✏📖
*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*RASHIDA ABDULLAHI KARDAM
(Rash Kardam)16
Da gudu Anti Safiya suka yi gun do wannan karo hannunta ke yawo a samam ruwa alamar ta soma shan ruwa tana nitse wa kasa tana tasowa. Abduljajil ne ya zo da gudu ya yi tsalle ya faɗa ciki ruwan don ceto ran Kausar.Sai a lokacin Abdulmajid ya umarci Jeddy da ya koma ɗakinsa da gudu Jeddy ya tafi yana ɗan haushinsa. Ko ya nuna alamar da muwa shima ya juya da gudu ya haura matakalar ya nufi ɗakinsa ya kwanta yana tariyo abun da ya faru wani sabon takaicine ya ƙara turnuƙesa tsaki kam yayi ba adadi.
Kasan cewar Abdulhajalil ya iya ruwa bai samu wahala ba waje kama Kausar sai dai ta ɗan masa nauyi ne sabi da jikinta da ya sake. Miƙata ya yi ma Anti Safiya ta ajiye ta a gefe ganin cikinta ya ta so yasa ta saka hannunta ta danna cikinta nan take ruwa ya soma fita ta bakinta da hanci kasancewar ruwar ba ta sha da yawa ba nan ta fara attishawa sosai.
Abba da ya jima a tsaye a bakin gareji daga shigowarka gidan ya ga lokacin da Abduljalil ya faɗa cikin ruwan don ceto ran Kausar ya na kallon yanda Anti Safiya ta taimaka mata da sauri ya ƙaraso cikin gidan yana tambayar,
" Safiya ɗauketa mu ta fi asibiiti kawai,"
Anti Safiya ta ce,
" Za ta tashi da ikon Allah yanzu ma ba matsala ta farfaɗo bakomai da yarda Allah."
Sam Abba bai yarda ya ƙara mai maita masa abunda ta faɗa a baya da kyar ya yarda.
Anti Safiya ne ta ɗauketa cak su ka nufi cikin gida ta kwantar da ita kayan jikinta ta cire mata sabida gudun sa mata mura zazza6i maganin zazzaɓi ta bata ta sha daga nan kuma ta bata shayi mai kauri ta sha ta kwanta nan da nan bacci ya dauketa.
Abba ɗakinsa ya shiga don yau ba zai fita aiki ba sabida yana hutun ranan ne ya kamata su dawo daga tafiyar da su ka yi. Ruwa ya watsa ya kwanta kafin kausar ta farka don bacci mai nauyi ya dauketa. Abba sam bai ji dadin faruwar haka ba har ya fara tunanin sa afitar da Jeddy daga gidan sai ya tuna in yayi haka bai kyauta ma Abdulmajid ba. Sam Abba bai san mai ya faru tsakanin Abdulmajid da kausar ba.
Kausar bata farka ba sai bayan sallah azahar lokacin Maman Abdulmajid ta dawo daga gun aiki duk suna falo suna zaune, kausar na farkawa ta fito tana ta murtsike ido Abba na ganinta ya ce,
"Zo nan diyata ya jikinkin?.
Wani kallo Mamin Abdulmajid ta bita da shi ba laifi ya rinyar kyakyawace sai rashin wayewa da tsafta sam bata so ganinta haka ba don bata ga wani makusa a jikinta ba sai ƙazantar nan da rashin wayewa.
"mtssw."
Maman abdulmajid ta dan yi tsaki duk bata so ganin yarinyar haka ba amma to miye don yaso taimaka mata har sai ya dauko ta daga gidansu ta shiga cikin yaransa ga shi ta ga Safiya na ta wani rawar kai ta ke yi akan yariyar.
Abduljalil na ganinta ya kwashe da dariya Abba ya kallesa ya ce,
Masa lafiyarka kalau kuwa?
Abduljalil ya amsa masa da
" Lafiya lau abba."
Nan Ya fara basu labarin abunda ya faru amma ya ɓoye ma Abba dukan da Abdulmajid ya yi ma Kausar kowa dariya ya keyi a falon harda su Umaira Nana khadija kam kallon ɗaya ta yi maKausar taji tana mugun Kaunar yarinyar kusa da ita ta koma ta zauna.
Maman Abdulmajid najin haka ta soma sababi wai ga irintanan daga zuwanta tasa danta ya sha ruwan bayi, ganin fushin da Abba ya yi ne yasa ta mike ta kama Umaira ta nufi dakinta Abdulmajid kam ransa ya gama baci badon tsoron fadan Abba ba da yau Abduljalil ya yi bayani kuma ganin Kausar a falon ya ji sam baya kaunar zaman gurin so ya ke ya tashi ya kasa sabida tsoron Abba.
YOU ARE READING
...YA FI DARE DUHU
General FictionLabarin ƙauna gamida cin amana da tausayi ga uwa uba soyayya.