✏📖
*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*RASHIDA ABDULLAHI KARDAM
(Rash Kardam)Wannan shafin naki ne
*Sanah Sulaiman Matazu*
(Ummu Beenah)57-60
Kai ya girgiza yana jin lalle zai yi ƙoƙarin cika umarnin Mummynshi yau harta na haɗa shi da Allah.Amsa mata ya yi zai kiyaye nan suka ci gaba da ƴan hiraraki, Abduljalal bai bar gidan ba sai bayan sallah azahar.
Maman Abdul gidan ya mata ba daɗi sai yau ta ƙara tabbatar da danga da mutum ya fi danga da kara. Rashin Safiyya a gidan taji ba daɗi koba komai tana rage mata ayyuka ga motsinta ma kaɗai tana jin daɗi ƙalƙe jama'a ma rahma ne. Ta ke ta fara dana sanin irin kiyayya da cin zaragin da ta mata, tasan Safiyya ta fita komai na rayuwa ta wulakanta ɗanta da Mahaifinsa ya kasanace mai kuɗi fida mijinta a kuma ta kasanace ƴar uwar mijinta amma son zuciya yasa ta aikata haka jikinta ne ya yi danyi harta soma kuka da haka bacci ya yi awon gaba da ita...
Abduljalal cikin shirinsa ya fito ƴar ƙaramar y
jakarsa ya rataya a gefen ƙafaɗarsa, kasancewar ya yi sallama da kowa fuskansa ɗauke da murmushi mota ya shiga direba ya ja sa zuwa filin tashin jirage...
***
Cow boy cike da farin ciki ya sauko daga jirgi a hankali ya ke takowa duk da ba karonsa na farko zuwa kasar India ba kenan amma wannan karon yana jinsa cikin farin ciki.Ga kuma a shekara ɗaya haɗuwarsu da Nanda don yanzu cikin sauki ya ke zuwa ya gama harƙoƙinsa, wannan karon ma ya shigo da kwayoyi da kuma hodar ibilis wanda aka shigo da shi ta cikin jirgin ruwa. A hankali ya ke tafiya har ya iso motar da aka zo ɗaukarsa baƙa ce mai baƙin gilashi. Cike da nishaɗi ya ke kallon titunan gari jinsa ya ke cikin wani irin yanayi da haka har suka iso ƙofar gidan da zai sauƙa.
Jakarsa ya wurga a kan gado ƙafin ya ajiye wanda ya ke hannunsa, yayoyi ya ciro sunkai guda biyar wani karamin zif ya ja yasa hannunsa ya ciro layukan waya sun kai guda goma, waya biyu ya buɗe ya saka layi guda uku ya ajiye wayar. Wanka ya shiga ya yi bayan ya fito ya kira waya aka kawo masa abinci da zai ci. Bayan ya ci abinci wayar Nanda ya kira ya shaida masa yana cikin kasar India don su saka ranar da zasu haɗu.
***
Kausar ɗaure ta ke da shawul ɗin wanka ɗaya tana goge jikinta Suhana ce ta banko ƙofar ɗakin kallo ɗaya zaka mata kasan abirkice ta ke.Bakin gadon ta zo ta zauna ta dafe kanta idanunta ɗauƙe da damuwa ta rasa ta yaya ma zata soma yin bayani ma Kausar.
A hankali Kausar ta tako zuwa kusa da Suhana ta zauna tare da dafa kafaɗarka ta ce,
"Suhana mai ya ke faruwa? Mai ya same ki duk naga a birkice kike?.
Suhana kai ta ɗaga tana kallon Kausar cike da tausayi ta ke taji jikinta ya ƙara sanyi idanunta ya cika da kwalla. Cikin salon lallashi ta soma magana.
"Kausar!"
Suhana ta kira sunanta a cikin salon karyar da zuciya
"Na'am Suhana."
Kausar ta amsa.
Suhana ta ci gaba da cewa,
"Kausar ki yi haƙuri da yanda kaddaranki ta zo miki mai kyau da maras kyau. Kuma san cewa bawai Allah ya manta da ke bace a'a yana sane da ke, ki ɗauƙa hakan shine alkairi a rayuwarki ki yi imani da Allah kuma amshi dukkan abun da ya zo miki kona farin ciki ko na baƙin ciki."
Cike da tsoro Kausar ta ce,
"Suhana ki faɗa min mai ya ke faruwa dan Allah."
Cikin rawar murya ta ke maganar gaba ɗaya ta tsorata don bata san mai zai fito da ga bakin Suhana ba.
YOU ARE READING
...YA FI DARE DUHU
General FictionLabarin ƙauna gamida cin amana da tausayi ga uwa uba soyayya.