BABI NA ASHIRIN DA HUDU ZUWA ASHIRIN DA BAKWAI

1.4K 73 1
                                    


✏📖
*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

   RASHIDA ABDULLAHI KARDAM
               (Rash Kardam)

Ina gaidaku kyauta Antis ɗina

Anti Asma'u Tahir (Anti Wawu)
Anti Aisha (Colsas english Islamic DP 2012)
Anti Aisha Maman Abdulmajid
Anti mu na Kt Maman biyu
Anti Maijidda Musa
Anti Asma'u Karofin Madaki
Maman Walid
Hadiza Harɗawa
Halima D Umar
Ubaida (Mimi)
Anti Zakiyya Gambo

da sauran wanda bansamu sako kuba amin affuwa

24 to 27
Abdulmajid a hankali ya buɗe idonsa bai sauke sa ko ina ba sai akan Kausar da ta ke dariya kasa kasa, da sauri ya yunƙura zai nufi gunta.

"Washhhh!.

Ya sake faɗa tare da kara dafe gurin don wani irin azaban da ya ke ji kamar ta fi na da. Cikin kiɗima Mamqnsa ta karaso tana kara tambayarsa don duk ta gama ruɗewa. Kasa bata amsa ya yi sabi da azabar zafin da ya addabesa, don bai yi tsammanin akwai abu gurin ba shi yasa ya zauna da karfinsa. Maman Abdulmajid da sauri ta zo ta na duba kujeran can idonta ya sauka akan alluran da ke soke a tsakiyar kujeran. Hannu ta saka ta dauko tana jujjuyawa tasan ba mai wannan mugun aika aikan sai Kausar, da sauri ta kalli gun Kausar cikin sa'a taga tana dariya kasa kasa. Hanzari ta nufeta ba zato Kausar taji an cafko ta wani wawan mari Maman Abdul ta dauke ta da shi, Kausar sai da taga wasu fararaen taurari suna mata shawagi a saman silin ɗin daɗin, DUHU ta gani na ɗan wucin gadin, kafin Anti Safiyya ta tashi ta karbi Kausar Maman Abdulmajid ta rufe ta da duka sosai ta ke dukarta iya karfinta kamar wacce take dambe da sa'arta ko ince tamkar wacce  aka aiko ta. Duk yanda Anti Safiyya ta so karbar Kausar abun ya faskara. Kausar duk ta cika gida da ihu sosai tana niman hanyar guduwa ta rasa ga shi sam bata ga alamar za ta saurara mata, Kausar ta saka kafarta ta tukuikuye Maman Abdul tare da harde kafafunta sai jin timm! Kake  Maman Abdul ta zube a kasa tamkar kayan wanki gashi ta bugi mazaunanta sosai da gudu Kausar ta sauko ta yi hanyar kofar garejinsu zata fita mai gadi ne ya tare ta don kar abu ya bugeta don ya ga aruɗe ta ke. Kama hannunta ya yi ya kaita lambu ya rarrasheta tayi shiru da kyar sannan ya horeta da karta kuskura ta fito yanzu.

Maman Abdul da kyar ta mike sai zazzaga bala'i ta keyi ma Anti Safiyya wai ita ta goyama  Kausar  baya ta ke abun da ta gadama cikin gidan da bana ubanta ba amma ko ita ko Kausar yau a gidan.

Sam Kausar ta ki yarda ta shi go gidan sai da taga Abba ya shigo ta bi bayansa suka shiga yana ganin haka ya gane Aisha ce ta korota ko da suka shiga Maman Abdumajid ta taso za ta bugeta tsawa Abba ya daka mata yasa Safiyya ta shiga da su cikin ɗaki nasiha ya rinka yi Maman Abdul akan

"Ta yi hakuri da hallayar yarinyar ya kamata su mata uzuri sabida a irin gurin da taso."

Ko sauiraronsa ba tayi ba ta tashi ta tafi daki. kai ya girgiza yana mata fatan Allah ya sa ta gane don zuwan Kausar yasa ta canza hallayarta gaba daya...

Tunda wannan rikicin ya faru a tsakaninsu Kausar ko da gigin wasa bata kuma shiga sabgar Abdulmajid ba don ta ji ajikinta Mamansa ta mata duka bana wasa ba.

Abdulmajid kuwa ganin haka yasa ya samu sararin musguna mata a boye duk ta kyale shi bata kula shi.

Abduljalil kuwa bai canza mata daga abunda ke tsakaninsu ba illa wani muguwar shakuwar da su kayi komai tare suke yi wasa tare suke yi ko aiki aka basu amakaranta shi ya ke koya mata sam Mamansu bata son shakuwarsu.

Anti safiya kuma ta shiga N C E tana zuwa don acewarta ya fi mata wannan zaman banzan da take yi, Baban Abdujalal yayi bikon sam taki ta koma ta ce sam bata son ganinsa, yan uwanta sun  tambayeta mai ya hada su sam taki faɗa musu komai ya hadasu.

Abduljalal kam shi baya shigan shirgin Kausar amma wani lokacin in tayi abu tana burgesa har yayi ta dariya shi kadai...

Har yazu su Abdul basu samu gurbin karatu ba a kasashen da suke so hakan ya sa suka bata shekara daya a gida  Abduljalil kuwa ya samu gurbin cigaba da karatu a ATBU har ya fara zuwa. Su Kausar kuma sun kammala makarantar firamari suna jiran sakamakonsu don zuwa makarantar gaba...

Yau  asabar ya yi dai dai da zagayowar ranar haihuwar Abdulmajid, ko ina a gidan yasha ado sabida kwarya kwaryan liyafan da Maman sa ta shirya masa. Gidan cikje ya ke da jama'a ta ko ina.

Anti Safiyya ta shirya Nana Aisha da Kausar cikin koren lase mai mugun kyau yana da adon duwatsu farare ajikinsu ta sanya sumus farin takalmi da farin gwgwaro abunka da kausar farar mace ta ke ta fito fess acikin kayan kamar ba Kausar din kauyen Buzaye ba, tamkar ba Kausar dambun kwarkwata ba, ta ɓace daga Kausar kazama ta dawo Kausar yar birni mai kyau.

Duk in da ta gifta sai ance MASHAA ALLAHU BARAKALLAHU AHASANUL KALIKIN sabida kyau da kwarjinin ta take dashi. Maman Abdulmajid duk sai taji ta kara tsanar Kausar sabida yanda ake ta yaba kyanta ba ayaba na yayanta sosai sai dai abu ɗaya ta sani ko kadan baza tafi Abdulmajid da kyau sai dai su kara hakan yasa ta ke danji dama dama azuciyarta.

Kasancewar a cika acikin harabar gidan kowa ya sauka suna zazxaune a fararen kujerun da suke cikin rumfa a gidan uban gayya ake jira ya fito a fara gudanar da abunda ya yarasu. Saman ya zama shiru Kausar harta sauka sai ta ga Anti Safiyya ta haura cikin gidan da wasu kawayenta na makarantarsu suma ta gayyatosu sun zo, Kausar duk iskancinta ba ta yarda tayi ma Anti Safiya sabida irin rikon da tamata duk wanda ta gani da ga gunta yake tana girmama shi haka ita ma Anti Safiyya duk kawayenta sun san da labarin Kausar. Sai da su Anti Safiyya suka kai kusa da hawa matakalar ta yafito Kausar da hannu alamar ta zo, itama Kausar din daman tana shirin zuwa ta gaishe su kenan ta kirata.

Sai da suka isa Kausar ta iso cikin ladabi ta russunba ta gaidasu cike da ladabi kowa sai yaba kyanta ya ke. Anti Siyama ne ta kalli Anti safiyya ta ce,

Yar uwa na san ba a rasa ki da tuwo filis in akwai ni shi kadai nake ji kwadayin ci anan."

Dariya suka saka mata suna zolayarta kasancewar tana da sabon ciki Anti Safiyya ta ce,

"Kausar je ki kawo mata sauran dumammenan ɗazu."

Cikin ladabi ta amsa mata ta mike ta je kicin ta dumamashi gashi ko ta yi sa'ar miyan yauki ne ga yawa Kausar duka miyar  ta juye a cikin wani dan farantin cin abinci, ta soma fitowa ta ji ansake kida take taji sautin yana ratsa ko ina ai da sauri ta zura aguje don takai a fara shagali da ita.

Abdulmajid ne ya fito cikin shigan fararen kaya gauraye baki riga mai falmara yasa fara tass! sai bakin makilin wuya haka shi kuma baki takalmin kafarsa fara sol kallo ɗaya za ka masa ka ga irin madaran farincikin da ya ke ciki wanda ya kara fitar da kyawunsa Abdulmajid kenan dan kwalisa matashi mai ji da kansa mai cike da aji da ilimi ga gayu ga tsabta abun fa sai wacce ta gani, don a yanzu haka yan matan da suka gama makaranta da su da yawa suna kwo masa hari amma ba kowa ya ke kulawa su gaisa ba sai ya lura kina da aji sosai.

Cikin isa da takama ya ke takawa in har ka gansa sai ka rantse da Allah dan wani hamshakin mai naira ne sabida kom,ai nasa na masu shine sosai baya so har kan kari.

Kausar gudu take yi ta kai aikan sam bata lura ba sai taji tayi karo da mutum robar towon da miyar gaba daya ya juye ajikin wanda zukayi karo cikin razana ta dago,

"Inna lilahi wa inna ilaihi raji'un."

Ta furta cike da tsoro ta zaro manyan idon ta cike da dana tsani da nadama sam bata yi tsammanin haka amma abun da ta gani a idonsa irin kallon tsanar da ya ke mata yasa ta murguda baki ta juya zata bi gefe ta wuce cikin karaji yasa hannu ya damko ta ganin haka ta karasa juye masa sauran miyar afuskasa da roban a hannunta ta soma niman hanyar gudu sauran miyar na zuba amatakalar Abdulmajid shima da gudu ya bi bayanta.

...YA FI DARE DUHUWhere stories live. Discover now