✏📖
*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*RASHIDA ABDULLAHI KARDAM
(Rash Kardam)15
Jeddy ne ya fito da da sauri jin hayaniya da ihu acikin harabar gidan, yana fitowa ya ga uban gidansa ransa a ɓace ya nufi gun Kausar nan ya gane alamar yariyar ta ɓata masa rai ne tunda ga bulala a hanunsa kafin Abdulmajid ya isa gurin Kausar Jeddy ya isa yana haushi da gurnanini.Anti Safiya safiya ta zaro ido sabida sanin halin Jeddy kamar na uban gidansa ne sam baya da mutunci mugun karene kuma baya jin maganar kowa sai na Abdulmajid sabida ya koyarda shi abubuwa da dama bana wasa ba yasan in yana ɓacin rai yana ganewa ko Abba ne ke faɗa ma Abdulmajid in yayi masa laifi, Jeddy ya rinka haushi kenan kamar zai ciji Abban. Cikin faɗa ta fara yi ma Abdulmajid magana akan ya tsayar da Jeddy kar ya ciji Kausar ko ta ji ciwo amma ina bai ma san tana yi ba wai kunu a wani gida.
Kausar na jin ihun Kare sauran maganar ta maƙale mata a wuya bata ƙarasa ba ta miƙe, Kausar akwai tsoron Kare duk iya rashin kunyarta tana tsoron kare sosai bare ace kadangare wani irin zabura da ta yi ta miƙe ta fara gudu nan Jeddy ya rufa mata baya. Sosai suke gudu Abdulmajid ya na ganin Jeddy ya bi Kausar ya na kallo Jeddy ya ɗaga masa hannu alamar ya yi dai dai. Jeddy na ganin haka ya ƙara kaimi gun bin Kausar ga shi ta gaji tana tsoron ta tsaya wannan mumunan kare mai buzuzun gashi ya kamata yau kashinta ya bushe ai ta kaɗe har ganyenta.
Abduljalil abun ne ma ya samu matan falke ta haifi jaki, matar ɗan haya kuma ta haifi gida, mai nima bare kuma ya samu dariya yake ta yi ba kakkautawa har yana riƙe cikinsa shi abun ma kamar a dirama ya ke gani daga shan ruwan kashi da Abdulmajid ya yi har zuwa yanzu da Jeddy ya biyo Kausar.
Kausar na gudu cikin rashin sa'a ta je tsalake hanyar kwatarsu da ya fita har wajen gidan. Gashi ya taru sabida hanyar ruwar ta ɓaci duk wani ruwar dattin madafinsu da saurasu gun ya ke zuwa. Kausar bata ankara ba taji ta faɗa cikin guri.
Ma su gadi duk suna tsaye suna kallo ikon Allah suna tausaya ma Kausar ta taɓo Abdulmajid shi da bai bar ƙowa ba bare ita.
Isiya direba ya fi kowa murna wannan al'amari dariya ya ke yi ba kaɗan ba harda shafa inda aka maresa ɗa zu sai yanzu ya tuna wakar da akeyi ma Kausar a kauyensu, tabbas ta fitine su ne shiyasa lalle ya ga zahiri ko ya ce kaɗan ya gani daga ciki tunda ta jaza masa da yanzu ma ya jima a ƙiyama.
Anti Safiya da Abduljalil suka zare ido da gudu su kayi gurin, suna zuwa suka ga basa ganin Kausar da masu gadi suka nufo gurin da gudu don taimakon Kausar Baba Sale mai gadi cikin dabara da hokima aka zaro Kausar sai ɗoyi ta ke yi. Jeddy na gefe ya na haushi Kausar ana cirota ta buɗe idonta. Kausar lalle yau ta gamu da gamonta ko ince baga da gabanta Aljani ya taka wuta.
Mai Abduljalil zai yi in ban da dariya baka ganin komai sai kwayar idanun Kausar dariya ya ke kyakyawata har na hawaye ya rike ciki Anti Safiya abun ya bata dariya amma dadaurewa ta ke yi.
Jeddy ganin Kausar an fito da ita baiji zai kyaleta ba inba uban gidansa bane ya umarci ya bari ba zai kyaleta ba ya sake zuwa gunta a guje ta miƙe ta zura da gudu.
Cikin fushi Anti Safiya ta ce,
"Haba Abdulmajid baka da imani ne? Ai in ramawa kake son yi ka rama haka ya isa kalli ya da Jeddy ke binta karta ji ciwo mana, ka da katar dashi ko yau na faɗa ma Abbanka an fitar da Jeddy a gidannan."
Ko gizau Abdulmajid bai yi ba sai aikin zubar da miyau ya ke yi don ya kasa haɗiye yawunsa.
Fanjamm!
Karar faɗuwan Kausar cikin cikin ɗan ruwan da aka tara ana wanka da gun hutawa a gefen ruwan kuma lambu ne da sauran tsuntsayen da Abdumajid ke kiwonsu.
Da gudu Anti Safiya suka yi gun do wannan karo hannunta ke yawo a samam ruwa alamar ta soma shan ruwa tana nitse wa kasa tana tasowa. Abduljajil ne ya zo da gudu ya yi tsalle ya faɗa ciki ruwan don ceto ran Kausar.
YOU ARE READING
...YA FI DARE DUHU
General FictionLabarin ƙauna gamida cin amana da tausayi ga uwa uba soyayya.