✏📖
*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*RASHIDA ABDULLAHI KARDAM
(Rash Kardam)17
Abba ya kalli Kausar ya ce ina son gobe za muje makarantar su Nana Khadija acan zan saki sai kuna zuwa tare ko?.Kai Kausar ta daga masa alamar eh sai Abba ya ci gaba da cewa
"Kausar ina son kiyi karatu sosai kinji? Yanda in Abbanki ya ganki zai ji dadi sosai.'
Sai alokacin ma ya tuno mata da zancen makaranta ita kuma ban abunda tafi tsana kamar karatu hmm ta sauke wani sassanyar ajiyar zuciya'
Muryar Abba ne ya katse mata tunaninta yana musu nasiha ya na kuma fada mata in tayi kokari zai mata kyauta sosai.
Kausar baki ta wa washe tana murna Abba shima biye mata ya ke sunata hira tana msa shirme haka kurum ya ji yana son sauraron shirmenta yana burgesa.
Jiyowar da Abba ya yi ne ya ga shatin bulala ya kwanta a jikinta da sauri ya ce,
"Kausar wa ya da ke ki? Mai ya same ki anan har jini ya kwanta haka?.
Duk a lokaci ɗaya ya mata tambayar ta ke cikin Abdulmajid ya bada sautin kululu! Don ya sam Abba ba zai masa da daɗi ba fuska ya ɗaure yana kallon Kausar ta inda zata kalleshi wani mugun kallo ya soma aika mata da shi mai alamar in kika faɗa zaki sani.
Baki ta murguɗa masa ta yanda ko Abba bai gani ba. Ta masa dariyar mugunta mai nuna alamar banfa manta ba bakuma zan kyaleba sai na rama.
Anti Safiya tana tsoron kar Kausar ta faɗa ma Abba gaskiya zai yi faɗa sosai ko ya sa afitar da Jeddy hakan kuma zai iya kawo musu matsala a gidan.
Kausar ta juya tana kalon Abba da niyar ba shi amsa.
Muryar Anti Safiya ne ta ji ta na ce wa
"Ina ga faɗuwan ruwa da ta yi ne ya mata haka sabida wasan da su kayi da Abdulmajid ɗa zu. Kasan farin mutum ba wuya tabo abu kaɗan ya tashi bare ita da ta ke fara sosai.
Soaroro Kausar ta yi tana kallonta ta so a faɗa ma Abba amma ganin irin taimakon da Anti Safiya ta mata bazata ƙaryata ta ba don haka za ta rama da kanta za ta kaɓi ƴanci ma kanta.
Abba ya mata sannu nan ya soma yi ma Abdulmajid faɗa akan wasan banza.
Abba ya ci gaba da musu nasiha nan ya miƙe zai ta shi ya ƙara jadda maganar makarantar Mamin Abdulmajid ta fito ta ce,
"Ina ba zai yiwu ba sai dai in akaita na gwamnati ya ma za'ayi ace matsayin ta ya zama ɗaya da 'Ya'yana ina ba zai yiwu ba."
Ran Abba ya ɓaci wai wani irin hali Aisha ta ke son ɓullo masa da shi a gidansa abunda basu taɓayi agaban Yaransu ba yau ta masa gudun kar ya biyemata a gaban yara ya wuce ɗaki ta bi bayansa ita ma tana kananun maganganu.
Ya na shiga itama ta shigo nan ta fara sababi sam ba za'a saka ta a makarantar kuɗi.
Wani mugun kallo Abba ya aika mata dashi ya ce,
"Aisha kin yi kaɗan ki canza min ra'ayina ke kike da iko akan yaranan ko kuma ni to ba fashi saina kaita makarantar kuɗi makarantar Nana Khadija."
Ya fita ya bar mata ɗakin itama cikin fushi ta nufi ɗakinta. Wayar ta ɗauka ta kira kawarta Lazuya Muhammad nan ta faɗa mata abunda ya ke faruwa, nan ta yi bata munanan shawara akan Kausar tana ingizata. Bayan sun gama ta kira Hajiya Umma nasiha ta mata sosai amma ina shaiɗan na mata zugazugi a cikin zuciyarta.
Da haka har dare ta yi kowa ya ci abinci Kausar kam jin daɗin miya ta ci abinci ba kaɗan ba. Da haka suka kwanta Kausar a ɗakin Anti Safiya ta kwanta...
Washe gari da safe Anti Safiya ta ciro sabon buroshin Abduljalal wanda bai fara amfani da shiba ta kai Kausar bayi ta samata makilin ta bata ta gwada mata yanda zata yi. Kausar na saka buroshi a bakinta da taji zaƙi ta kama lashewa tass! Ta lashe makilin ɗin tana lallashe buroshi ɗin Anti Safiya tana lekowa don duba Kausar kar tayi wani taɓargazan taga ta lashe makilin tass.
Anti Safiya ta riketa ta saka makilin a buroshi ta fara wanke mata baki sai da taga bakinta ya yi haske tukunna ta kyaleta ta fito. Gurin sallah ma sai da ta tsaya akan Kausar tukunna ta yi mai kyau. Addu'an safida-da-maraice ta sata tayi kafin suka koma suka kwanta.
Sai da gari ya waye tukunna suka fito cin abinci nan ma sai da Kausar ta zuba kauyanci kafin Anti Safiya ta zaunar da ita. Ruwan shayi ne da soyayyen dankalin turawa da sauran kayan motsa baki sai da aka zu ba ma Abba sannan suka fara ci.
Shugaban jiji da kaine ya shigo gurin cin abinci duk kujerun zama kowa na kai sai guda ɗaya da yake kusa da Kausar ɗan karamin tsaki ya ja da niyar Juyawa Abba ya dakatar da shi ya sa ya koma ya zauna dolensa akusa da Kausar.
YOU ARE READING
...YA FI DARE DUHU
General FictionLabarin ƙauna gamida cin amana da tausayi ga uwa uba soyayya.