BA BI NA ARBA'IN DA TAKWAS ZUWA ARBA'IN DA TARA

1.2K 75 1
                                    

✏📖
*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

   RASHIDA ABDULLAHI KARDAM
               (Rash Kardam)

48-49
Abduljalal tazi ya shiga ya koma otal din wanka ya yi ya kwanta cike da ƙaunar Kausar a zuciyarsa shi kaɗai kawai in ya tuna yanayinsu na ɗazu sai ya saki wani malalacin murmushi.
                          ***
Kausar suna shiga ɗakin Suhana wanka suka yi kafin suka kwanta zuciyarta cike da tunani Abduljalal da Abduljalil ga irin nauyin Anti Safiyya da ta ke ji da kunyarta in ta nuna bata son ɗanta.

Suhana ce ta juyo a hankali ta kalli Kausar ta ce,

"Kausar Abduljalal ya na matuƙar sonki da gaskiya yau na ƙara tabbatar da haka gashi kyakyawa ga saukin kai dan Allah ki soshi kamar yanda ya ke rokonki. Kausar samun masoyi na gaskiya kamar Abduljalal yana wahala a wannan zamani duk yawanci samarin yanzu  *MAYA'UDARA* ne yanzu.

Suhana ta ɗan ja numfashi ta ci gaba da cewa,

"Soyayyar gaskiya ta Mayaudari tana da wahalar ganewa, domin a yaudara ma soyayyar gaskiya ya ke yi. Ina baki shawarar da ki bar wanda zuciyar ke bulayi wanda banga alamar yana sonki kamar yanda Abduljalal ke miki ba. Kausar da ma ɗaya ta ke zuwa wa mutum karki sake ta kufce miki ki son Abduljalal ba za kiyi dana sani ba in Allah ya yarda."

Hmmm!

Kausar ta sauƙe wani sassayar ajiyar zuciya cikin muryar mai sanyi ta ce,

"Suhana nima ina son zuciyata ta so shi amma sam na kasa zuciyata Abduljalil ta ke so sabida shine murumin da yafara nuna min kauna ya zauna dani batare da ya kyama ce ni ba. Suhana kinsan ko ni wacece a gidansu Abduljalal?.

Kai Suhana ta girgiza alamar a'a.

Kausar filo ta jigina da jikin gadon ɗakin ta fara ba ma Suhana labarin ta tun daga lokacin zuwansu Abdulmajid da Abduljalil ƙauyensu da irin tsanar da Abdulmajid ya mata da Mamansa. Hatta hasaadar karatun da Maman Abdul ta mata bata ɓoye ba da irin ƙaunar da Anti Safiyya ta ke mata tun da ta zo gidan da irin burin ta na ganin cewa Abduljalal ya aureta.

Wani mugun tausayin Kausar ya kama Suhana  amma dariya da irin fitinar Kausar take yi sosai tana jin-jina rashin jin magana irin na kausar. Ta kuma tausaya mata matuƙa nan ta kudura a zucoiyar ta lallae zata je har kasan su Kausar kuma in ta tashi tafiya zata saka Babanta ya mata kyauta na girma.

Suhana ta nisa ta ce,

"Kausar kin san wani abu da na fahimta  labarin ki tsakanin ki da Abdulmajid."

Kausar ta nisa ta ce,

" a'a sai kin fada."

Ajiyar zuciya Suhana ta yi ta ce,

"Abdulmajid ya na sonki son da shi kanshi bai san yana yi ba kuma kinsan wani lokacin kiyayya yana kowa soyya fa."

Kausar ta wani bata rai ta ce,

" Allah ya min tsari da wannan mugun wanda yanzu haka ma ba'a san inda ya ke ba tun da ya fita karatu ya gudu bashi ba labarinsa."

Murmushi Suhana ta yi tare da fatan Allah ya bayyana shi, da haka suka kwanta washe gari ya kasance ranar hutun karshen sati hakan yasa ba makaranta da wasu ma'aikatar.  Kausar da Suhana girki mai lafiya suka yi ma Abduljalal Suhana na taya Kausar har suka gama suka yi wanka suka ci ado Kausar ta yi kyau har ta gaji.  Karfe shadaya da ƴan min tuna Abduljalal ya iso gidan Suhana, kwankwasawa ya yi suka masa izinin shigowa tun da yasa kafansa a cikin gidn ya zuba ma Kausar na mujiya ta yi matukar kyau acikin shigan sari riga da wando kayan ya karbeta kamar ita ma yar kasar ce. Cikin falo suka masa izini ya zauna suka gabatar masa da abinci  zama ya yi ya soma cin abinci santi ne ya soma dibarsa a hankali ya ke ci sai da yaji ya koshi sosai sannan ya yi Hamdala ya mike y koma gefe hira suke yi da Suhaana amma idonsa na kan Kausar sun dan jima kafin ya bukaci da su je gun hutawa . *KASHMIR GATE*  suka nufa sun dan jima tare da yin yan ciye-ciye sai kusan sallar la'asar suka bar gurin suka koma gida. Abduljalal bai bar gidan ba sai bayan sallah isha'i ya koma masaukinsa...

Washe gari da suka fita har gidan Kausar suka je nan ta dan ɗauki abunda zata bukata don Abduljalal ya ce su zauna da Suhana zaifi mata ita daya gwamma su biyu hakan yasa suka ɗibi abunda za ta bukata kafin su zo su kwashe sauran kayan. bayan sun fito yau *INDIAN GATE* suka je nan suka dan huta kafin suka dawo.

Akwana biyun da Abduljalal ya yi, ya ajiye ma Kausar wani matsayi a zuciyarta da haka ya cika su da kudi da tsaraba ya koma ranar  litinin da safe.

Sannu a hankali rayuwa ya ke ta fiya yanzu Kausar har sun ci shekara daya yaunza su tafi hutun karshen shekara. Suhana ta matsa Kausar sai dai ta bita Mumbai suyi hutu a can, amma ta ki hakan yasa ta yi fushi ta fita harkanta don ko wani hutu sai Suhana ta Kausar amma sam ta ki, ganin Kausar bata da niyar yarda yasa ta kira Abduljalal ta fada masa ya kira Kausar yasa ta dole ta shirya ta bi Suhana Mumbai.
               *****
Cow Boy sannu a hankali ya tako ya iso gurin yarinyar da ta taba sace masa kudi akan ya dauko ta zata haɗa sa da wani tantirin ɗan safara da kwayoyo nan ta masa sata ta gudu, ya na zuwa sai ya ga Suhana da wacce ta ke magana take gaban sa ya fadi da sauri ya damke hannun yarinyar amma idonsa na kan Suhana da yarinyar da suka fita wacce ta ke da surar da duk wani lafiyayyen namiji ya ganta sai ya yaba ganin yanzu ba sune a gabansa ba ya sa bai bi ta kansu ba. Janta ya yi har waje suka fito mota ya shigar da ita tare da nuna mata bindiga damƙe bakinta tayi hannunta ya ɗaure mata shi ta baya ya sake ɗaure mata idonta da bakin kyalle ya kuma mata kashedi dannan ya tada motar da zai nufi ROYAL HOTEL da ita ko mai ya tuna sai ya juya kan motar ya nufi wani gida da ya ke nesa da su suna isa ya sauƙo ya buɗe gidan ya shiga ya buɗe gareji kafin ya dawo ya jawo motar ya shigar da su. Yana fitowa ya zaga ta ɓan garenta ya aza mata bindiga aka ya gito da ita suka nufi cikin gidan.  Suna shiga wani ɗaki da ke ƙarshe a cikin gidan ya nufa da ita, kaca ya ɗauko tare da kwaɗo ya haɗa ƙafarta da jikin wani ƙaton karfe ya ɗaure nan ya wanka mata mari. Duk ta gama tsurewa sanin irin halinsa da ta ji faɗa, tana kuma dana sanin satan da tamsa da ƙaryan da ta masa. Cikin harshen turanci ya ke mata tambayoyi tana bashi amsa nan ya buƙaci ta bashi namban Nanda ta ce ita bata dashi wayarta ya zaro a jikinta ya duba yaga ba sunan Nanda hakan ya ƙara fusata shi nan ya fara mata salon mugunta kala-kala. Katamma ta ji azaba iya abaza ba shiri ta ce ya tsaya zata bashi nan ta karanto mishi da ka don haddacewa ta yi. Cow boy ya bukaci ta basa muhimman jawabi akan Nanda bata ɓoye masa komai ba hakan ya ji daɗi amma ya ce bazai sake ta ba yau a ɗauren ya barta don abun da kawo shi Kasar India kenan kuma ya samu.

...YA FI DARE DUHUWhere stories live. Discover now