✏📖
*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*RASHIDA ABDULLAHI KARDAM
(Rash Kardam)46-47
Suhana wayar Kausar ce a hannunta ganin kirar Abduljalal ne ya sa da sauri ta tsaya ta nufi gurin Kausar da niyar kaimata wayar.Cow boy bin Suhana ya ke da kallo ganin ta sauƙa ta nufi inda mutane ke zaune a hankali ya ke kallon in da ya nufa ta ke gabansa ya wani irin faɗuwa wa zai gani a guri tabbas dole ya samu abun da ya ke so yau ɗinnan abun da ya jima ya na mafarkin samu don abun da ya kawosa kasar India kenan cikin sauri ya soma ta kawa...
Su Kausar waje suka fita don amsa kiran Abduljalal duk jikinta ya yi sanyi rawa ya ke ta ko ina, don tasan in Abduljalal ya ji tana Club ransa zai ɓaci bata ɗauka ba sai da suka bar cikin Club ɗin suka yi nisa gefen hanya suka gan gara da motarsu kafin kiran Abduljalal ya kuma shigowa.
Jiki na rawa ta ɗauka bayan sun gaisa ya ya ce,
"Albshirin ki."
Da sauri ta ce,
"Goro Yaya Abduljalal."
Murmushi ya ce,
"Gani a cikin garin India na sauka har na je otal na sauka wayarki na ke ta nima ya ki shiga na Suhana ma a kashe."
Cikin harshen turanci ya ke mata maganar jikinta ne taji yana ta bari cikin sarkewar murya ta ce,
" Dan Allah da gaske ne Ya Abduljalal?.
Murmushi ya yi,
"Kausar dole na in zo in ganki ina tsananin kewarki yau kusan shekara biyu da wani abu rabon da in saki a idona, ina kewarki ga ni na sauƙa a LAKSMI INTERNATIONAL HOTEL."
Jikin Kausar ko ina kaɗawa ya ke yi, Suhana da ke tana ji wayar a fili ta saka dukansu suna ji Suhana kan motar ta juya yan da zai kaisu Laksmi International Hotel.
Gudu ta ke shararawa Kausar kuma suna ta waya da Abduljalal da jikinta ya yi sanyi sosai wanda tasan in Anti Safiya ta ji ta je Club ranta zai ɓaci bazata ji daɗi ba. Allah ya taimake ta ma ba shigan banza ta ke yi ba kuma duk da zasu je gidan rawa ma hakan baisa tasa kayan da suka wuce kima ba.
Suna isa shima Abduljalal ya sauko tun da ga ne sa ya hango ta Kausar ta ƙara girma fatarta ta murje ta ƙara fari sau yanzu ya ke ƙara gode ma Allah zaɓin da ya yi yasan Inshaa Allah ba zai yi dana sani ba. Abbansa ne kawai ya ke tunanin yanda zai tun kare shi da maganar. A hankali ya ke ta kowa ya iso gabanta tun da ga ƙasa ya soma binta da wani mayen kallo ya na haɗiye miyau a hankali ya rinka takawa har ya iso gabanta daf da ita hasken cikin otal ɗin ya karaɗe ko ina wanda ko da kwayar allura ne ya faɗi za ka iya ganinsa ka ɗauka. Abduljalal idansunsa ya sanya acikin na Kausar wasu zafafan ƙaunarta ta ke hangowa a cikin idanunsa wanda bata taɓa ɗaukar ya na mata ita ba cikin zuciyarta ko ta kasa tantance tsakanin Abduljalil da Abduljalal waya fi sonta. Hucin nufa shinshi ta ji ya ƙara kusanto kusa da fuskanta cikin wata siririyar murya wanda shi kanshi bai taɓa ɗauka yana da irinta ba ya ƙara sunkuwa cikin raɗa-raɗa Abduljalal ya ce.
"Kausar ina matukar sonki kuma sonki na kara karuwa a cikin zuciyata na rasa ya zanyi da ƙaunarki, zuciyata tana bugawa ne da sonki da Kaunarki."
Wani iska mai cike da ni'ima da daɗi ya shaƙa don yanayin ya ma matuƙar masa daɗi ganin irin yanɗa Kausar ta dawo zuciyarsa cike ta ke da so da kauna yana jin in bai samu Kausar ba ya ya zai yi.
Kausar kama ji take wani baƙon yana yi na ziyartan ta tabbas lallai son Abduljalal ya ke mata mai girma a gareta. A yau kam ta hango ɗumbin ƙaunarta a cikin kwayar idanunsa wanda tana ji in har ta butulce ma sonsa bata san ya zai yi ba.
Sam sun manta da wata Suhana a gurin, Suhana kam ta jin-jina ƙaunar da Abduljalal ya ke yi ma Kausar gaskiya sun matuƙar burgeta irin salon soyayyar da
Abduljalal ke ma Kausar ido kawai ta zuba musu tana kallonsu cike da sha'awa da burgewa.Abduljalal ya yi ƙara-ƙasa da murya ya lumshe idonsa ya buɗe su ya sauke su cikin na Kausar kallonta ya ke batare da ya kyafta su ba a hankali ya kara furta kalmar.
"Kausar Ina Matukar sonki da ƙaunarki domin Allah, na zaɓi wa'yannan kamalaman ne su maye min gurbin sallama a gareki saboda hakan shine samun sanyin zuciyata da irin azabtuwa da sonki da kaunarki, kallon ki da nayi a yanzu ya sanya min sanyi da nutsuwa a cikin zuciyata ina jina cikin wani ni'imtaccen farin ciki wanda ba zan iya misalta miki girmansa ba."
Ya gama karanto iya kaunar da Kausar ta ke masa ko kwatan na sa bai kaiba hakan bai sa ya ji sanyi gwuiwa ba zai yi iya ƙoƙarinsa gurin tusa ma Kausar sonsa da kaunarsa a cikin zuciyarta ta yi kane-kane. A hankali ya kai gwuiwansa ƙasa ya ɗanyi rau-rau da ido tare da marairaicewa ya haɗa hannunsa giri guda alamar roko ciki rawar murya tamkar mai shirin yin kuka ya soma magana.
"Kausar ki taima ka ki soni ko da rabin wanda nake miki ne, Kausar sonki ya zama fitilar da ya ke haska min cikin zuciyata, ki taimaka min da sonki ko da ɗan gutsiri ne ina jin son ki na zagaya ko ina na jinin jikina Kau..."
Bai samu daman ƙarasawa ba Kausar ta biyo shi ƙasa itama ta saka gwuiwarta idanunta tab da hawaye cikin rawar murya ta ce,
"Ya Abduljalal dan Allah ka tashi da girmanka ka tsuguna min ina matuƙar jin kunyar hakan dan Allah ka tashi."
Ko alamar miƙewa bai yi ba murmushi ya yi mai ɗauke da ma'anoni daban-daban cikin salon so ya ce,
"Kausar shi So ba ruwansa da girma ko kuɗi, mulki, ko sarauta so yana shiga zuciyar mutum ne batare da ya yi maka sallama ko niman izini ba. Kausar ni kam ina kara gode ma Allah domin ya min babban kyauta da baiwa haka kema kyautar ɗaya ce, ya sanya min tsananin kaunarki a zuciyata, Kausar ƙauna ta kasance kyauta ce wanda Allah ya ke ma wanda ake ƙaunarsa ina gode ma Allah da ya min kyautar sonki da kaunarki a lokacin da banyi tsammanin hakan ba ki yarda dani ki furta min kalmar kina sona."
Jikin Kausar ya gama yin sanyi tabbas Abduljalal ya ci ta so shi ko don irin ƙaunar da Anti Safiyya ta nuna mata in har tana gun bazata ji daɗi ace ɗanta ya na niman abu haka a gurinta har ya dawo kamar almajiri, ya zata yi da zuciyarta da ta cika da son Abduljalil shi kuma bai taɓa nuna mata hakan ba bai kuma furta mata ba sai dai tana karantar hakan a cikin kwayar idanunsa.
Gyaran muryan da Suhana ta yi ne ya dawo dasu daga duniyar soyayyar da suka lula. Abduljalal ya kalli ida ta ke sai a lokacin ya tuna da ita. Bai miƙe ba cikin harshen turanci ya ke mata magana.
"Sis yi haƙuri mun shagala da yawa na ga sanyin idaniyata gaba ɗaya ta mantar dani komai sai kaunarta kaɗai nake iya tunawa."
Murmuahi Suhana ta yi ta ce,
"Naga alama don ka nutse a cikin tafkin so sosai."
Murmushi ya yi har sai da sautin ya fito fararen hakwaransa suka bayyana reras gwanin burgewa.
A hankali ya miƙe kafin suka gaisa da Suhana Kausar ma miƙewa ta yi jikinta a sanyaye kanta ƙasa wani kunya ta ke ji tana ganin tamkar Anti Safiyya tana gurin tilon ɗanta ɗaya tak ya yi haka.
Ganin dare ya soma yi suka buƙaci zasu koma gidansu nan ya ce lalle sai ya rakasu haka suka shiga mota Suhana ta buƙaci Kausar da su taje gidanta su kwana tunda ya fi ƙusa da shi za su fara samu Kausar taki da farko sai da Suhana ta ɗan ɓata rai kafin Abduljalal yasa baki Kausar ta yarda zata kwana a gidan nan suka sauka kafin ya tafi ma ya jima ji yake kaman in ya tafi shikenan Kausar ta masa nisa.
YOU ARE READING
...YA FI DARE DUHU
General FictionLabarin ƙauna gamida cin amana da tausayi ga uwa uba soyayya.