BABI NA UKU

2.9K 150 0
                                    


*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

   RASHIDA ABDULLAHI KARDAM
               (Rash Kardam)

3
Wani lallausar murmushi Kausar ta saki ba abunda ke mata daɗi kamar taji ana mata wannan kirarin jin kanta take ya fasu yayi girma kamar dala-da-gauron dutse. Abunka da yaran kauye sun san kan hausa.

       Abulle ce ta iso da tawagarta su Ladidi ta soma habaice-habaice da bakar magana.

Abulle ƴar Inna Jummai ce kishiyar Umman Kausar. Yar Kausar kenan.

    Kafin Kausar ta bata amsa su Salame da Aishalle sun cafe magar suka fara wurga ma Abulle hausa.

     Tamkar abun zai dawo faɗa don Kausar ba'a mata ta share, Sam bata ɗauko halin Ummarta ba.

     Lamiso ƙwanwar Sallame ce ta yanko a guje tana haki. Ta iso ta taras ana faɗa jan  su Salame gefe tayi da Kausar ta ce.

       “Adda Kausar a hanyata ta zuwa Dan-dali naga Iya mai ƙosai da Ɗahe za su je gidanku sai masifa ta ke yi wai kin daki Ɗahe har bakinsa ya fashe. Sai ashar ta ke ƙundumawa tamkar  Bamaguziya".

Cikin tsoro Kausar ta zaro ido ta ce.

     “Yau na shiga uku in Malam ya rike ni gashi ba'a sani ba na fito yanzu ya zanyi?".

    Sun daɗe suna tunani kafin Kausar ta saki wani murmushi mai ɗauke da mugunta.

     Ku biyo ku ga a bun da zan mata nasan ai bata isa gidan mu ba yanzu haka".

Tana gama faɗan haka suka ruga a guye suka nufi hanyar gidan su Kausar suna isa da sanɗa suka shiga soron gidan anan tasa  su Aishalle su maƙale a ƙarshen kusurwa soron gidan. Kasan cewar gidan ba haske ba zaka iya ganin wanda ke zaure ba.

Da sauri ta shiga da ta ɗauko babbar rigar Malam dake ɗakinsu fara kal! Tare da wani yadi shima fari tana zuwa ta zura babban rigan a jikinta, tare da yin hannu da karan dawa. Aishalle ta ba ma ɗaya kyalle ta rufu dashi kasan cewar ta fisu tsayi. Kausar ta matso kusa da ita ta raɗa mata wani magana a kunne naji sun kyalkyale da dariya.

Daga nesa Kausar ta hango Iya mai ƙosai ta nufo gidan sai masifa ta ke zazzagawa Kausar ta ce.

      “Yauwa ga ta nan zuwa ku yi shiru kar ta gane".

  Dai dai  nan Iya suka iso ƙfar gidan da saurin ta ta shigo soro gidan. Bata yi aune ba ta ga ɗan ƙaramin abu a acikin farin kyalle na yawo kafin ta yi wani yun kuri sai ganin wani tayi yana nufo ta.

Iya mai kosai tana ganin farin abu yana nufota take taji wani miyau ya zo mata wanda ta haɗiye batare da sani ba. Dariya aka soma yi cikin farin kyallen cikin kakkausar murya gashi kumata ya rane mai kama da na manya aka soma ce wa.

"Maraba da zuwanku faɗarmu hahaha! bai mai ficewa daga nan hahaha!".

Take ta soma ja da baya cikin tsananin furgici da razana gamida kiɗimewa, don tunda Iya take a rayuwanta bata taɓa gamo da fatalwa ko Aljanu ba sai yau.

“La ila ha illallahu.... Ɗahe kana ina yau munyi gamo da Aljannu da na sani da ban zo gidan Ja'iran Yarinyan nan ba, hala tambotsan kanta ne soka zo mana...". 

Bata gama rufe baki ba taga fararen abun su iso ta, wani irin juyi tayi tare da sake kara wanda yayi dai dai da saukowan fitsarin da ta ke matsewa ya soma bin ƙafarta. Ihu mai firgitarwa tayi bata san lokacin da tayi  wani tsalle ta haye Ɗahe tafita zaure da gudu har tana gwaruwa da kofar gidan.

Gudu ta ke tana ihu sam bata lura da kwatar da ke gabanta ba sai jin fanjamm!! Karan faɗuwar Iya cikin kwata.

Kausar da suka cire farin kyallen da ringan suka boye suna dariya.

...YA FI DARE DUHUWhere stories live. Discover now