*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*RASHIDA ABDULLAHI KARDAM
(Rash Kardam)10
Abban Kausar ya na zuwa ya ɗaga dorina ya fara tsula mata ganin Inna Jummai da ta taimaka aka kamata tana ƙokari tashi hakan yasa ta ɗafemata in Malam ya kai bulala tare ya ke samun su Inna Jummai na ta cewa,"Ya haka Malam ni kake duka ai".
Ina sam baijinta sai da ya musu lilis ya sake Kausar. Da gudu tayi ɗakinsu cikin ƙasan gado mai rumfa tashi can kuryar gado ta maƙure sai kurma ihu ta keyi tamkar wacce aka yanke mata naman jikinta. Takaici ne ya kama Malam ya zo da hanzari don ya ƙara jibgarta amma ina kash! Ta ɓuya yanda ba zai iya shi ba, in har zai dake ta to sai ya shiga ƙarƙashin gado gashi manyan kaya ne a jikinsa haka ya haƙura ya koma. Kausar tana kuka da ƙarfi a hankali ta soma ragewa har bacci ya ɗauketa...
Umma na jinta zuciyarta na ƙuna duk irin tabiyar da ta bama Kausar amma ina sam Albasa batayi haƙin ruwa ba, Baƙin tukunya kenan mai haifar da farin tuwo sam halayansu ya banbanta dana Ummarta rashin jinta yayi yawa abun har tsoro ya ke bama Umma.
Wa shegari bayan su Umma sun idar da sallah asuba Umma ta kalli Kausar ta kira sunanta a hankali.
"Kausar."
Kausar ta amsa da,
"na'am Umma."
"Kausar yanzu abunda kika yi kin kyauta? Wani irin hali kike son tasowa da shi? Irin tarbiyar dana baki kenan? Kin san irin kunshi da fushi da kika sani jiya akanki aka cimin mutunci, yanzu kin kyauta da kikayi sanadiyar zubar da hawaye na? Za ki shiga cikin fushin Ubangiji mai tsanani, ki kiyaye bana son wannan halin kinji."
Kai Kausar ta ɗaga mata alamar eh!.
Umma ta umurceta da ta tashi suje tabawa Malam haƙuri da Inna Jummai.
Ɗakin Malam suka nufa Umma ta zauna gefe ta gaida Malam ba yabo ba fallasa ya amsa mata nan ta bashi haƙuri, Kausar ma ta bashi haƙuri nasiha ya mata sosai kafin ya sa Umma ta kira Inna Jummai za si yi magana. Ko da Umma ta je kiranta sai da ta gaggasa mata baƙar magana Umma bata jira taba ta koma ɗakin Malam.
Ko da Inna Jummai ta zo ba sallama bare gaisuwa ta nimi guri ta zauna sanin halinta ya sa Malam bai damu da hakan ba. Gyaran murya yayi ya soma cewa,
"Ba komai ya sa na na taraku ba anan sai don inƙara muku ƴan nasihohi ku zauna lafiya da junanku ke Jummai ina son kiyi haƙuri da abunda ya fatu jiya. Sannan yau Kausar za ta birni, jiya Malam Nasiru ya roƙi in bashi Kausar ya tafi da ita ya yaba da hankalinta zai sata a makaranta tayi karatu acan. Sabida rashin nutsuwar da ban samu ba shiyasa ban faɗa muku ba yau inshaa Allahu za'a zo a tafi da ita."
"Jakar ubanan wacece za'a tafi da ita birni? Ban san baƙin jininmu ya yi yawa har haka ba, don muna furci ga Abulle ace baza'a tafi da ita ba sai Kausar, wannan nufurcine da kisisina anje an gama asirceka acika gida da asiri to ahir munfi ƙarfin muna fuka kuma ba inda Kausar za taje sai dai su tafi dukansu kuma ai Abulle ce babba ba Kausar ba don haka Abulle ya kamata aje da ita don ta dandali arziƙi.
Wani kallo Malam ya mata kafi ya ce,
"Ba shawarar waninku nake nima ba Kausar dai ƴata ce nike da iko da ita ba wani ba kuma ita ya tambaya ba Abulle ba, don haka ku bani guri ke kuma ki harhaɗa mata kayanta kafin ɗan anjima."
Ya ƙarashe maganar ya na nuna Umman Kausar.
Inna Jummai na fitowa ta ta ce,
"Tirr! Abun ta ƙaƙare za'a tura ƴa karuwanci birni, tsohon banza ko mai zai samu a jikin wannan ƴar mininuwar yarinyar ƴar da ko ƙirgen dangi bata fara ba bare andai ji kunya uwa da uba sai son kuɗi da abun duniya, tunda za'a kai tallenta birni ko ince za'a kaita aikatau."
Maganar ta doki Umma sosai amma ta yi shiru kamar bata ji ba. Hannun Kausar ta kama suka koma cikin gida ɗaki tashiga ta tattaro sauran kayan Kausar masu datti ta fara wankesu.
Kausar ko najin abunda ya faru murna fall ya cika mata zuciya ba koma ta ke ƙaunar gani ba sai baƙon ranar wanda duka yita yawo dashi mai kirki dashi amma banda ɗayannan.
"Mtsssw"
Ta ɗanyi tsaki a zuciyarta ko wani haushin Abdulmajid ta ke ji da ta tuna abunda ya mata ranan.
A hankali ta lallaɓa ta fita gidan aminenta ko da ta isa kwanan gidansu salame ta hango suna ƙus ƙus da sauri ta isa gunsu, kunnenta suka kama suka faɗa mata wani magana shewa suka yi suka tafa. Cikin sanɗa suka soma tafiya katangar wani gida suka ɗale suna leƙe wata mata da ta ke wanka ganin matar da mama a ƙirjinta ya sanya Kausar ta kallesu tana dariya ta ce kai kuga wannan abu mai kama da lemu guda biyu nan wallahi suna min kyau tsaya ku gani. A hankali suka sauƙo ɗan kwalinta ta kunce ta ɗauki kwallon guruba guda biyu da suke ya she a gefe ta ɗage rigarta tamannasu tare da ɗankwalinta juyawa bayanta tayi Aishalle ta ƙulle mata, ta ke saman rigarta ya ɗago kamar wacce ta fara ƙirgen dangin da gaske. Suma sauran haka suka yi sai wani karairaya suke yi suna jin kansu kamar ƴan mata, sun ɗan ƙara gaba suka ƙara leƙa bayan gidan su Illu mai burodi cikin sa'a kuwa Saratu matarshi tana wanka sai leƙawa suke yi suna dariya.
Malam Ilu mai burodi ne ya fito daga bayan zanar gidansa ya gama gyarawa zai koma gida, yankowar da zai yi ya hangosu kai ya girgiza ya koma ya samo zabgegiyar icemsa mai kyau ya soma sanɗa a hankali a hankali.
Salame ne ta jiyo da niyar musu magana ta gansa a hankali ta sauko kafin ta juyo ta ce,
"Ku gudu."
Jin haka ya sa suka sauko kowa ya ware shima Malam Ilu ya rufa musu baya...
*'YAN UWA MUNA BARAN ADDU'ANKU, KU SANYA MAMANA A ADDU'ARKU BATA DA LAFIYA SOSAI KWANA BIYUNNAN. ALLAH YA BATA LAFIYA TARE DA ƘARFIN IMANI DA SAURAN MARASA LAFIYA AMIN.*
*FWA*
KAMU SEDANG MEMBACA
...YA FI DARE DUHU
Fiksi UmumLabarin ƙauna gamida cin amana da tausayi ga uwa uba soyayya.