✏📖
*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*RASHIDA ABDULLAHI KARDAM
(Rash Kardam)Wannan shafin nakune
Maryam S Bello
Maryam Gital
Maryam S Idabawa
Pharty Zahra
Ummu Aisha
Feedo Sodangi
Faridat Sweery
Jamila Moh'd Ali28 to 30
Gudu suke yi sosai suka isa harabar gidan dum mutanen da ke suna ganin yanda miya ta ɓata fuskan Abdulmajid suka saka dariya. Hakan ba karamin kara samu guri ya yi a zuciyar Abdulmajid gurin tunzurasa. Gudu ya kara ya kamo.Kausar ya fara bata mari ganin da gaske jibgarta yake ta makalesa take wasu suka rimka yaba wa da irin kyan da sukayi a haka ya yi da wasu ke niman jin ba'asi.Maman Abdul da ke gefe ta ji hayaniya ta ɗago kai taga irin abun da ya garu da sauri ta nufo gunsu rai a ɓace tana zuwa suka rufu ma Kausar ihu ta ke kamar ranta zai fita. Abduljalil da gudi yazo yana kare dukan da Mamansa ta ke ma Kausar don jin kowa ni saukar dukan yake tamkar wuka a kasaka ana yaɗe masa naman jikimsa yana matukar jin Kausar a jinin jikinsa baya kaunar abun da zai taɓa masa ita don shi kaɗai yadan mai ya ke tana di a cikin zuciyarsa.
Abduljalal jikinsa har wani ɓari ya ke kamar mazari mai ta musu za suna dukanta. Sam ya tsani yaga ana musguna mata don ta samu wani sashe acikin zuciyarsa wanda iya ce zai tsaya fassara shi ɓata lokacine burinsa ya je ya yi karatu kawai Allah ya dawo da shi lafiya da daka mako mai kyau don zuciyarsa cike take wasu MAFARKAI wanɗa a kulum ya ke fatan su zama gaskiya. Abduljalal ya na zuwa naushi ya kaima Abdulmajid shima ya shiga dukansu ga Abduljalil shikuma yana tare ma Kausar dukan Mamansu yana bata hakuri. Abdulmajid cike da ɓacin ɗai ya kama Abduljalal da faɗa nan guri ya kaure kowa da kalar abunɗa suke faɗa ya yi da wanda basu san matsayi Kausar ba suke so suji ita ɗin wacece haka wani matsayi take dashi haka?.
Nana Aisha ganun faɗan ya zama babba hakan yasa ta fara kuka tana kwala ma Anti Safiya kira. Umaira kuma itama kukan take yi a gefe.
Yan liyafa madadin su raba sai suka ja gefe suna kallo wanda suka san matsayin Kausar kuma suna kara zuga Maman Abdul.
Jin ihu yas Anti Safiyya da kawayenta saukowa da hanzari ganin abunda ke faruwa tana zuwa ta shiga tsakanin su Abdulmajid ta ja Abduljalal gefe hannunta ta ɗaga ta ɗauke Abɗulajalal da wani mahaukacin mari cikin ɓacin rai ta ce,
"Mai kayi kenan ɗan uwanka zaka kama da faɗa?.
Sororo ya tsaya tamkar wanda bai da hankali ajikinsa tun da yake da Mamansa sai yau ta masa irin wannan mari amma ko kaɗan baiji zafinda ba tunda akan KAUSAR ne hakan ya faru. Jin tambayar da Anti Safiyya ta masa cike da ɓacin rai ya kalle ta ya ce,
"Mama kiyi hakuri akan Kausar ne bazan iya jura ba."
Sai a lokacin Anti Safiya ta tuna danita da hanzari taje ta taya kawayenta kwatan Kausar suka haura sama.
Maman Abdul takaici ya haɗu mata goma da ishirin da ɗanta Abduljalil da ta duka akan Kausar mai yarinyar nan take takama dashi.
Gida ya kacamr da hayaniya yayin da wasu suka soma watsewa wasu ko suka tsaya ganin kwaf. Shigowan Abba gidanne afujajan ya sa sallami mutanen cike da ɓacin rai haura sama Aisha ya kira da Safiyya da sauran yaran cikin fushi ya ke faɗa, tunda Kausar ta zo gidan bata taɓa ganin ɓaciɓ ran Abba irin na yau har ya kuma bata laifi sabida irin niman maganarta duk da basu san musabbabin abunda ya haɗa su ba.
Sai da ya gama faɗarsa cikin sanyin jiki ta russuna tana kuka tabashi hakuri, ta je gun Maman Abdulmajid ma taba hakuri haka Abdulnajid ma, sam yau taji bata kyauta ba ta zama sillar wargajewar fatin cikin mutanen da suka ajiye kyama suka ɗauke tamkar nasu sosai ta basu tausayi baran Anti Safiyya bakaramin mamaki tayi ba don tunda Kausar ta zo gidan duk rikicin da za'ayi bata taɓa bama kowa hakuri ba ko Abbane sai yau.
YOU ARE READING
...YA FI DARE DUHU
General FictionLabarin ƙauna gamida cin amana da tausayi ga uwa uba soyayya.