Suna kaiwa falon ta janye hannunta taya rike kallonta yayi "ni bacci nakeson yi na gaji" tafada tana kallonshi murmushi ya mata "toh muje ki kwanta tunda kin fasa shan ice cream din" bata ce kala ba ta juya ya bi bayanta koh da suka koma dakin nadia bata ciki
Kan gado ta kwanta shi kuma ya ja mata kofa ya koma dakin sa
Bathroom ya shiga ya sakar ma kansa shower wani irin new feeling yake ji but he can't explain it
Is it shagwaban da fareeda ke masa ne koh kuka her baby doll acting ke sa shi jin haka he jst couldn't say
But to him koma menene he loves it,,,,, ahaka ya karasa wanka ya fito bayan yayi sallah ya kwanta flat akan gado wani sabon nishadi na ziyartar sa
She didn't know why she reacted that way toward deen amma tunda ta ga tayi galaba akan nadia sosai xata gyara plan din ta
It ba wai dole sai deen ya so ta ba koh kuma ya amshe ta amatsayin matar so ba noo she jst wants to b treated fairly
Bbu wukanci bbu cin fuska don taga take taken nadia baiwa take son mai da ta don dole.
Gaba daya kayan dake kan mirror ta watsar dasu na fashewa sun fashe
Xaman tayi akasa gefen gadonta gaba daya ta fita hayyacinta gashin nan ya wargaje kamar mai karamar hauka
Ba karamin mamaki deen ya bata ba yau shi da bai son ganin fushin ta balle kukan ta amma ace yau tana nuna fushinta amma yayi banxa da ita har da mata tsawa
Wayar ta fizgo daga caji ta kira aminiyarta bugu daya ta daga"sai yau kk tuna dani nadia"
"Ke ni ba wannan ba ina cikin damuwa wllh" jin tone din nadia ne yasa hafsat ta ce" lfy kuwa kawata meke faru ne " "hafsa babe ya yi aure " "aure aure fa kk ce nadia toh garin ya,kuma kk zaune" hafsa ta ce cikin tashin hankali kamar ita akayi wa kishiya "wllh hafsa a first I thought ba wani abin damuwa bane tunda ni yakeso kuma xan samu sauki ta wajen abubuwa daya ashe ba haka bane" ta fada tana hawaye
"Lallai kawata ynxu ke namiji xaki xuba wa ido da sunan yana sonki shi ne kk saki jiki tukun na ma wacece matar" sanin me hafsat ke nufi yasa tace"yar fa garinsu ce can kaduna shine mamanshi ta aura masa" "aw kice ba yar kowa bace toh ai duk ba abin tashin hankali bane kawata" "ba fahimce ki ba hafsa kin ko san irin makircin da yarinyar nan ta hada yau kuwa"
Dariya hafsa tayi"makirci ai duk makircin ta baxata iya da kissan mu ba nadia ke dai ki bari na san yanda xamuyi"
"Aa hafsa kin san fa ni all those boka da malamai bason su nake ba dey always back fire back to people" nadia ta fada kai tsaye
"Look at you wake bin old model din nan ynxu ai da kissa masu xafi xa mu horata da kanta xata bar gidan ba sai an koreta ba"
"Dan allah kawata toh ynxu ya xa ayi ne"cewar nadia
"Muna Jos ynxu ne bikin kanwar baban ummi sai next week xamu dawo dana shigo xaki ganni" "toh shikenan kawata sai kun dawo" sallama suka yi sai a sannan nadia ta ji dan sanyi aranta don ta san hafsa kamar yunwar cikinta
Tun suna yan mata suka hadu hafsa ta kasance ya daya tilo gun iyayenta wanda adalilin hakan yasa suka sangarta ta duk abinda takeso ana mata ko min girmansa kuwa
Ahaka suka hadu da nadia abinka da ga kudi kuma ya hadu da kudi nan fa nadia ta kara samun experience akan wasu abubuwa daban daban hafsa ma batason sharing koh kadan
Koh riga idan ya mata kadan Tarawa ake agu daya akona su don wai ita baxata sa ba wani ya saka ba 😅
Ahaka har ta hadu da mijinta sukayi aure nan ma ta hana amata kishiya sabida mjinta mai ra'ayin mata hudu ne sabida dukiyarsa da ya tara haka ma son yara da yake amma hafsa ta ce fir ita ba da ita ba kuma bbu mai shigowa ya haifa
