba ta so yace mata ynxu rayuwarsa ba kamar da ba

Hira suka dan taba har da fada mai salman ya kammala service dinsan an tura sa aiki nan abuja

"Toh allah ya kawo shi lfy " "ameen" kan yayi mata sallama

Ahmad ne yashigo office din ya kalli deen"shege abokina naga sai wani fara'a kk yau"

Dan bata fuska deen yayi"meka gani"

'"Har sai ka wani tambayeni ai it's very obvious " ya bashi amsa yana dariya

Deen bai kara cewa komai don Ahmad din might b ryt tunda koshi kansa ya san yau daban yakeji

Canxa topic din yayi"ina ganin bayan sallah in allah ya kaimu xaniyi tafiya"

Dakatawa ahmad yayi da laptop din ta yake latsawa "ina xakaje" "Paris koh new York it depends on her choice" ya fada yana shafa shajen fuskarsa

Tabe baki ahmad yayi "kai wai har ynxu baka gaji da yawo da nadia ba"

Harara sa yayi"eh ban gaji ba tunda ita kadai ce matata ynxu "

"Masha allah ni ai sai ynxu na gane mutumina ashe da amaryarka kk" yana dariya

Fareeda
Wardrobe dinsa ta bude ta sa fuskarta ciki tana shakar kamshin deen sosai saukin soyayya ke diban ta kofar da aka bude ne yasa ta yi saurin rufe Wardrobe din tana ja da baya

Nadia ce a tsaye tana kallonta"toh yar gidan barayi hala sata xaki masa koh"

Bata ce komai ba don she don't even have d strength to argue kayan ledar ta kwasa ta fita

Ganin yanda ta ke tafiya ahankali yasa nadia ta kura mata ido "No ba dai ba dai ba dai deen dinta ya? Rufe bakinta tayi ta tafin hannunta

Laundry basket dinsa ta nufa nan ta ci karo da bedsheets din jiya dagawa tayi ta na dubawa aiko taci karo da abinda takeson gani waton jini

Ball tayi da basket din ta fito a fusace kasa ta nufa bbu kowa don tuni fareeda ta koma dakinta

Hajjo ce ta fito da broom da mopper alamar so take ta fara aikinta

"Anty sannu da fitowa"hajjo ta gaisheta

Banxa ta masa ta kuma haura sama direct dakin Fareeda ta tafi tana kwankwasa kofar kamar mahaukaciya

Fareeda
Tunda ta ga nadia tasan xata nimeta da fada don haka koh da taje kai kayan ledar kasa ta hangi hajjo mika mata tayi tace don allah ta sa mata a dustbin

Ta koma dakinta ta sa key kwanciya tayi kan gado
Tana jin ta sanda take mata knocking amma ta mata banxa sai ma ta ciro wayar ta da tasa acaji

Samun kanta tayi da neman nmbr deen kirar na shiga tayi saurin katse ta "haba fareeda control yourself mana karfa ya raina ki" duk cikin xuci take xancen ta

Deen
Suna hira da ahmad dake aiki kan laptop dinsa shi kuma yana latsa wayar sa ya ga flashing a wayar sa ganin fareeda ce ya gyara xama ya sake niman layin ta

Tana kwance ta ga kiransa innalillahi kar dai mtn sun mika kirana ni kam nace beeb suka mai 😆 🤣

Katse kiran tayi ta shiga yi masa message kamar haka"ni karka kira" ta tura masa

Yana kokarin kara kiranta atunaninsa network ce ta katse ta yaga sakonta murmushi yayi ya kuma gyara xamansa kan kujerar shima ya mata sako

Deen:toh me kk son nayi
Fareeda:muyi magana ta nan
Deen:fada min me kk so
Fareeda:ni ban son komai
Murmushi yayi har sai da ahmad ya dago ya kalleshi

Deen:do u want me to come kinji dadin jiya kenan
Fareeda:ni ni yaushe na fada maka haka
Deen:ai ba sai kin fada ba
Sosai hirar tasu ke mata dadi ji take ina ma yana gefenta
Fareeda:ni dai ynxu yaushe xaka dawo
Deen:yaushe kk son na dawo kuma mexaki aje min
Fareeda:me kk so na aje maka
Deen:you
Wani yarr fareeda taji "ni kuma" "yes in ba hakan ni da dawowa sai can cikin dare"
Turo baki tayi kamar agabansa take "ni koh "

"eh ke " 😅 😂 ba fashi ya fadi hakan ba nice nan 😄 😆

"Toh naji xan dawo da wuri mkk so na taho maki dashi"

Kusan minti 3 shuru bbu reply har ya cire rai sai yaga ta turo "you and ice cream "

Sabida dadi bai san sanda ya daki table din ahmad ba yana dariya

kamar wani wawa haka ahmad ya saki baki galala yana kallon deen "kai nifa ban son iskanci tashi ka koma naka office din dan bura uba kai"

"Kai wllh ban san haka yaran nan suka iya soyayya ba" deen ya fada

"Eh ba shakka dole kace haka hala ka dibe masu yarinyar shiyasa"

Harara ya yi wa ahmad ya cigaba da latsa wayarsa "dan rainin wayau" cewar ahmad yana cigaba da aikin sa

Fareeda
Mamakin kanta take wai ita ce yau ke soyayya kuma ba kowa ba sai hayatuddeen dodon gidansu khady gyara kwanciyarta tayi akan zuwa 12 sai ta tashi ta dafa masu abincin rana

Nadia
Haushi taji sosai ta fareeda bata kulata ba dakinta ta nufa fuuu wanka tayi shaf shaf ta shirya cikin doguwar riga ta atamfa ta sa karamin gyale akanta ta dau Jakarta ta shige motar ta ta bar gidan

Fareeda
Sai 11:45 ta farka fuska kawai ta wanke ta sa hijabinta ta sauko kasa kamar yanda tayi zato bbu kowa aciki

Sai data shiga kitchen ne ma ta jiyo muryar hajjo ta baya ta dan leketa ta ga me takeyi

wanki take kuma ba na kowa ba sai na nadia

Bata mata magana ba ta shiga aikin daura abincin ta fried rice and pepper chicken tayi sai cos low

Bata gama ba sai karfe 1 dai dai sai data kai komai dakinsa ta aje kan ta nufi daki taje tayi wanka tayi sallah

ta sauya kaya xuwa sky blue crop top an rubutun"hello baby " agaban rigar sai black pencil jeans ta tufke gashin ta abaya

Kan gado ta xauna ta fara niman layinsa amma har kiran ya tsinke bai daga ba sai data masa miss call har biyu daga karshe jefar da wayar kawai tayi tana mai jin haushin kanta da take nuna masa so haka

Deen
Ya shanyo kwanan gidan sa ne yaji ana kiran sallah agefen gidan yayi parking kan ya wuce masallaci don sallah

Sun idar kenan yaji ringing din wayar sai daya fito masallacin ya duba ganin ana sake kira

Murmushi kawai yayi ya shige motar yayi wa mai gadi horn

Mommah

BIYAYYATA Where stories live. Discover now