BABI NA GOMA SHA TARA ZUWA ISHIRIN DA DAYA

1.5K 80 1
                                    

✏📖
*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

   RASHIDA ABDULLAHI KARDAM
               (Rash Kardam)

19
Abba zai
sauke su Kausar da Nana Khadija  a Prince and princes primary school. Kausar dakin Anti Safiya ta je ta ɗauko gilashin da taga Abduljalal ya saka a gefe taga abun makalawar muya na kwala riga shima ta ɗauka tare da kambas ɗin shi ta sa a jakarta ta ɓoye sai sun fita za ta saka sabida itama yau tana son ta dawo yar gaye ta na burge mutane. Nana Khadija ne ta zo ta rike mata hannu suka fita harabar gidan suka shiga motar Abba ya nufi makarantarsu.

   *KAUSAR A MAKARANTA*

Ko da su ka iso makaranta a bakin Makarantar Abba ya sauke su kasancewar ya gama Kausar komai aji kawai za su shiga. Assembly su ka wuce bayan anyi ta ken kasarmu sannan aka gabatar da addu'o'i shugaban makaranta ya gabatar da jawabi tare da sabbin malaman da aka sam karinsu da ga nan aka gama a cikin layi dalubai su ka nufi aji suna waka. Kowanne dalubi ka gani cike da farin ciki yake sabida ranar aka dawo makaranta daga dogon hutun da su ka tafi. Kausar da Khadija sune a karshen layin ko da suka zo shiga aji Kausar ta ce ita ba yanzu za ta shiga ba sai ta gama kallon yan makaranta. Khadija ta shiga ta zauna suna jiran zuwan Malamin turanci don shi zai fara musu darasi yau.

Kausar takalmin kafarta ta cire tasa na Abduljalal  ta saka ta kawo makalin kwalan riga ta sanya. Tana cikin haka taga wani dogon malami ya shiga ajin yana shiga taji ajin yayi shiru dan haka ta makala gilashinta ta mike ta nufi ajin tana zuwa ta taras sun gama gaida shi kowa ya zauna kasancewar malamin ya bata baya bai ga shigowarta ba sai jin dariyan yan aji da sowa yasa shi jiyowa dariya ne ta so kubuce masa amma sai ya da ke cikin tsawa da harcen turanci ya ce,

"Ke miye haka wani irin shiga ne haka? Da ga ina ma kike?.

Sam bata gane mai ya ke nufi ba sai da ya mata da hausa ganin sabuwar ɗaluba ce.

Kausar ganin ana mata dariya ta dauka ta gama burgesu ne sai ta gyara tsayuwanta tana kallon wannan Malamin da kyau ta ce,

"Da ga kauyen Buzaye na ke can waje Rijiyar Malam kafin ka isa Nabardo."

Ƴan ajine suka sake sowa suna mata dariya. Malam Sani ne ya juya ya daka musu tsawa ta ke kowa ya shiga hankalinsa. Kallo ya kare mata ya tuna da yarinyar da aka bashi bayanne akanta sabuwar daluba kuma daga kauye ta ke, don haka sai ya sata ta zauna a bencin gaba yasa ta cire gilashin daga nan ya fara musu darasi.

Ko da aka tashi tara duk wan da ya ga Kaudar da shigar da ta yi sai ya yi dariya sosai nan ta dawo abun nunawa ita kuma a tunaninta ta burgesu ne.

Ba yanda Nana Khadija bata yi da ita akan ta cire takalmi da gilashin ta ki da haka har suka koma aji aka ci gaba da karatu.

karfe sha biyu aka tashe su a makaranta Isiya direba ne ya zo daukansu sai hararan Kausar ya ke yi ita kuma ta  ganin haka ta ringa mur guɗa masa baki.

Yau sati Kausar uku a gidan kwarkwata sun dameta hakan yasa Anti Safiya ta aske mata kai da reza ta mata malu tandal su Abduljalal da su Umaira  dariya su ke mata tun tana dariya har ta fara jin haushi.

a ban garen makaranta kuwa tana zuwa ana mata darasi na musamman a gida. Tsakaninta da su Abdulmajid da Abduljalal kuwa ba shiri gwamma Abduljalal Anti safiya tana tsayar  ma sa, Abduljalil ne kawai suke shiri yana biye ma shirmenta.  Mamin su Abdulmajid ma ba wani canji duk ta tsani Ksausar sam bata kaunan ta bude ido ta ga Kausar a gidan.

Zaune suke a Falon gidan Kausar sun da wo daga islamiya da  suna shigowa suka gaida mutanen falon ta zo zata wuce ta gefen Abdulmajid don mugunta da gan gan yasa mata kafa ta faɗi ta ke bakinta da goshinta ya bugu ya kumbura sundum. Sannun karya ya fara mata suna hada ido ya harare ta ya mata gwalo. Takaici ya kamata  Anti Safiya ne ta wanke gurin ta sa mata magani sannan ta shafa mata man zafi a inda ya kumbura.

...YA FI DARE DUHUWhere stories live. Discover now