Murmushi anty amarya tayi tace wllh mami na dade ina son yin maganar nan amma allah bai nufa ba gashi kin rigani yi ai ni dan gidana na bukatar wani auren mai sunan aure"
Da alamu dai kun san abinda ke faruwa ni kadai aka bari I duhu koh cewar abba yana kallonsu da murmushi mai sanyi don yana jin dadin zaman lfy da hadin kan su
Dariya mami tayi bbu wani duhu abba kawai dai mu muka halin da dan mu ke ciki
Kwarai kuwa cewar anty amarya
Naji naji shikenan toh shi hayatun yace yana son ta har xai aureta ne koh kuma ku kk zaba mai hakan
Ya tambayesu duk da shi ma bai gane wannan auren da hayatun yayi ba ace koh xuwa gida gaida su bata yi duk xuwan da yake yi shi kadai ne ba aji su ba amma kowa ya gan su yasan kawai xaman ake tun ba hayatun ba da kallo daya xaka masa ka gane bai samu kula irin na masu aureAbba bai ce ba amma hakan shi xai kawo wa dan mu farin ciki da natsuwa don yarinyar da natsuwa ga BIYAYYA
Haka su kai ta kawo masa hujjoji har ya amince akan suje su sami maman in tayarda toh sai a fara nima masa,(ance xaman lfy tsakanin kishiyoyi sai iyayen mu toh muma muna rokon allah ya bamu ikon koyi dasu )
Haka akayi mami da anty amarya har gida suka samu mama da maganar tayi farin ciki sosai amma ta nuna masu basu da kowa anan sai dangin babban su fareedah wanda suke gujeta tun yana da ran,bata tunanin xasu saurareta akan komai nata balle na ya'ayanta
Karki damu mama komai xai xo mana cikin sauki insha allahu ke dai izininki muke nima sai ki bar mana sauran cewar mami
Toh amma duk da ko na amince abin da kamar wuyar kuma kunga ita fareedah karatu ta dauko har can fa Abuja cewar mama dauke da damuwa afuskarta
Ai fareedar mai sauki ne mama karatu kuma ai daman shi din acan yake da xama kinga kenan faduwa ta xo dai dai da xama sai tayi karatunta da aurenta
"Ynxu usman shikenan abubuwan da xata bukata koh"
Iyasu kenan fareeda amma waxai rakaki can cewar usman yana gyara xaman saka kujerar "ni kadai xanje duk da ma mama bata gama yarje min ba tafada tana canxa fuskartaInsha allahu ma xata barki koh dai na je na fada mata xan rakaki ne har can
Kallonsa tayi ganin bada wasa yake ba "aa usman ba sai anyi haka ba ni ba sai ka je ba
Wllh xanyi iya binki fareeda kema kin san ban wasa da duk al'amuranki ba koh pls ki bari na rakaki da kin gama komai kinyi settle down sai na dawo ya fada da fuskar tausayi
Aa usman ka barshi kawai bara naje gida kar mama tajini shuru xan mata kitso ne tafada tana mikewa bai ce komai ba har fice daga shagon shi
Usman dan saurayine mai shekaru 25,wanda ya gama karatunsa rashin aiki yasa ya bude shagon photocopy ya fara haduwa da fareeda ne a sanda ta xo yin passport a shagonshi na photocopy tun aranar yaji ta burgeshi canji ya hadasu yace ta dawo ta karba don dai yasamu ya kara ganinta tun bata kulashi har taxo suka fara gaisawa har suka saba shi yake mata komai na makaranta har ta samu admission ynxu sonta yake har ya kai ga ya furta mata amma tace masa karatu ne gaban ta sai ta gama xatayi wata soyayya bai yi fushi ba yace a yi zumunci kafin nan allah yayi ta gama wannan kenan.
Tana shiga gidansu nana ta tare ta azaure adda kin san me "sai kin fada tana mai wucewa ciki
Jan ta nana kuma yi baya tace su hajia sun xo akan batun makarantarki cak fareedah ta tsaya tana kallon taDan allah me tace masu toh tafada ta kamo hannun nanah
Ki bari kyaji daga bakinta nana ta fada ta gudu cikin gidan da harara fareeda ta bita ita ma ta shige cikin gidan
*abuja*
Jibi xanje kaduna ki shirya mu je " deen ya fada yana mai shafa gashin kan nadia dake kwance ajikinshiShuru bata ce komai har na tsawon minti biyar " baki ce komai ba nadee
Tashi tayi daga jikinshi tace babe kasan I have things to do anan koh
Bai ce mata komai ya mike yayi bayi,bin shi da kallo tayi ta ja tsaki ta koma ta kwanta
Nadia buhari diya ce daya tilo gun iyayenta,yayin da babanta mai kudi ne sosai,wanda ake iya sa shi a layin masu kudin abuja,nadia fara ce sosai wacce hakan bai hanata karawa da mai ba amma mayukan masu tsada wanda xaka ga har hasken ta ya fita daban da na farare ya koma ja,tana da kyau amma ba can ba,siririya ce doguwa mai son ado da kwalliya,a kasar waje tayi karatunta inda anan ta hadu da deen yayinda shi kuma yaje wani seminal na yan kasuwa a kasar,abin ya bata mamaki don bata taba ganin dan Nigeria mai kyawun halitta irin shi ba,chocolate color ne shi mai sheki,ga brown eyes da pink lips mai laushi ga gashin kansa baki wuluk wanda ya sha askin waves sanye cikin sky blue suit,white long sleeves and a royal blue tie yayi kyau sosai tun anan ta fara binshi har hotel din daya sauka tun yana yarfa ta don shi ba mai son muamala da mace bane har ya fara tankata tun a waje take son bashi kanta sabida nuna masa da tayi tana son sa da son kasancewa dashi yace mata aa ta bari sai sunyi aure ahaka har aka fara nima masa auren ta duk da mami da anty amarya basu yarda da tarbiyar nadia ba koh gidan taxo su ke lallaba ba ita ba,xama take kan kujera ai mata komai,daga ita har familynsu gani suke deen ya hadu ta ko ina amma banda inda ya fito waton iyayensa,su mami sun fahimci haka amma abba yace ai da ita xai xauna ba da danginta ba ahaka akayi aure har rana irin tayau koh hidima ta taso agidan koh dangi nadia bata zuwa balle ziyara koh ta wayane.
Hayatuddeen dana kirki da hakuri amma ba komai yake dauka ba,bai son raini da surutu,hatta nadia kyaleta yake yi son shi sai an kaishi bango yake hukunta mutum,baya son ya ga mutum mai rawar kai nadia na jin dadin xama dashi ne sakamakon ta lura yana biya mata bukata koh da bai so ba tara da sanin cewa tara ta kawai yake kafin ta cika ya watsa ta lol.
*kaduna*
Yau kwana hudu kenan da zuwansu mami gun mama tun fareeda najiran taji ance ta hada kaya sai abuja amma shuru kuma bata son tada maganar mama tayi fushi tace ta fasa.Da daddare bayan sun gama cin abinci nana na tattara kwanukan mama tace "fareeda har ynxu kina da muradin yin karatun nan abuja" damm gaban ta ya fadi don bata san me xa afada mata ba "eh mama ina so" ta fada ahankali kamar mai roko "na amince amma da sharadi daya" kallon mama tayi ganin har yanxu bbu alamun wasa kan fuskarta mama ta cigaba
Da auren ki xakije "aure aure aure fa mama da wa kenan ni da ban da kowa kuma ina ni ina aure ni da xanje karatu" magana kawai take bata gane me take fadi ita kanta
" ki amince ne koh aa" shuru tayi don kanta ya kulle wani irin aure kuma saboda xatayi karatu shi ne xa ahada ta da wani can wai aure tab di shurun da tayi ne yasa mama cewa tashi kije kiyi tunani gobe xan ji amsar taki
Tana gaman fadin haka ta mike ta shiga daki,anan fareeda ta ja hijabin ta ta lullube don sanyin da ta ji kamar tafara ji nana dake kofar dakin bata shigo ba ta daga labulai tace ke adda meye na tunani anan kawai ki amince tunda kina son karatun
Shuru tayi bata ce komai ba ta saka hijabinta ta fice sai shagon usman.
Shin Deen xai amince kuwa ?
Me fareedah xatayi gun usman?
Shin nadia xata xauna da kishiya ?
Ku biyo muji yanda xa akaya a littafin BIYAYYATALike comment and share
Mommah ❤️