*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*RASHIDA ABDULLAHI KARDAM
(Rash Kardam)4
Cikin takaici yayi ruf-da-ciki a kan gado sam shi baya son zuwa kauye. Ga su da kallo kamar sun ga sabuwar hallita.“Mtsssw Abba da ka janye tafiyar nan don bana so ba zaka gane bane."
Wani iska mai zafi ya furzar daga bakinsa a hankali ya furta.
“bana son yan kauye ko ma ya ya suke".
Da wannan tunanin ya lumshe idonsa kamar mai bacci.
Abduljalil ne ya turo k'ofa ɗakin cikin zakwaɗin gami da zumuɗi ya hayo kan gado.
“Ya Abdul yau ina murna gobe zamu Buzaye ina son zuwa kauye. Baran kayen Fulani insha nono da na Jarawa in ci dambu gashi sun iya gwaten tsaki mai daɗi da wake a ciki, al'adunsu yana....".
Wani mugun kallon da Abdul ya aika masa dashi ya kasa karasa sauran maganan ta makale a wuyarsa.
“Mtswww menene abin so a Kauye? Bayan Fulani sunfi kowa hauka da kauyanci".
Abduljalil bai tanka ba sanin halin ɗan uwansa yanzu za su iya haurawa in ya nuna zaƙewarsa akan tafiyar.
Da daddare Mummy tayi kwalliya mai kyau cikin salon da ta san tafin jan Hankali Alhaji Nasir da hakan ta isa gunsa cikin kissa da kisisina irin na Mata masu aji da daraja sai da ta bashi hakuri ya sauko nan suka soma faranta majunansu rai cike da so da ƙauna...
Da safe kayan karin kumallo ta haɗa musu. Wanka tayi ta gyara ɗakinta da na Mijinta ta shirya yan makaranta itama ta yi shirin aiki ta fito falo, anan suka yada zango suka yi braakfast(karin kumallo)bayan sun gama ta musu adwo lafiya ta rike hannu Umaira kasancewar ita ce auta kuma k'arama ce ba za'ayi tafiyan da ita ba. Sai da ta kara jama Abdul kunne kafin suka fita zuwa gun aiki.
*******
Kausar Sanye ta ke cikin kayanta na Fulani k'afarta tasha takalmin roba irin na Fulani ga sandarta nan a hannu tana tafe tana wakarta.Gona ta nufa inda Shanu suke huɗa wa Malam ita ka ɗai sai wakarta take yi, ganin zaman ya isheta ita kaɗai. Bishiyar Gwaiba ta hau ta tsinka iya son ranta ta saka a gabanta ko wankewa babu ta fara ci kamar wacce ta samu naman 'Dawisu.
Tun daga nesa ta hango wata Mota lafiyayya mai ɗan karen kyau da sheki tamkar yau aka ɓareta a leda. A yanda take kallon motar ba zata ɗauka zata koɗe ba harta kai ga sufa.
Take taji tana son ta ga su waye a cikin wannan motar. Do ita a sannin ta mota masu kyau basa shigowa garin sai dai in sun fita bakin titi suga suna wucewa.
“Kai aradun Allah wannan Motar mai kyau ne zan so na ga suwaye mutanen ciki yan birni da suka zo garin mu."
Da sauri ta kunto yar ɗan kwalinta ta zuba sauran gwaiban aciki. Ta ɗauko tayanta da ta barta ranar da tazo a gona ta gyara tsayuwanta.
“Buwuun! Buwuun!! Buwuun!!!".
Ta burka tayar tare da samata giya tamkar mashin gudu take bako tsayawa har ta soma hango motar duk da ta mata nisa a haka ta ke binta.
Ba karamin mamaki tayi ba ganin motar ta tsaya dai-dai k'ofar gidansu.
“Kausar! Kausar!! Kausar!!!".
Salame ke kwala mata kira.
Cikin takaici ta juyo don bata son abun da zai katsemata abunda tayi niyar yi.
K'afarta tasaka cikin tayan sai jin cuhhsss! Karan taka burki da tayi nan take tayar ta tsaya, ɗan guntunwar kura ne ya tashi. Cikin rashin fara'a take kallon Salame.
YOU ARE READING
...YA FI DARE DUHU
General FictionLabarin ƙauna gamida cin amana da tausayi ga uwa uba soyayya.