BABI NA ARBA'IN DA DAYA ZUWA ARBA'IN DA BIYU

1.3K 70 0
                                    

✏📖
*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

   RASHIDA ABDULLAHI KARDAM
               (Rash Kardam)

41-42
Kausar ta gama sadaukarwa tana jiran ta ji ƙofa ya bugeta sai taji shiru hakan ya sa ta buɗe idonta a hankali sai ta ga ya koma yana shirin dawowa da sauri ta faɗa cikin gurin Aisha sai murmushi ta ke yi. Hannunta ta kama suka bi bayan Haidar kasancewar ta san gun sosai duk randa suka shigo kasar Dubai basu da gun cin abinci da ya wuce DIAMOND RESTAURANT gurin cin abincinne na manya kuma duk abinci kasahe da dama za ka samu a girin suna yi. Ko da suka je Kausar kaiyanci ta yi ba kaɗan ba ta re da santi don ba karya sun iya girki. Nama da wani madara mai lafiya  da sauran kayan ciye ciye Haidar ya sa aka kawo musu. Sai da suƙa ci suƙa koshi sannan suka fito Tazi Haidar ya tsara suka shiga dukansu Masallaci suka je sai da suka gabatar da Sallah  sanann suka sake fitowa filin saukan jirage suka sake mayar da Kausar nan suka yi sallama tare da  canje namba da Aisha ta musu godiya ta je suka tafi ba su jima kuwa aka sanar da jirgin da za taje Indiya nan da minti goma zai tashi.

Suna zaune har lokacin ya cika na aka kirasu suka shiga jirgi bayan sun kammala komai jirginsu ya tashi zuwa India.

Karfe sha biyu da minti goma jirginsu Kausar ya sauƙa a New Delhi.  Sannu a hankali fasinjoji suke sauƙowa, Kausar na ɗaya daga cikinsu cikin nutsuwa da hankali ta ke tafiya ga gajiya a tattare da ita sai tafiyarta ta ƙara canzawa tamkar Hawainiya.

Cikin nutsuwa ta ke tafiya har ta iso inda muta ne ke tarar yan uwansu kamar daga sama ta ji muryan wani cikin harshen tura ci ya ce,

Barka da zuwa Kasar Idiya Fatima Hassan Muhammad."

Da sauri ta jiyo ta kallesa murmushi ya mata.

Cikin ladabi Kausar ta amsa masa katin shaidarsa ya nuna mata, yana ɗaya da ga cikin wakilan da Gwamnatin Najeriya karkashin jagoranci Gwamnatin Jihar Bauchi ta wakilta. Sai da suka gaisa nan ya ɗauke ta a mota suka tafi. Gurin Saukan baki na MAHATMA GHANDI HOTEL ya kaita nan ya kama mata ɗaki ya mata bayanin zata zauna nan da zuwa kwana biyu zuwa uku kafin a gama komai sai ya kaita gidan da za'a kamata haya ta zauna. Godiya ta masa sosai sannan ya bata nambar wayar shi  ya kuma karɓi nata.

Kausar kayanta ta cire ta shiga bayi baki ta hangame cike da kauyanci don bayin ya haɗu ba na wasa ba. Sai da ta ɗauki kusan minti goma tana kalle kalle kafin ta kunna ruwa ta watsa ta ɗaura alwala bayan ta fito ta shafa mai ta ɗan murza foda. Ɗakin taji ana kwankwasawa  cikin tsoro ta mike taje bakin kofar ta ɗan jima kafin ta sa hannu cike da tsoro ta buɗe ƙofar. Wani ta gani sanye da kayan ma'aikatar otal ɗin, gaban rigansa an rubuta DANIEL KHAN da manyan harafi. Hannunsa ɗauke da faranti da kwanukan abinci akai, cikin harshen turanci ya gaisheta ya faɗa mata abinci ya kawo mata hanya ta bashi ya shiga  ya ajiye godiya ta masa ya fita.

Tana komawa cikin ɗakin ta ɗauko doguwar riga maras nauyi ta sanya sai man baki ta ɗan shafa,  nama ne da  wani irin abinci suka kawo mata,  abincin ya gagareta ci naman kaɗai ta iya ci shi ya kosar da ita. Hamdala tayi kafin ta mike ta buɗe jakarta wayarta ta ciro ta kunna nan taga sakwanin sun shigo ta buɗe ɗaya daga Abduljalal ne ya turo mata kalamai masu sanyi daɗi tare da mata ban gajiya da hanya. Ɗayan kuma Anti Safiyyane da Nana sai na karshsn daga Abduljalil shima barka da hanya ya ke mata.

Da haka har ɗare ya yi wanka ta kuma ta kwanta bacci, washe gari bayan tayi sallah ta karya tayi wanka cikin shigar riga da skirt na atamfa ja da ratsin baki da ruwan ɗaurawa bakaramin kyau ta yiba. Kofar ɗakin taji an kwankwasawa ko da ta buɗe Mutumin jiya ta gani hanya ta bashi ya shigo ya zauna cike da tsoro zuciyarta na ɗarr ta zauna a kasa ta gaisheshi ya amsa da fara'arsa. Bayan sun gama gaisawa ya ce ta ɗauko mayafinta da fasfo ɗinta sai takardunta da kwafinsu mikewa ta yi ta tattari komai a bakin jakarta sannan ta saka takalminta maras tudu shima baki ta yafa gyale ja bakaramin kyau tayi ba sosai shima kansa ya yaba da kyanta ba laifi. Ɗakin ta kulle suka sauka motarshi suka shiga nan suka nufi NIMS UNIVERSITY da ke cikin NEW DELHI. Ko da suka iso Jaipur Rajasthan unguwara da makarantar ta ke, Kausar tana zaune a mota sai kale kale take da yanayi mutanen garin zuciyarta ce cike da farin ciki wai yau ita ce a kasar su Amirkhan da Sharokhan da Salman Khan. Kuma ga Indiyawa nan wasu da shigar kanan kaya wasu kuma shigar su ta Indiyawanne abun gwanin burgewa.

Gine gine suka wuce na burhewa wani Katafaren guri a kofarsa a rubuta *WELCOME TO NATIONAL INSTITUTE OF MEDICAL SCIENCES (NIMS UNIVERSITY INDIA)* wani sassayar ajiyar zuciya ta sauke sannu a hankali motarsu ya kutsa cikin makarantar gurin da aka tana da don ajiye motoci nan suka ajiye tasu suka fito, ban garen karɓan ɗalubai suka nufa.

Tsari da zubin makarantar makarantan abun burgewa ne ɗalubaine daga kasashe daban daban na duniya makaranta ne da ake karantar da abubuwa da dama. Suna zuwa kofar office ɗin ya nuna ma Kausar wasu kujeru da ke gefe ta zauna mutum ɗaya suka samu suna gana wa da mai ofishin. Bai su jima ba ya fito hakan ya basu daman shiga bayan sun shiga cikin harshen turanshi Mr  Mahamud Adam suka gaisa da wani Ba indiyen da ke ofishin mai suna Balvir S  Tumar. Kausar itama ta gaidashi ya amsa kujera ya nuna musu suka zauna nan Mr Muhamud Adam ya gabatar da Kausar ba tare da ɓata lokaci ba ya ɗauko wani farar takarda ya yi yan rubuce rubuce ajiki sannan ya manna shaidar tambarin makarantar ya basu tare da nuna musu wani ofishi inda za'a mata wasu yan tambayoyi. Godiya suka masa suka nufa koda suka je Kausar bakinta cike suke da ambaton Allah har ta shiga inda zata amsa tambayoyin. Cikin ikon Allah bata daɗe ba kuma komai ya zo mata da sauki ta masa nan aka bata takarda shaidar ɗaukanta da na shaidar ita ɗalubansu ce a makarantar da sauran abubuwa. Kofa suka fito tana kara gode ma Mr Mahamud Adam, murmushi ya yi sannan ya ɗan roki alfarman ta jirashi bari ya zo. A gefe Kausar ta ke zaune tana kallon yanda ɗalubai suke shiga da fita, kaman daga sama taji karar jiniyar motoci wanda suka taho a jere reras farare tass! Gwanin burgewa duk wanda suke gurin da masu wuce wa sun zuba ido suga mai fitowa daga motar. Wasu mutanenen suka fito tare da zagaye motar alamar akwai shugabansu aciki dukkansu sanye suke da fafaren kaya. Sun ɗan jima da tsayuwa kafi babban motar da ta kasance ta tsakiyarsu aka buɗe murfin, sai da ya kai kusan minti biyar da buɗewa kafin aka soma zuraro kafa. Kausar da ke gefe duk ta gama kaguwa da taga waye zai fito daga motar nan haka lalle tabbabs babbane kuma masu ji da naira gami da mulki. Da sauri ta sauke idanunta kan takalmin da ya haɗu ga ɗaukan a hankali ta kalƙi kafafun take bi da kallo cikin zakuwa da zakwani da soma bin kafar daki daki wani irin lumshe ido tayi ta buɗe tare da furta,

"Tsarki ya tabbata ga Ubangijin da ya ke hallitar fatan ɗan Adam lalle mamallakin wannan kafar abun..."

*FWA*

...YA FI DARE DUHUحيث تعيش القصص. اكتشف الآن