BA BI NA HAMSIN DA BIYU ZUWA HAMSIN DA UKU

1.3K 64 3
                                    


✏📖
*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

   RASHIDA ABDULLAHI KARDAM
               (Rash Kardam)

*WANNAN SHAFIN NAKI NE ANTI ZEE DAN MALIKI (MAI HADARIN NAIRA) BAUCHI ALLAH YA KARE MIN KE ANTINA TA GIDANMU😍😍*

52-53
Tun da Kausar ta tafi Nana ta ke jin gidan ya mata wani iri Abduljajil kuwa ya na zaman jiran sakamakon gwajin aiki da yayi, ganin yana zaman banza ya nimi koyarwa a wani karantar kuɗi yana ɗan samun na kashewa. Maman Abdulmajid kuwa kulum cikin tunanin ɗanta take yi zuciyarya cike da kewarsa amma ina ba shi ba labarinsa wani lokacin ta yi kuka har ta gode ma Allah.

Abba kuwa tamkar abun bai dame sa ba yana sabgoginsa yake yi. Jarabawarsu Nana Khadija na Neco ya fito ta samu credit shida hakan yasa Abba ya sayo mata form na N C E ta cike ba su jimaba aka kira gwaji in da ta samu gurbin karatu a ATAP zata karanci English Islamic. Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya musu daɗi ba daɗi.

Abba na zaune a falo ranar lahadi ya kunna radiyo yana jin labarai nan ya ji ana faɗan mumunan tsautsayin da ya afku a BUZAYE ruwa ya musu ta'adi inda aka rasa rayuka da yawa wasu kuma sun ƙaura sun bar garin. Cikin tashin hankali ya nufi ɗakin Safiyya nan ya kira ta ko da ta fito ya ce,

" Safiyya ɗauko mayafinku zamu tafi Buzaye yanzunan."

Suna isa Buzaye duk an watse ga gidajen gurin ya shafe hankalin Abba ya tashi nan ya fara niman Malam Hummad Hassan ta ke wani ya shaida masa ya ai ya tattari iyalansa su  koma kasarsu. Abba hankalinsa ya matukar tashi ya Malam Muhammad zai yi haka ko ya manta da yarsa Fatima Kausar ne? ji kinsu ba kwari suka dawo don ba wani cikakken bayani akansa sun dai san mutumin Nijar ne ya zo nan fatauci ne kasar Nageria.

Haka sukadawo gida basu bi ta kan Maman Abdul ba don sunsan ba abinda da zai dameta Abba ya hana kar a fada ma Kausar abun da ya ke tafiya. Abduljalil ya matukar tausaya mata da iyayenta suna waya da Kausar amma hakan baisa ya fa ya fada mata ba. Anti Safiyya ta jin-jina lamarin ta sanar ma Abduljalal ta hana kar ya faɗa mata. A hankali rayuw ake tafiya har sun tasamma cin shekara ɗaya.

Anti Safiƴya ta kira Abduljalal  ta bukaci da ya zo Najeria ayi maganar Auresu kawai da Kausar don a iya tunaninta bata ga wanda ya dace ya rike amanar Kausar sai ɗanta don zata saka shi kuma zata hana shi.

Abduljalal ya shirya batare da ya ja dogon lokaci ba ya zo  Najeriya kowa ya yi murnan ganins nan ya cika su da tsara ba a gidansu ya sauka Alhaji Ahmad Dan zaki yayi farin cikin ganin dansa sosai, Abduljalal bayan ya huta ya sami Daddynsa da maganar auren Kausar kuma Mamansa ta aminta da yarinyar da halallayrta da goyon bayanta akan niman auren yanzu na shi ya ke nima.

Alhaji Ahmed Dan Zaki ya ce,

" Sam bai min ba ni ban goyi baya ba ai ba Safiyya ce kaɗai ke da iko akan ka ba da har ita zata maka wannan zabi.'l"

Abduljalal ya ji zuciyar sa ta koɗa cikin tari bacin rai bar gidansu ya nufi gidansu Abdulmajid ɗakin Anti Safiyya ya nufa ya sanar mata abu da ya ke tafiya.

Anti Safiyya ta ce,

"Abduljalal ka lallaba Baban ka har ya amince ka yi auren nan mafaifi ne dole sai ka bisa a hankali."

da haka Abduljalal ya amince

Abduljalal tun da ya zo kullum cikin lallaɓa Daddynsa ya ke yi akan maganar auren amma ya tubure ya ce shi bai san wannan zancen ba

ran anti safiyy ya baci nan ta sanar ma Babansu Abdulmajid abunda ya ke faruwa  bai ce mata komai ba, ya kira wayar Alhaji ahmad Ɗan Zaki  bayan sun gaisa ya abukci yana son ganinsa za su tattauna ba tare da bata lokaci ba ya amsa da zai zo.

...YA FI DARE DUHUWhere stories live. Discover now