BA BI NA AMSIN DAI-DAI ZUWA HAMSIN DA DAYA

1.4K 67 0
                                    

✏📖
*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

   RASHIDA ABDULLAHI KARDAM
               (Rash Kardam)

*Wannan shafi naki ne Jamila Muhammad Sabo (Anti Jamy) da ke baby Allah ya barmin ku😍😍*

50-51
A daren ya kira aka shirya musu visa ita da shi don tare zasu bar ƙasan, ɗaure ya barta ta kwana. Wa shegari da safe ya fita motsa jiki kamar yanda ya saba, bayan ya gama ya dawo zuciyar sa cike da son sake ganin Suhana da yarinyar da ya ga bayanta bai ga fuskarta ba idanunsa na cike da kewan sake ganinta. Bayan ya dawo waya ya yi aka kawo masa abun karyawa shi da ita sun karya  ya haɗa mata ruwan wanka ya bata kaya ta canza kafin ya sake ɗaureta don ranar litinin ya ke son barin gari zuwa Dubai. A haka ya ci gaba da kulawa da ita har zuwa ranar litinin suka samu komai zuwa yamma jirginsu ya ɗaga zuwa Dubai... Ko da suka isa nan ya wuce da ita wani arnen gida wanda ya ke c
da ɗakunan sirri na karkashin ƙasa anan suka ɓoyeta don baza su sake ta ba har sai cimma burinsu...
                           ****
Kausar da Suhana cikin farin ciki suka isa Mumbai nan Kausar taga tarba ta karamci da so nan ta ƙara razana da irin tarin dukiyar da Baban Suhana ya ke da shi yaransa su uku ne Adeel Sa'ad Khan sine babba sai Samir Sa'ad Khan shi ya ke bin Adeel sai Suhana Sa'ad Khan ita ce autarsu. Gaba ɗaya burin kowa a gidan ya faranta ma Suhana rai don ita ce mace ɗaya kuma autarsu suna mugun ji da ita. Kowa a gidan ya san Kausar Samir kam sun sha haɗuwa da ita in ya je duba Suhana a New Delhi hakan yasa suka saba Adeel ne kawai bai santa ba a fuska sai a waya wani lokacin suna gaisawa.

Zaune suke a falo suna hira suna dariya Daddyn Suhana ya juya ya kalleta  ya ce,

"Suhana ina Kausar ta ke kin barta ita kaɗai ke kina nan kina dariya ai zata ji ba daɗi."

Da murmushi a fuskanta ta juyo ta kalli Daddy ta ce,

"Dad ta shiga wanka ne fa shiyasa na fit..."

Bata samu daman karawa ba gani Adeel ta shigo da ƴar jakarsa a rataye a kafaɗarsa da alama daga tafiya ya dawo.

Da ihun murna Suhana ta miƙe ta je ta rungumesa kowa murna ya ke yi Adeel ya dawo.

Cikin falon suka shiga ya ajiye jakar sannan ya gaida Mummynsu da Daddynsu ya dawo cikin ƴan uwansa ya zauna. Sai murmushi suke suna gaisawa don ya kwana biyu baya gari yau ya dawo daga Kashmir...

Kausar da ke gaban madubi datana can-cara kwalliya ta ji hayaniya da ihu kamar za ta fito sai ta ji ana fadin Adeel Adeel ko shakka babu Adeel Bhai ne ya dawo, rass! Gabanta ya faɗi da ta tuna da irin zafinsa da rashin sakewa wa mutane yanda Suhana ta ke bata labari.

Cikin shigarta ta hausawa ta fito rass! Da ita ta yi masifar kyau bare yanzu da ta ƙara murjewa da farin fata. A tamfa ce a jikinta kore sharr! Da baƙi sai ratsin ruwan madara a jiki, takalminta ta ciro sabuwa maras tudu wanda Abduljalal ya kawo musu iri ɗaya ita da Suhana, sai gyale kore da kalan madara da ke jikin atamfar atamfar sai bakin sarka da ɗan kunne bakinta ya sha jan janbaki. Kausar mace mai kyau wanda ko ke ɗiya mace in kin ganta za ki so ki ƙara ganinta gashi Allah ya mata zubin kirar halitta. A hankali ta ke takawa ta nufo cikin falo gabanta na wani irin ƙoɗawa kanta a ƙasa fuskanta cike da kunyar da baya ɓuya kunya irin na fulanin asali...

Tun kafin ta shigo cikin falon ƙamshinta ya rigata isowa Suhana murmushi ta yi a zuciyarta cike da ƙaunar Kausar sabida tsabtarta ga kuma hankali.

Dukka hankali su na ga ƙofar shigowa falon sabida ɗan ƙarar takalmi alamar tafiya da ke ta shi ɗaya-bayan-ɗaya.

A hankali ta shigo fuskanta ɗauke da murmushi kanta a ƙasa, Adeel ne ya fara tozali da ita ta ke ya ji zuciyarsa ta wani irin ƙoɗawa bugun zuciyarsa ya ƙaru da sauri-da-sauri. Kasa haƙuri ya yi ya miƙe idanunsa a hanka ba abunda ya ke yi illa tasbihi ga Allah da ya ƙagi wannan surar tabbas yana ganin farare hausawa da su amma wannan farinta dabanne kyanta dabanne daga Allah ne don ya sanya mata wani sihirtaccen kyau na musamman. Mummy ma ta yaba da kyanta kowa da ke falon sunyi matuƙar mamaki da ganin irin kallon da Adeel ya ke mata, don shi mutum ne wanda baya shiga sabgar kowa bare mata harƙan gabansa kawai ya ke yi. Adeel sam bai iya ɓoye abun da ya ke so ba, hakan yasa kowa da ke falon ya karanto tsananin son Kausar a cikin kwayan idonsa.

...YA FI DARE DUHUWhere stories live. Discover now