BABI NA GOMA SHA UKU

1.4K 98 5
                                    


*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

   RASHIDA ABDULLAHI KARDAM
               (Rash Kardam)

13
Jin ihu yariya mace ya sa Anti Safiya da Abdulmajid fotowa da gudu har suna rige rigen saukowa don su duba waye ne, Abduljalil ma daga ɗaki ya fito a guje ya rufa musu baya don ihun ba kaɗan bane kuma dagajin ihun kasan mai ihun wani babban abune ya sameta.

Tsaban gudu har ya so ya wuce ta, turus ya ja ya tsaya ganin yarinya da kaya da sunka ɗan koɗe ta tamke idonta sai ɓari ta ke yi, ɗaya hannun kuma ga ɗan kullin sauran kayanta ta matse su a hamatanta. Mamaki ne ya kamasa ko takaicine ya rasa wanne zai yi ɗaya wai shin me ya kawota gidansu yarinyar da ya baro a can kauye ko dai tsaban haushin da ta bashi ne ta ke masa gizo jin ƙafarsa cikin wani abu kamar ruwa ya saurin duba ƙafarsa sai yaga abu kamar ruwa ne ke saukowa daga matakalar da Kausar ta ke ya ke bin tafin ƙafarsa kalo ya bi inda ruwan ke fitowa. Ba daga ko ina bane illa kasan Kausar cikin ɓacin rai don ya gane ko miye wato fitsari ta yi cike da takaici ya nuna ta da ya tsa,

"Ke wa ya kawo ki nan? Wani irin iskanci ne za kk sake fitsari a nan?.

Bata buɗe idonta ba bare tayi wani magana. Takaici ya ƙara kamashi ƙafarsa ya ɗaga ya soma goga mata tafin ƙafarsa a kayanta ya na goge fitsarin.

"Kai Abdulmajid wani irin iskanci ne haka? Kana da hankali kuwa?.

Ce war Anti Safiyya ta na ƙarasowa gugrin da sauri ta kama Kausar. Sam bata yi mamaki ba daman ta san da batun zuwanta. Juyawa ta yi ta kalli Abduljalil ta ce,

"Ma za je ka ɗebo ruwa a saka anan."

Da gudu Abduljalil ya yuya kawo ruwa a jikin ta zuwa kafarta ta samata sannan ta kora ya sauka ta kuma saka ma Abdulmajid a ƙafarsa sannan ta sa Abɗuljalil ya kira Ladiyo mai aikinsu ta gyara gurin haurawa sama ta yi da Kausar.

Abdulmajid kam ransa ne ya ɓaci ba kaɗan ba wato Anti Safiyya akan wanna banza ƴar kauyen za ta masa faɗa to bari Abbansa ya dawo yau ko kwana ba za tayi a gidannan ba za'a fitar da ita. Koma mai ya kawo ta sai ta tafi yau kuma sai ya yi maganinta don ya ga bata da kunya.

Abduljalil kam murna ya ke yi Kausar ta zo yau zaisha dariya, don shirmenta ba ƙaramin burgesa ya ke yi ba.

"Kausar! Kausar!! Kausar!!.

Ya furta sau uku tare da murmishi yana girgiza kansa.

Anti Safiya tana haurawa da ita sama ɗakinta ta wuce da ita, ruwa ta haɗa mata a bayi ta sa ta cire kayanta sai ɗan zani tayi ɗaurin ƙirji ta kaita bayin don ta yi wanka.

Kausar na shiga bayin ta tsaya ta kare masa kalo ita tunda ta ke a rayuwarta bata taɓa ganin guri mai kyau tsab tsab kamar wannan gurin ba. Leka bahon wanka ta yi ta ce,

"Kai wannan ba dai kyauba kamar wajen kwanciya, ko miye wannan oho ansa bikitin ruwa a ciki, ga bakin famfo ma aciki kai ƴan gayu su ji daɗinsu gwamma dana baro ƙauyennan da ba zanga wannan abun ba aradu kwanciyana danyi aciki."

Cikin bahon wanka ta shiga ta kwanta sai dariya take yi.

Kamar ance jiya taga wani ɗan abu a sama ga famfo a jiki gefe kuma ga wani ɗan abu da murfi kamar zata je ta buɗe sai wata zuciyar ta ce mata ke hala randar ruwansu ne sai ta fasa. Fitowa ta yi a bahon wankan tana kalle kale a cikin bayin. Jin kamar alamar mutum yasa ta fito da bokitin wankar kusa da ƙofar bayin ta tsuguna tana wankanta ruwan yana gangarowa cikin ɗakin.

Anti Safiya jin shirun ya yi yawa yasa ta shigo ɗakin ruwa ta gani ɗaga bayi na fitowa cikin mamaki ta ke kallon ƙofar,

"Kar dai ace Kausar ba a cikin bahon wanka ta yi wanka ba?.

Sam ta manta da Kausar ba abunda ta sani a gurin bare ta san miye amfaninsu. Anti Safiya bata gama Mamaki ba Kausar ta buɗe ƙofar bayi ta fito.

"Kausar a ina kika yi wanka?.

Kausar ta nu na mata bakin ƙofar bayin.

Anti Safiyya ta ce,

"Miyasa bakiyi a cikin bahon wankan ba?.

Kausar ta ce,

"Ai na ɗauka gurin kwanciyane."

Dariya ne ya so kama Anti Safiyya sai ta daure ta kira Ladiyo don ta gƴara gurin.

Kaya da mai ta shafa ta bama Kausar kaya ta saka  ta kai ta gurin cin abinci, ta jera mata komai amma ta manta bata sa mata ruwa ba ta sauka don neman Isiya direba ta aike shi. Kausar ta fara cin abinci ta ji tana son shan ruwa ganin ba randa a gurin sai ta tuna da wanda ta gani a bayi. Wasu ƙananun kofuna ta gani guda uku a guri ta ɗau ɗaya tan zuwa ta buɗe bayi a hankali ta ɗaga murfin abun aiko ta ga ruwa kaɗan akwance a ciki, kofin tasa ta ɗiba ta koma falo ganin ruwn ba zai isheta ba ta ɗauki sauran kofuna guda biyun  ta koma bayin ta sa ke kalato ruwan tana tarawa a faya kofin.

Abdulmaji na shigowa yaga ruwa a kofi ga abinci a gefe bai kawo Kausar bane ke ci ya ɗauka Anti Safiya ne don bai ga ta fito gurin karyawa ba ɗa zu ya ɗaga kofin ya kai bakinsa.

Anti Safiya ne ta shigo ganin ba Kausar a gun cin abinci bata tambayi Abdumajid ba ta shiga kwala mata kira.

"Kausar! Kausar!!.

"Na'am."

Ta masa Anti Safiya na jin muryarta a ɗaki tabi bayanta da sauri turus ta ja ta tsaya ganin Kausar da kofuna da ruwa ta buɗe ƙofar bayi za ta fito.

"Kausar mai kike yi da kofi anan?.

"Ruwa na ɗebo nakai can waje na ajiye agun abinci ganin ba zai isheni ba na zo ƙarawa."

Ido Anti Safiya ta zaro.

"A ina kika ɗibi ruwan?.

Da ke bata gama fitowa da ga bayin ba da hannu ta nuna mata gun kashi ido ta zaro tana tafa hannu.

"Kar dai ruwane Abdulmajid ya ke sha a falo."

Maganar kuwa bai sauƙa a ko ina ba  sai a kunnen Abdul.....

*FWA*

...YA FI DARE DUHUWhere stories live. Discover now