Ana ta shirye shiryen bikin khady wacce suke ta zirga zirga daga gida zuwa gidan gyaran anty asabe yar maiduguri(ina gaida ki kawata)😊
Sosai ake mata gyara koh Ince ake masu don anty amarya tace ita ma fareeda amata
Yau ta kama satin su daya da kwana uku da ake masu gyara kai kana ganin su xaka dauka su biyun ne amaren lol 😆
Gyaran kai da kitso duk aka masu sai kuma yau da xasuje lalle Anty bilkisu ce zata kai su don har ta iso daren jiya kaduna,,,,,,
"Ina kk ku tashi mana ku shirya mu tafi kun dai san gidan lallen nan xamu jima koh" cewar anty bilkisu
Kwance suke da wasu kawayen su akan gado wasu na waya wasu kuma na ayyukan gaban su
"Ai ni anty ina sai dai ku tafi don wllh gaba daya agajiye nake jina" cewar fareeda tana kara gyara zaman pillonta
Harara anty bilkisu ta watsa mata "ai baki isa ba dole dake xa'aje don aban umarni daga sama kema amaki"
Dariya yan dakin sukayi mariya daya daga cikin su tace "miji dadi muma allah ya nuna mana namu" duk suka amsa da ameen
"Kinga ni anty na shirya saura ita"cewar khady ta na daukar jakarta
"Yauwa amarya ke ma tashi kar ki bari na karaso nan" tana gama fadin haka ta fice daga dakin
"Ni na rasa koh kece amaryar fareeda sai yauki kk"cewar ummi
Dariya suka karayi gaba daya har da fareeda "ku wai baku ganewa ne babyn mu ne ahanya" cewar khady tana yi wa fareeda kwallo
Duk suka juyo su kalli fareeda suka kwashe da dariya har ta tafawa
Daure fuska tayi ta kalli khady "ni koh wllh xamu hadu ne xaki fadamin koh ke kk ban ajiyar babyn"
"Ina kk ne wai" suka juyo muryar anty bilkisu daga falo
"Gamu nan"khady ta amsa "kun ga sai mun dawo dan allah kuyi kuje waje sadi ku amso min dinkin nan" ta bude kofa ta fita
Jiki amace fareeda ma ta mike daman da hijabi jikinta jaka kawai ta dauka sai wayar ta da bbu mai kiranta ta bi bayan khady
Sai karfe biyu suka isa garin kaduna direct wajen abokansu suka wuce inda suka duba inda xasuyi event din gobe waton dinner suka tabbatar komai yayi kan suka karasa gida sai daya aje ahmad a gida kan ya wuce nasu gidan
Daman sun san da xuwan sa shiyasa anty amarya ta hada shirya masa abinci kala biyu da kayan snacks
Sai daya ci abinci yayi wanka ya kwanta ya dan yi bacci sai la'asar ya farka yayi alwala ya wuce masallaci koh da ya dawo gun mami yayi ta raba ido koh xai ga fareeda amma shuru
Har ya kare xamansa ya koma gun anty amarya tana xaune da wasu yan mata suna hada soverniers din da xa a raba gun dinner gobe ya shigo gefenta ya xauna bayan ya amsa gaisuwar da sukai masa
"Naji gidan shuru yaran nan fa" tasan wa yake nima amma ta yi kamar bata gane ba "au auta wai wllh yana zaria gun sister binta" yayarta kenan
Daga mata kai kawai yayi can kuma yace "Billy taxo kenan" yana nufin anty bilkisu "eh tun jiya amma ta fita da amaren nan gun gyara"
Bai kuma cewa komai ba nan ya xauna koh xai ga dawowar su amma shuru har magrib ganin ana kiran sallah yasa ya mike alwala yayi anan bangaren anty amarya ya wuce masallaci
Fareeda
Allah masanin juriyan datayi har aka kammala lallen nan amma wllh ta gaji ji tayi kamar xatai amaiSai bayan sallar magrib suka dawo gida suna shiga dakin mami su ka tadda abba ya dawo sannu da xuwa suka masa "eyyye kaga manyan gari har andawo"