✏📖
*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*RASHIDA ABDULLAHI KARDAM
(Rash Kardam)18
Shugaban jiji da kaine ya shigo gurin cin abinci duk kujerun zama kowa na kai sai guda ɗaya da yake kusa da Kausar ɗan karamin tsaki ya ja da niyar Juyawa Abba ya dakatar da shi ya sa ya koma ya zauna dolensa akusa da Kausar.Yana zama Kausar ta saki wani lallausar murmushi jin daɗi wani karamin daman da ta samu na rama abun da ya mata miƙa kafarta tayi ta lacce sa.
Da sauri Abdulmajid ya ɗago ya kalleta cike da mamakin rashin tsoronta gwalo ta masa. Wani takaicine da baƙin ciki ya takokari kirjinsa ganin Abba na gurin ya sa ba yi da ikon yi mata wani abu.
Maminsu da kanta haɗa ma Abdulmajid shayi ta ibar masa dan kalin da miya ta tura masa gabansa. Sai da ya ɗan ja aji kafin ya kurɓi shayin ya ji da zafi kuma ya masa daɗi sosai. A hankali ya ajiye kofin yana jira ya ɗan huce kafin ya sha.
Kausar na ganin haka ta juya ta kalli kowa ta ga ba wanda hankalinsa ya ke kanta wani ɗan karami kofi ta gani da farin abu aciki nan ta faki idonsu ta ɗauka ta juye ma Abdulmajid aciki ta na ci gaba da shan nata tana jira taga mai zai faru duk da bata san miye a kofin ba.
Abdulmajid na ɗaukan kofi yana sawa abakinsa ya ji gishiri kauu! Aciki. Ya ɗago da niyar ajiye suka haɗa ido da Abba ganin yanda Abdulmajid ke yamutsa fuska Abba ya ɗauka iskanci shine ya motsa. Tsawa Abba ya masa ya sashi ma za ya kurɓe shayin. Abdulmajid ya na runtse ido ya na sha. Kausar na ganin haka ta yi murshin migunta haƙanta ya cimma ruwa. Ƙafanta tasa ta lacce shi sai da suka haɗa ido ta masa gwalo wani takaicine ya turnuƙesa bai san lokacin da ya kurɓe shayin ba ya miƙe yana yamutsa fuska ya nufi ɗaki. Bayi yashiga ya wanke bakinsa amma har yanzu yana jin gishiri gishiri.
Abdulmajid duk ya ji duniya ta masa kunci ba kuma wanda ya tsana kaman Kausar gashi ta shigo masa rayuwansa alokacin da bai yi za to ba. Gashi ta sa Abba bai damuwa da shi ba haushinsa ma ya ke ji yanzu.
"Mtssw."
Ya ja tsaki ya sanya hannu a gashin kanahi ya cukurkuɗa ya jima yana wani na na zari komai ya tuna ya yi wani murmushin mugunta.
Abba ya ɗauki Kausar ku kaje makarantar su Nana ya biya kuɗi makaranta ya kuma roka abata aji uku kamar yanda Nana Khadija ta ke aji uku. Sun mata gwaji amma bata da wani ilimi da kyar Abba ya roƙa aka barta aji uku ya kuma musu alkawari za'ana mata karatu na musaman a gida tukunna suka yarda aka kai ta aji ukun.
Suna fita daga makarantar kasuwa ya wuce da ita ya sassaya mata kaya da su jaka da safan makaranta kafin suka dawo.
Wa Anti Safiya ya bata duk kayan Kausar daman ita ta ke kula da ita ya ce ran litini za'a koma za su fara zuwa.
Da yamma suna zaune a falo Anti Safiya da Abduljalil da Kausar sai Nana Khadija suna hira Abduljalal ya shigo da gudu yana kiran Mamansa da gudu yaje ya rungume Anti Safiya yana faɗa mata irin rashinsu da ya yi. Gefenta ya zauna kowa na ta ɗaukin zuwansa.
Kausar ta sake baki da hanci tana kallonsa ya mata kyau sukam dukansu yan gayune itama tana son ta dawo yar gaye kamarsu ta ƙara kallonsa a zuciyarta ta ce.
"Barin ga shima na da sauƙin kai ko za su karane da don ba zata taɓa kyale duk wanda ya mata ba."
Sai a lokacin Abduljalal ya lura da Kausar da irin kallon da ta ke masa. Gilashin da ke idonsa ya zare ya kalleta sama da ƙasa yaga wata kucaka da ita daga ganinta ka ga bagidajiyar Kauye.
"Ke lafiya ki ke min irin wanna kalo haka?.
Baki Kausar ta murguɗa masa ta kau da idonta.
Abduljalil ya kalla ya ce,
"Wannan fa da ga ina ta ke haka? Sai shegen kallo kamar ta ga talabijin."
Dariya Abduljalal ya yi ya bashi amsa da,
"Kausar sunanta."
Daga haka bai kuma ce masa komai ba ya yi shiru. Anti Safiya ta harareshi alamar bata son ta miƙe ta nufi ɗakinta...
Sannu a hankali kwanaki suke tafiya yau ta ke Litini. Duk duk wani ɗalubin da ke cikin garin Bauchi ya shirya don zuwa makaranta. A ɓan garen gidansu Abdulmajid haka su ma Abdulmajid da Abduljalal da Abduljalil sun shiryo cikin kayan makarantarsu na Sabil Sunlight baƙaramin kyau ya musu ba inka gansu gwanin burgewa. Direba ne ya ɗauke su ya tafi da su Nana kuma da Kausar da Abba zai sauƙe su a Prince and princes primary school. Kausar dakin Anti Safiya ta je ta ɗauko gilashin da taga Abduljalal ya saka a gefe taga abun makalawar muya na kwala riga shima ta ɗauka tare da kambas ɗin shi ta sa a jakarta ta ɓoye sai sun fita za ta saka sabida itama yau tana son ta dawo yar gaye ta na burge mutane. Nana Khadija ne ta zo ta rike mata hannu suka fita harabar gidan suka shiga motar Abba ya nufi makarantarsu.
*KAUSAR A MAKARANTA*
YOU ARE READING
...YA FI DARE DUHU
General FictionLabarin ƙauna gamida cin amana da tausayi ga uwa uba soyayya.