Sai data sanyo hijabi kan ta sauko suka tafi,tun daga wannan lokaci fareeda take juya deen ahannunta shi kuma yana biye meta don yana jin dadin abubuwan da take masa ni kam nace abinka da wanda bai saba ba
Ahaka suka kwashi sati guda suna abu daya tun fareeda na yi da sunan kwatar yanci har ya bi jikinta
Sosai take son jinta kusa da deen wanda shima abangarensa hakane
Nadia xuba masu ido tayi kamar yanda kawarta hafsa ta bata shawara
Ayau deen ya yanke shawarar dai daita gidan sa yayin da yau fareeda ta yi paper na karshe na first semester dinta haka xalika ita ma nadia yau take sammanin ganin hafsa don jiya da daddare suka shigo garin
Da wuri fareeda ta dawo bayan exams dinta wacce ta kasance Friday
Tana aje bag dinta ta tube hijabi ta dawo kitchen don dora abincin rana hajjo ta tadda akitchen din ita girkin take yi "ina wuni"
"Lfy lau sannu da aiki" ita ma ta amsa mata ta mai debo abubuwan da xata bukata daga store
"Anty abinci kuma xaki daura " hajjo ta tambayeta ganin tana kokarin yin hakan
"Eh da wani abu ne" "ai ba sai kinyi ba na riga dana daura"
"Naga ai mai gidan bai cin abincin da kk dafa koh"
"Eh amma ai kema koh kinyi baxai ci ba " wars ido waje tayi "inji wa" fareeda ta fada
"Bai cin abincin yan aiki ai" "aw wani ya ce maki ni yar aiki ce"
"Anty nadia ta ce ke yar aiki ce"
"Kan uban can yar aiki ni""tafada tana nuna kanta
"Toh bari kiji ni matsayina daya da nat nima matar gida ce" ina fadin haka na cigaba da aiki na don sosai abin ya bata min raiIta ma ganin ban kara cewa komai ba sai ta cigaba da aikin nata
Ban dadde ba na gama na juye a kula na jera akan tray na yi sama dashi
A dakinsa na aje sabida ynxu anan muka fi cin abinci ni dashi
Dakina na koma nayi wanka na sauya kaya xuwa lace milk color mai ratsin brown doguwar riga na daura dankwalin na fesa turare
Yau koh hodar da lip gloss din ma ban tsaya sawa ba don jin karar motar daya shigo cikin gidan
Sai dana sa takalmi na kuma dan yi yan gyare gyaren dakin na kimtsa ko ina kan na fice don tarban deen
Dakinsa na leka son yana kusa da nawa bbu kowa alamar ma ba a shiga ba
Banyi wata wata ba na sauka kasa turus nayi don ganin nadia da kawarta xaune suna magana amma suna ganina sukai shuru
Duk dana dan tsargu sai na wayance na shiga kitchen juice na dauka da ruwa sai cups na fito xan haura sama na jiyo hafsa
"Wannan ita ce kishiyar wannan abin" tafada tana nuna ni tana dariya"Wllh wai ita ce kiji fa namiji da niman magana" nadia ta amshe
"Toh ai laifinki ne kema da kk bari har ta sake haka jiba fa har wani shige da ficen ta take hankali kwance"
"Kawata ke dai bari ina nan xanyi maganin munafukar"Har na kai sama sai na juyo jin kalmar munafuka"bani bace munafuka sai dai kece munafukar" na fada ina hararar su
"Ke ni kk fadawa haka" nadia ta mike
"An fada maki koh ce maki nayi tsoron ki nake""In kin isa yar halak sauko kasa dan uban ki" cewar hafsa
"Ba dai ubana ba wllh wawuya kawai " rai na zafin zagin ubana da tayi