✏📖
*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*RASHIDA ABDULLAHI KARDAM
(Rash Kardam)Wannan shafin naku ne.
Khadija Gombe
Meenal nijar
Hauwa
Mrs Al'amin
Husna Idris
Sugura Abdullahi
Hajara Salisu
Nafisat Al-hassan36-40
Tafiyar da bai fi minti goma sha biyar ba suka iso kofar gidan. Take jikinta ya ɗanyi sanyi tunawa da tayi da halin Maman Abdul yanda ta tsaneta. Suna sauka shi ya fito ya buɗe bayan mota ya ciro akwatin kayanta. Ta tattara sauran kyaututukanta suka shiga gida Nana da gudu ta zo ta rungumeta sai da suka gama ihunsu kafin ta nufi gun Anti Safiyya ta rungumeta.Maman Abdul tana jin dawowarta amma kunyan abun da ta mata ya hana ta fitowa shiru ta kara yi a ɗakin.
Wanka ta yi ta canza kaya kafin ta ɗebo abinci ta ci, daga nan suka saka Anti Safiya a tsakiya suna ta hira suna dariya.
Da daddare Abba ya tarasu ya kara musu nasiha akan sun girma su kame mutuncin su ya kuma sa musu albarka. Abduljalil ne ya ciro sabbin waya guda biyu kirar Sony Ericsson mai rufuwa da buɗewa (open and close) mai mugun kyau guda biyu masu fararen jiki sai dai kowanne yana da ɗan ratsin kala atsakiyar sa in aka kira mutum sai ya fara kyalli yana wuta wayar ta yi kyau sosai ya bama Nana mai ratsin ja amatsayin kyautar kammala makarantarta tare da katin ɗari biyar aciki. Itama Kausar ya bata na mai ratsin kalar sararin samaiya a tsakiya.
Take murnan su ya tsananta suka kara gode masa kowacce yasa mata nambansa dana Abba dana Anti Safiyya dana Maman Abdul.
Anti Safiyya ma tayi murna sosai da haka rayuwarsu ya ci gaba da tafiya, da farko Maman Abdul ta ɗan sauko ta soma sakewa da Kausar amma bayan da ta cika wata guda abun ya sha bam bam don sabon babin tsanarta ta buɗe sabida zugan da take samu daga mugayen kawaye.
Abduljalil kuwa kullum cikin kiran Kausar ya ke susha hira a waya ga kalamai irin ta masoya ga abubuwa masu kyau ya ke sayo musu amma bai taɓa furta mata a fili yana sonta ba sai dai yana riritata tana kuma hango zallan sonta a idonsa wanda a yanzu ta gama faɗawa kogin kaunarsa. Abba ya mai da Kausar da su Nana sabon islamiya suna zuwa don sam baya son wasa da ilimin addini Kausar na wata biyu Abba ya haɗa mata goma na arziki ya haɗata da direba ya kaita kauyensu ta kwana biyu a gun iyayenta Kausar murna agunta ba acewa komai kafin su tafi ta roko Abduljalil da kuɗin da Anti Safiyya ke bata wanda Abduljalal ke turowa a bata suka shiga kasuwa ta yi sayya ma yayansu Salame da Aishalle. Bayan sun dawo gida suka ɗau hanyar buzaye.
***
Tun bayan tafiyar Kausar Makarantar kwana haka rayuwar Ummanta ya kasance daɗi da ba daɗi tana hakuri a haka suka shuɗe shekara huɗu lokacin Kausar ta shiga SS1 lokacin akayi bikin su Aishalle da Salame wanda ya zo akusan lokaci guda. Tana makaranta akayi sai da suka dawo hutu ta zo duba iyayenta tukun ta samu labari har gidansu ta je musu da tsaraba sunyi murna sosai.Saude da Karime kuwa awannan shekarun sau biyu suna ciki ana zubar wa. Laure ne tayi aure a wani kauye da ke gaba da su. Abulle kuwa ansha kamata a ɗakin saurayi Malam ya yi duka har ya gaji uwarta kuma bata son laifin yarta. Da kyar wani mai Mata uku ya auri Abulle taje gidansa ta fara masa halin ɓera ga yawan faɗa da matansa hakan ya sake ta saki uku yanzu tana zawarci a gida.
Kausar tafiyan minti arba'in ya iso da su kofar gida Isiya direba na tsaya bata jira shiba ta fito aguje ta shiga gida tana kwala ma Ummanta kira da gudu ta shiga ɗakinsu ta faɗa jikin Ummanta tana murma Umman ma cikin murna ta rungume yarta. Yara ne suka shigo da kayan Kausar da Isiya direba t
ya basu, Umma ta je ta buɗe ɗakin zaure aka shimfiɗa ma Isiya ta barma aka kaimasa nono.Malam tun a hanyar gona ya samu labarin dawowar ɗiyarsa cike da murna ya kara hanzarta tukin koɗaɗiyar babur ɗinsa ladis wanda ta ji jiki sosai ta fita hayyacinya.
ESTÁS LEYENDO
...YA FI DARE DUHU
Ficción GeneralLabarin ƙauna gamida cin amana da tausayi ga uwa uba soyayya.