FIKRA WRITERS ASSOCIATIONRASHIDA ABDULLAHI KARDAM
(Rash Kardam)_Bissmillahi rahmanu rahim_
*_GATARWA_*
*_Dukkan yabo ya tabbata ga Allah. Muna godiya a gare shi, muna neman taimakonsa, muna neman gafaransa. Ya Allah! Ka azurta mana tsoronka wanda zai iya hana saɓa maka. Ka azurta mana ɗa'a a gareka wacce za ta kai mu ga Aljannarka, Ka ba mu yakini wanda zai zai iya saukaka mana masibun duniya, Ka ba mu jin daɗi jinnu da ganinnu, da ƙarfin gaɓabuwanmu har k'arshen rayuwanmu. Ka sa jinmu da ganinmu, da gaɓaɓunmu suza su gaje mu. Ya Allah! Ya Allah ka bamu ikon fansa akan wanda ya zalunce mu. Ka ba mu taimako a kan makiyannu. Ka da kasa duniya ta zama ita ce babban burin mu. Ka da ta zama ita ce matuk'ar iliminmu. Kada kuma Ka sanya mana musibarmu a cikin addininmu, kuma kada Ka sa waɗanda ba za su ji tsoronka ba kuma ba za su ji tausayinmu ba, su zama sune za su saurace mu, ko sushugabance mu. Ya Allah! Ka ƙyautatawa da gaskiya cikin dukkan al'amuranmu, ka kuma tsare mu da wulakancin duniya da azabar lahira. Allahuma amin Ya Allah!._*
_Ya Allah! Ka ba wa raina da zuciyata da tunanina tsorin Allah. Ka tsaftace min raina da zuciyata da tunanina a cikin wannan rubutun littafin da zanyi. Kai ne cancantar wanda zai tsaftace min shi. Kai ne majiɓancin ga raina da zuciyata. Kai ne kuma shugabansa. Ya Allah! Ina ne man tsari da illimin da bai da amfani da tunanin da bai da amfani a yawuwana da kuma cikin wannan rubutu da zanyi. Amin Ya Rabbil Samawati wal Arad._
SHARHI
'''Wannan labarin ƙagagen labarine ban ɗauki labarin wani/wata nayi amfani dashi ba, in kuma yazo dai dai da na wata/wani sai anyi haƙuri da hakan.'''
Page~1
Dukawa tayi kasa tare da zare ƴar sillifas ɗin da ke ƙafarta, ɗan karanin gyalenta da ke ƙuugunta ta kuntoshi tare da zura takalmanta a cikin gyalen ta ɗamare shi a ƙuugunta.
Dan zaninta da ya koɗe ta tattare shi, ta gyara tsayuwarta da kyau ta rike makaɗin tayanta da hannu ɗaya. Daya hannu ta rike tayan.
“Buwun! Buwun!! Buwun!".
Tayi wani irin ruri tamkar karan tashin babur tare da sanya ma tayarta giya tamkar wacce take tuka mota ta lula kan hanyar rairaiyin jar kasar da ke kauyen.
Gudu take tamkar sabuwar Mota da tasha tayu masu ƙarfi da kyau.
Tun daga nesa na hango gungun Yara suna laɓe. Sam Kausar bata lura da su ba don yanda ta kwalo gudu tamkar barewa ke sharara a dokar daji
“Kausar Dambun ƙwarƙwata, Kausar kazama”.
Suuu taja wani wawan burkin wanda yayi sanadun tashin ƴar ƙaramar ƙura a gurin, wani irin gurnani tafara yi tamkar Damisa da ta shekara ba abinci ta gama ɗibo yunwa. Wani irin juyi tayi tamkar walkiya a sararin samaniya, a sukwane ta yi kwana ta nufi inda ta ji muryan Yaran na tashi.
Gungun yaran na ganin haka kowa ya arci na kare, don sanin halin Kausar ko a gaban wayen inta rike yaro sai yaji a jikinsa.
Gaba ɗaya Yaran sun watse duk ta rasa wa za ta bi. Can ta ƙyallo shugaban tawagarsu Ɗahe da gudu ta bisa.
Ba a binda ke tashi a bayan Kausar sai kura tamkar Dokin da ke sharara gudu a Sahara, ko ince tamkar wace ta samu sabuwar kwalta ɗoɗar ba gargada, ganin Ɗahe zai tsere ma ganinta
ta kara kai gami da zama, kafin ta ankaro ya iso ƙofar gidansu ya shiga da gudu.Kausar na isowa bata tsaya wata wata ba tayi cikin gidan, cikin zafin nama irin na matashitya da ke ji da yaranta tayi wuf tashige ɗakin Iya Mai kosai.
“ke! Ke!! Ke!!! Kausar lafiya ki ka biyo Ɗahe?".
Kausar bata saurare ta ba tayi cikin ɗakin kasan gadon Iya tayi ta soma janyo Ɗahe da ya shige kasan gado mai rumfa.
Iya da hanzari ta mike ta soma kiciniyar ɗaura zani tana narka manya manya ashar goron da ya ke cike fam a bakinta shi ya taimaka guri kumfar da ya cika ta ke bakin ya fara rawa kamar mazari an taɓota Iya mai niman ayaraye nanaye bare an taɓota har gida.
“Lalle yau sai kin gane kuren ki, ki zo har gida kuma har cikin ɗaki zaki biyo min Jika, kuma kice zaki dake shi, don tsabar fitsara da rashin kunya yau sai naga mai kwatarki inga Shegen da ya tsaya miki da ƙafafunsa acikin kauyen nan".
Kafin ta isa Ɗahe ya kurma uban kara.
Kausar sai jibgar sata take tamkar ta samu jakinta.
Kafin kace me jini ya ɓalle ta baki ta hanci dai-dai lokacin Iya tashigo, ganin abunda ya faru, ta zare ido ta dunkulo ashar ta narka.
“Jar uban nan lalle yau sai na karairayaki a gidan nan".
Da sauri ta yi gun Kausar ta kai mata wawar damƙa.
“Wayyo Ummana Iya zata kashe ni ki zo ki cecen".
Da sauri ta harɗe ƙafarta a jikin Iya ta yanda ba zata iya dukanta ba. Iya ta sa hannuda niyar janyo Kausar ta jibgeta, ba-zato-ba-tsammani naji timmm! Iya ta zube a ƙasa. Da mugun gudu Kausar ta fita daga gidan bata tsaya ko ina ba sai inda ta bar tayanta. Da sauri ta ɗauka tasa gudu, ta nufi hanyar gida. “Aushh! Washhh!! Ja'ira shegeyar Yarinya ƴar banza ta yar dani zata ci kwal ubanta yau har gun mai gari zan kaik'aran ƴarsa. Ni abun ya isheni haka yarinya kamar Aljana, sai shegen fitana da bala'i yau ta taro ni buhun barko no da na masifa sai naga gatanta yau".
Da kyar ta miƙe ta ta janyo Ɗahe da ke kwance a kasa, ta ɗaga sa zuciyarta cike da ƙunci. Kausar bata ja burki a ko ina sai ƙofar gidansu da ya sha fenti irin na masu halin kauyen. Da gudu tayi cikin gidan ko sallama babu. Ummi da ta fito daga ɗakin Mai gari da kwano a hannunta da alama anci abinci ne a ciki, ta ga Kausar ta shigo kai ta girgiza.
“Allah ya shirya ki Kausar bansan yaushe zaki girma ba? Na sha faɗa miki muhimmacin yin sallama da ladan da ake samu amma sam kin ki kula". Washe hakwaranta tayi da suka rine harsunyi kalan ɗaurawa yalo-yalo dasu tsabar datti.
Kausar sam bata son tsabta ko wanka bata sonyi sai Umma tayi dagaske wani sa'in ma kulle ƙofar gida takeyi ta hanata fita har sai ta dirjeta sosai.
Madafi(kitchen) ta nufa ta ɗauko kwanon abincinta ko hannu bata wanke ba ta fara cin abinci.
Umma da ke kallonta ta ce.
“Kausar na sha gaya miki in zaki ci abinci kina wanke hannu ki sabida dattin da ke hannu ko da wasu cututtuka. In har kin wanke zasu fita,kuma zaki kare kanki da kanuwa da ga wasu kwayan cutta da kananun cututtuka da ido ba zai gani ba".
Kausar sai kai loma take tamkar ba da ita ake yi ba.
Umma ta na kallon yarta a zuciyanta tana mata addu'a Allah ya shiryata.
“Kausar baki fa yi addu'a ba, kin kuma san ba kyau. Don duk wanda ke cin abinci ba bissmilla to yana ci ne tare da Shaiɗan. Shaiɗan kuma in yaga bakayi bissmilla ba, sai yana maka kazanta a cikin abinci misali: kamar yana mayar maka dana baki yana jagwal-gwala abinci. Sannan yin bissmilla kafin cin abinci sunnan Annabin mu ne kuma sunna ne mai ƙarfi dan haka ki dage kinji Kausarata".
Kai Kausar ta gyaɗa mata taci gaba da cin abincinta.
“Banga kin yi bissmillan ba?".
Kausar ta turo ɗan karamin bakinta kamar zatayi kuka don bata son ana yawan mata magana a hankali ta ce.
“Bissmillahi fil auwalihi wa akhirihi".
Murmushi Umma tayi ta miƙe tare da faɗin.
“In kin gama kiyi wanka ki saka kayan Islamiya ki tafi".
Kai Kausar ta girgiza ta ci gaba da cin abinci.
YOU ARE READING
...YA FI DARE DUHU
General FictionLabarin ƙauna gamida cin amana da tausayi ga uwa uba soyayya.