Washe gari bayan sun fito daga masallaci ya mikawa salman bundle din kudi "gashi nan kuyi kudin mota in kun kai ka sanar min"
"Toh yaya mungode" ya amsa kudin shi kuma deen ya haura sama
Nadia na ganin sa tace "babe wai meke faruwa ne " "na me fa ?" Ya fada yana zama kan gadon
"Naga fareeda da katon trolly ta kai kasa " "eh kaduna xata" ganin yanayin sa ya sa ta rufe bakinta bata kuma cewa komai ba
Kwanciya yayi ya rufe idanunsa ba don yana jin bacci ba tunanin irin hukuncin da xai wa fareeda yake wanda nan gaba akace tayi masa musu baza tayi gigin aikatawa ba.
Sai da fareeda ta soya masu chips da egg sai tea suka karya sannan kowa yaje dakinsa don shiryawa
Sai 10 suka fito bayan mai gadi ya sama masu taxi da xai kai su motor pack
Deen na kallonsu ta window har suka shiga taxi suka wuce
Kaduna
Sai karfe biyu suka shiga garin kaduna gidan su mami suka sauka daman can sun san da xuwan su don haka an shirya masu komai da komaiSai da suka ci su ka sha sukayi wanka suka huta
Bayan sallar la'asar khady ta raka fareeda gidansu
Tana shiga ta fada kan mama "wayyo mamana I miss you" "ke wllh xan mareki fa baki san kin girma ba koh" mama ta fada tana ture ta
"Oyoyo adda ya makarantar" cewar nanah tana aje masu alalen gwangwanin da suka dafa na rana
"Eyye nanah ke ce haka wllh kin girma sai jami'a" "wata jami'ar ni ai aure xanyi" nanah ta fada tana dariya
Duka fareeda ta kai mata "har ynxu baki canxa ba wllh sai shegen son aure"
"Adda ni ba wannan ba me kk taho min dashi na Abuja "
Jakar ta ta jawo da wata babbar leda ta ce "gashi nan sai ki dauka na mama ma yana ciki godiya nanah tayi ta soma bude ledar
Dogayen riguna ne har kala uku sai kayan kwalama su chocolates,biscuit lollipop, da su taurare da man shafawa
Sai na mama hijabai ne kala biyu sai sabulai da vasline,takalma kala biyu sai atamfa guda biyu
Mama ta sama ta albarka nan suka dan yi hira har ta basu labarin makaranta da cewar ai ynxu shekara 2 kawai ya rage mata
Mama tayi farin ciki sosai ganin yanda fareeda ta canxa tayi kyau kamar ba ita ba,,,,,tunanin rayuwar ta tayi sanda ta nace xata xo kaduna(zaria) karatu mahaifin ta yace ba da yawunsa,
Batai masa BIYAYYA ba ta nace ahaka har ta samu taxo iyayenta ba masu karfi bane kuma gashi bbu wanda ta sani a garin
Koh kudin data eda registration dashi kanwar mamanta ce ta bata su sabida ita mahaifiyarta ta dadde da rasuwa
Bbu wurin kwana bbu kudin kama haya bbu na hostel ahaka tayi ta yawo a makarantar ahmadu bello University
"Aah yar uwa baxaki je gida bane koh hostel" (mama)"Aa ni banda wurin kwana ban san kowa ba anan"
"Ayya hala ke sabuwar daliba ce koh" cewar asiya daga mata kai mama tayi
"Toh in ba damuwa ki xo muje dakin mu sai ki kwana kafin gobe ki san nayi koh" sai da mama ta kallesu da kyau su uku ne basu hijabi
Doguwar riguna ajikinsu ta kanti sai gyalene akafadar su
"Asisi in baxa ta je ki xo mu wuce kar ta bata mana lokaci pls" cewar ummi
"Ke wllh matsalata da ke kenan ummi gajan hakuri ai dole tayi tunani kafin ta bimu koh tunda bata san mu ba"
Tsaki ummi taja ta juya mata baya "xamuje ne koh aa" cewar asiya tana kallon mama