BABI NA TAKWAS

1.9K 107 1
                                    


*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

   RASHIDA ABDULLAHI KARDAM
               (Rash Kardam)

8
*******
Mummyn su Abdul tana fita gun aiki ta nufa cikin L E A(Local Government Education Authority). Da ke cikin garin bauchi RANK Road. Sauri sauri take tafiya na funi cikin ofishinta dake Account section (Bangaren Kudade). Tun da ga hanya kowa sai isar da mata gaisuwa yake suna mata sannu da zuwa Aunty Aisha, kasancewarta mace mai sakin fuska ga barkwamci. Don duk kusan ma'akatar suna girmamata hatta manyan da ke sama da ita suma tana girmamasu, shiyasa suma suke ganin kimarta a wurin. Dadin karawa mace ce mai son addini abun da ke karamata kima da kwarjini. Tana zuwa kofar ofishinta masinja ya mata sannu da zuwa ta amsa cikin girmamawa, nan yaso ma tsokanar Umaira.

“Ah! Lalle yau da Hajiya karama a kazo ne?". Ta ke Umaira ta washe baki sabida duk randa aka zo da ita yana sayar mata alawa, yana dan tsokanarta kuma yana kyautata mata sabida sunan Mamanta ne akanta Aisha. Kuma Anti Aisha tana ganin kimarsa shima. Bayan tashiga ofishinta ta same shi tsaf ko ina a gyare sai kamshi da ke tashi ga sanyin A.C(Air Condition) da ke ratsa ko ina na ofishin. Tatardu ta jawo ta fara duk wasu ayyukan da ya dace. Bata leko waje ba sai da lokacin sallar Azahar yayi tayi sallah tawo da huta sabida ta karasa duk wani aikin da ya da ce tayi duk ta kammala, hakan yasa ta zauna a doguwar kujeran da ke ofishin Umaira na gefe tana ta zuba mata surutu. Karfe Hudu dai dai ta bar gun aiki sauri sauri ta dawo gida don shirya ma Alhajinta girkin tarba da yaranta. Tana isowa agurguje ta shiga kitchen(madafi). Ta soma tsara duk wata girkin da tasan Alhaji zai yaba da shi. Sai karfe shida saura minti ashirin da biyu ta kammala komai. Sauri sauri ta shiga wanka sai da tabbatar da ta wanku tana fitowa ta daura alwala tasanya hijab kasancewar an soma kiran sallah.
              ****
Tafiya suke fuskan kowanne su dauke da fara'a sabanin gogan namu wato Abdulmajid da hakan ya zame masa tamkar a jinin jikinsa yake. Abduljalil kam ji yake kamar su koma a barsa a can, yana son gari irin haka baran in da irin su Kausar me zai dame sa. Abduljalil ya kalli Abdul ya ce.

“Ya Abdulmajid nikam ban so mu dawo ba kamar mu koma a barni a can."

“Mtsww! miye abun so a kauye? Ai yanzu ma ba ka makara ba, ga tagar mota za ka iya fita tanan ka koma."

Abdul ya mayar ma Abdulajil da amsa.

Murmushi Abduljalil yayi don ya harbo jirginsa, har yanzu da takaicin Kausar gami da tsanarta a zuciyar Abdulmajid. Shiru yayi bai kara tanka masa ha har suka soma shigowa cikin garin Miri. Nan suka shiga cikin garin zuka sada zumunci da gaida yan uwa da abokan arziki.

Abduljalil tunda ya haɗu da Abduljalal nan suka shiga hirar yau she gamo.

Abduljalal ɗan Anti safiya ne ya zo shi hutu Miri ne gun Kakarsu. Shima duk a gidansu Abdulmajid ya ke. Abduljalal shima miskili ne na ƙarshe kusan halayyarsu ɗaya da Abɗulmajid, mai ɗan saukin cikinsu kenan Abduljalil sam shi ba ruwarsa bai ɗau girmar kai da jiji da kai irin nasu na masu sarauta ba. Dalilin shakuwarsu kuwa shi Abduljalil ya iya Mathematic (lissafi) sosai shi yas a Abduljalal ya liƙe masa ya na koya masa, don in yace zai liƙe ma Abdulmajid ne sam bai cika son hayaniya ba sai ya ga dama ma ya masa don halinsu ƙusan ɗaya ne shiyasa kowa ke ji da kansa baran Abduljalal da ya ke ɗan masu kuɗi ga kuma mulki shiyasa shima ya na jin shi wani ne.

Basu bar garin ba sai daf magriba sanan suka dau hanyar cikin gari. Abduljalal ya so ya bi (Mamansa Anti Safiya) su koma Bauchi don yayi kewarta sosai ga Abbansa ma ya matsa sai ya je masa hutu ya ki kuma hutunsu ya ƙare saura sati ɗaya su koma makaranta.

Sun danyi tafiya mai nisa kaɗan kafin suka shigo cikin gari lokacin an fara kiraye kirayen Sallah magriba. Han yar unguwansu da ke Ibo Quarters suka nufa sai da suka dan shiga cikin unguwar dai dai wani kofar katafare gidan sama mai kyau da dauke ido, yana da fenti kalar kore da fari. A saman gidan rubuta GIDAN SARKIN FADAN MIRI) da manyan harufa.

Gida ne na karamin mai kudi wanda ke da rufin a siri Ubangiji. Gidan kusan a layi ita ce mai kyau, sai wata gidan sama da ke gefenta ta dama itama ba laifi tana da dan kyau amma bata kai na su Abdul ba. Sai ɗaya gefen hannun hagu kuma asibitin AL-MANZIR ne a gun.

Katon gate(garejin mota) suka ƙusa hancin motarsu zuwa cikin gidan gun ajiye suka nufa suka faka kowa ya fito.

Suna isa kofar shiga cikin gidan Abdulmajid ya sauke ajiyar zuciya a hankali ya furta.

“Duk wanda ya bar gida gida ta barshi gaskiya ne yau ɗaya na yi kewar gida."

Da ɗan gudun sa ya nufi cikin gida yana kiran “Mummy! Mummy!!! Mummy!!! Ga mu mun dawo".

Yana shigowa falon ƙasa ba ta nan da han zari ya soma hawa matakalar har ya isa tsakiyar falon sama.

Mummyn su Abdulmajid tana shirin shiga daki don gabatar da sallah magriba ta ji muryan Son(Danta) dinta ya shigo falo ya na kiran ta. Da sauri ta fito kicibus suka yi a falo da sauri ya yi gunta ya rumgumeta yana fadin.

“Mummy nayi missing dinki".

Cikin jin dadi da fara'a ta dago.

“My Son(Yarona) kun dawo? Ya hanya ina Daddyn ku?".

Kafin ya bata amsa su Khadija suka shigo tare da Anti Safiya da Abduljalil, sai Daddy da ke bayansu. Sannu da zuwa ta musu ya amsa a cikin sakin fuska. Juyowa yayi kalli Abdulmajid da Abduljalil yace.

“Ku hanzarta yin alwala mu tafi masallaci kar murasa sallah magriba".

Ya na gama fadin haka ya nufi dakinsa don dauro alwala. Bai dade sosai ba yana fitowa su Abdulmajid suka fito nan suka sauka zuwa Masallaci. Su Nana Khadija da Umaira da Anti Safiya kowacce itama ta je yin alwala don gabatar da sallah.

Bayan sunyi Sallah su Anti Safiyya suka fito falo. Suna zaune har aka kira a isha'i kafin suka koma daki kowa ta sallah isha'i.

Su Daddy ba su dawo ba sai da suka tsaya a masallaci aka gabatar da nasiho sannan sukayi sallah isha'i kafin ya taso keyar yaransa zuwa gida.

“Assalamu'alaikum". Suka shigo dukansu da sallama a tare Daddy na bayansu.

Anti Safiya , Umaira Nana Khadija da Mummynsu da tafi to daga daki duka suka hada baki gurin amsa musu Sallamansu da.

“Amin Wa'alaikumusalamu wa rahmatullah".

Tukun suka shigo cikin Falon Daddy kuma ya nufi dakinsa don rage kaya. Mummynsu ma ta bi bayansa da sallama ta shiga sai da ta masa sannu da hanya da tambayar mai jiki kafin ta taimaka masa ya cire kaya. Ta hada masa ruwan wanka ya watsa don yaji dadin jikinsa kafin suka fito falo don cin abincin dare.

Sai da kowa ya zauna Mummy ta saka wa Daddy abinci a plate take kamshi ya fara buga hancinsa. Ido ya lumshe yana matukar son girkin Aisha duk inda yaje ya saba da girkinta shi yasa yake matukar sonta da ji da ita. Ta dawo masa tamkar tsoka daya acikin miya. Tamkar kifi daya acikin rafi, sam ba zai iya nisa da Aishansa ba mace ce wacce ta can canci  yabo da so ta musamman. Ɗon wani lokacin in ya so zolayarta ya kance da a yanzu ne na ke niman aurenki da na nininka sadakinki sabida tsadarki. Ko kuma randa ta masa abunda ya matuƙar sa shi farinciki ya kan ɗauki kuɗi masu ya wa ya bata ya ce wannan sadakinki ne na ƙara miki.  A hankali ya sauke wata sassayar ajiyar zuciya ya gyara zama tare da yin bismilla ya fara kwasan girki Aisharsa abar sonsa.

Sai da ta saka ma kowa tukun ta zauna tafara cin nata, tana aika ma Daddy da dan kalonsu na soyayya cikin dabara ba tare da ta bari yara sun fahimci hakan ba.

*Ƴan uwa kuyi haƙuri da wannan naso turo muku feji biyu banda caji ɗakyar nayi editing wannan ma wayar yana ta min warning ba caji. Amma gobe in yau Allah ya kaimu inhar na samu caji zan yi da yawa in Allah yarda amin.*

*FWA*

...YA FI DARE DUHUDove le storie prendono vita. Scoprilo ora