✏📖
*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*RASHIDA ABDULLAHI KARDAM
(Rash Kardam)Wannan shafin naku ne *FIKRA WRITER'S ASSOCIATION*
Aisha Ya'u Kura
Batooul Mamman
Farida Abdullahi
Fulani Ɓingel
Khadija Sidi
Ummu Hanan
Ummu Abdoul
Lubna Sufyan
Rofaida Omar
Rash Kardam
Sanah Shahada
Sanah Matazu54-56
Abbansu Abdul yana ganin saƙon Safiyya murmushi yayi don yasan ba ko shakka taji abunda ya ke faɗa a waya burin shi kenan da fatansa wayar ya mayar aljihu fita waje.Cikin abokansa ya shiga suna gaisawa Abduljalal kuwa bakinsa har kunni yana gaisawa da abokanansa ya sha fararen shadda gezina fara sol da farin takalmi farin hula ba ko ɗigon baƙi a jikinsa hatta aikin kayan ma fari ne, hakan ya ke bayyana zallan farin cikin da ya ke ciki duk da ba tarewa amaryar zata yi ba don ana ɗaura aure jumma'a ranar litinin zai wuce don ana nimansa a gun aiki sabida ya kusa kammala aikin da ya riƙe shi saura wata ɗaya da sati biyu.
Abuljalil fuskansa kamar ya kurɓi kanwa murmushin dole yake yi, zuciyarsa tana masa tuƙuƙi da zafi yana danasanin adana son Kausar da yake yi a zuciyarsa na har sai ta dawo gashi yana ji yana gani za ta masa nisa garin kallon ruwa ƙwaɗo ya masa ƙafa.
Hmm!
Ya sauƙe wani sassanyar ajiyar zuciya ya soma karanto addu'o'n tafiyar da kuncin zuciya....
Jama'a da ya ga suna nufo Abduljalal da ke can karshen layin shigowa Masallaci Jumma'a da ke Igbo Quaters suna masa murna hakan ya tabbatar masa da cewa an ɗaura auren Kausar da Abduljalal, Anti Safiyya da Ahmad Dan Zaki. Maroka ne suka soma sana'arsu, Abduljalal duk inda ya yi karo da maroƙa rafan kuɗi ya ke ciro ya ke watsa musu fuskansa ɗauke ya ke da annuri farin ciki kuwa ba'a misaltashi.
Abbansu Abdul bakinsa har kunni yau kam ya cika burinsa ga shi ya aurar da Kausar ya cika alkawarin da ya ɗauka duk da bai sanar da iyayenta ba. Ta ke jikinsa ya yi wani sanyi tabbas sai yanzu ya ga kuskuren da ya yi na aurar da Fatima Kausar ba tare da sanin iyayenta ba, anya ya musu adalci kuwa? Mai ya rufe masa ido da har ya aikata haka tun da Safiyya ta zo masa da maganar bai yi tunanin haka ba ganin ba'a san inda iyayenta suka nufa ba jiki a sanyaye ya nufi cikin gida don shiryawa za su wuce wajen Walima.
Abba na shiga gida ruwa mai sanyi ya sha kafin ya ɗan huta sabida zafin da kansa ya ke masa. Wanka ya sake yi ya sauya wani kaya nan suka nufi Zaranda Hotel don anan za'a gudanar da walima.
Ango Abduljalal shima kayan ya sake shaddace ruwan madara ta sha aiki kalar dark brown takalminsa da hularsa kalan aiki, farar gilashi mai kyau da tsada ya sanya a idonsa ango har ango, ko mahassadansa iya kaci hotuna ya tsaya ɗauka a wayarsa shi da abokanansa suna gamawa suka shiga mota suka nufi ZARANDA HOTEL.
Walima ta yi walima don aci ansha an kuma raba kyaututuka na ban girma don Alhaji Ahmad Dan Zaki ya kashe kuɗi bana wasa ba, sabida bikin ya masa kashi biyu ne nasa da na ɗansa...
Bayan sun dawo gida tsirarun abokan wasa wanda suka zo tafiya da Anti Safiyya Miri suka yi ta tsokanarsu duk da taron bikin a MIRI za'a yi sabida nan ne asalin gidansu Safiyya kuma sabida basa son asamu matsala da Aisha shiyasa suka zaɓi hakan.
Murmushi kawai ya ke musu yana basu amsa don shikam yau bakinsa har kunni. Bayan wucewarsu ya shiga ɗakinsa na gidan ya cire babban garensa ya kwanta zuciyarsa cike da farin ciki.
Wayar su Kausar ya kira a kashe cike da tunani ya ƙara lafewa a fillo ya ɗauko ɗaya ya rungume zuciyarsa fari ƙal yau burinsa ya cika Kausar ta dawo mallakinsa kaman yanda ya ke fata.
A Miri kuwa walima na gani na faɗa suka shirya sam Anti Safiyya bata so tunda ita wannan auren bawai farin ciki ta ke yi dashi ba. Malama Khadija ne ta gabatar da lakca akan zamantakewar aure da yan nasihohi daga nan aka rarraba abubuwan ci da sha aka rufe da addu'a aka watse.
Da daddare tamkar ɗaukan budurwa motoci Alhaji Ahmed Dan Zaki ya turo suka ɗauki Amarya da jama'anta....
Washe gari ta kama yini Anti Safiyya ta yi kyau sosai don angonta ya fito da ita akwati saiti ɗaya ya mata cike da kaya masu tsada ga kyautar makullin mota aciki wannan na murnar ta dawo gidan shi ne. Ya kuma gyara mata gidansa da ke New G R A anan ya ajiyeta.
Ƴan biki sunci sun sha a haka akayi yini aka watse, misalin ƙarfe goma ango ya shigo cikin fararen kaya sai zuba kamshi ya ke yi.
Anti Safiya da ke gefen gado tana sharɓan kuka tamkar budurwar da ke kewan rabuwa da iyayenta. Alhaji Ahmad ya ta ko a hankali sallama ya mata bata ko kallesa ba sanin muhimmancin sallama yasa ta amsa masa ciki-ciki.
Murmushi ya yi ya zauna kusa da ita ta matsa ciki ɓacin rai ta ce,
"Ka ga ni kar ka kuskura ka matso in da na ke, kai har ka manta mai ka aikata cikin kuka ta ce, ka san illar zina kuwa? Mai zai kareka duk matanka ba mu maka ba ace sai ka nimi yar..."
Bata ƙarasa ba ya tsuguna a ƙasa idanunsa sun ƙaɗa sunyi jajazur ya ce,
"Safiyya ki gafarce ni ki ya feni nasan na *TAFKA BABBAN KUSKURE* da na zo ina dana sani. Safiyya sharrin shaiɗan ne ban san ya akayi zuciyata ta ingiza ni na aikata hakan ba. Na yi nadama matuka ki tausaya min ki gafarce ni nasan kin min hallacin da ba kowacce mace ke iya wannan hallacin ba. Kin rufa min asiri amma me duk da haka ina tunanin makomata a gun Ubangiji amma sai dai ki sani ba da sona nayi ba hasali ni bansan ya akayi na je ga yar aikin ki ba kuma acikin gidanki."
Ko kallonsa bata kuma yi ba ta tashi ta fito falo shima biyo ta ya yi ganin zai takura mata ta sake komawa ɗakin ta saka masa makulli ba tare da ya zare ba ta faɗa kan gado tana ruzar kuka.
A haka bacci ya ɗauke ta da asuba sallah ta yi bayan ta idar ta yi ƴan addu'o'inta ta koma bacci ..
Musali goma da wani abu Abduljalal ya shigo gidansu Daddynshi ya samu a falo yana zaune bayan ya gai dashi ya zaunna a gefe. Abba ya je ya kwankwasa mata ƙofa tare da shaida mata Abduljalal ya zo.
Anti Safiyya ta fito cikin shiga ta alfarma sai ƙamshi ta ke zubawa, Daddy ta ƙasan ido ya ke kallonta yana haɗiye wani miyau don yana mugun kewar Safiyya.
Cikin girmamawa Abduljalal ya gai dasu, madafi ta shiga ta shirya musu kayan karin kumallo ta kawo musu...
Bayan sun karya suka taɓa hira Daddy ya ɗan fita Anti Safiyya ta kira Abduljalal ɗakinta nasiha ta masa game da aure da yanda zai riƙe matar sa amana, sannan duk yanda rayuwa ta zo masa da kaddara ya amsa da hannu biyu ya yi godiya ma Allah kada ya kasance mai butulci.
Kan Abduljalal a duke yana mai jin nauyin Mamansa sosai.
"Abuljalal."
Anti Safiyya ta kira sunansa.
"Na'an Ummi na."
Ya amsa mata cikin girmamawa.
Cike da jin daɗi Anti Safiya ta amsa tana wani ƙasaitaccen murmushi ta ce..
"Ban yarda ka bi gun Kausar ba, ka hakura sai ta dawo dan Allah. Kar kuma ka matsa mata da kira ka barta ta yi karatunta cikin nutsuwa tunda sun kusa kammalawa bana son ta kasa hankalinta gida biyu kuma wannan ita ce damanta na ƙarshe a fagen karatu kuma ta samu sakamako mai kyau."
Kai ya girgiza yana jin lalle zai yi ƙoƙarin cika umarnin Mummynshi yau harta na haɗa shi da Allah.
Amsa mata ya yi zai kiyaye nan suka ci gaba da ƴan hiraraki, Abduljalal bai bar gidan ba sai bayan sallah azahar.
*FWA*
YOU ARE READING
...YA FI DARE DUHU
General FictionLabarin ƙauna gamida cin amana da tausayi ga uwa uba soyayya.