BABI NA ARBA'IN DA UKU ZUWA ARBA'IN DA BIYAR

1.4K 80 4
                                    


✏📖
*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

   RASHIDA ABDULLAHI KARDAM
               (Rash Kardam)

Wannan shafin naku ne

Kamal Lawal Dambu
Muhammad Sanee Bauchi
Dr Sani A Jingino
Abdulyassar Aminu
King Boy
Dr Abdulwahab Musa Sari
Mubarak Idris Dakta
Prince AV
Zaidu Ibrahim Barmo
Abubakar Sulaiman

43-45
Lallae mamallakiyar wannan sura bata wasa bace, a hankali ta ke fitowa kafin ta fito gaba ɗaya. Kausar sake baki da hanci tayi tabbas yau kam ta ga irin kyawawan da ta ke ganinsu a film, duk da tun shigowarta ta gansu da yawa kuma akwai munanan da yawa sai dai abun da ta yi tunanin shine mafi kyawun sune suke shiga film don ba gaba ɗayansu bane kyawawan kuma farare akwai masu kamar bakake amma sai taga kaman bakaken mu na Najeria sun fisu kyau sosai a fuska su dai gashin ne kawai za su gwada mu su.

A hankali ta fito tare da kare ma gurin kallo fuskanta kwance ya ke da murmushi wanda ya kara kawata fuskan. Tafiya ta farayi tare da girgiza gashin kanta wanda ya kwanta a gadon bayanta. Ko ina na jikinta motsawa ya ke do min tana ɗaya da ga cikin jerin mata masu kyau da aji. Riga da siket ne ajikinta na kanan kaya wanda basu gama sauka kasa ba, kafarta sanye yake da wani takalmi mai kyau da tsini idanunta manne ya ke da bakin tabarau, bakinta ya ji janbaki kalar ja, taku take ɗaya bayan ɗaya cikin nutsuwa da isa Suhana kenan yariya ɗaya tilo Ministan mumbai wanda ya kasance babban mai kuɗi kuma ɗan kasuwa don yana ɗaya daga cikin masu kuɗin Indiya.

Kausar da ke gefe tana kallo Mr Mahamud Adam ne ya yafito ta da hannu akan ta zo, kafin Suhana ta iso gurin ta tashi. Ko da ta isa mota suka nufa suka shiga cikin gari layin waya  suka saya  sannan suka shiga cikin gari duk wasu abubuwanda za ta bukata ya sata sannan suka dawo otal din. Godiya ta masa sosai ya tafi ko da ta koma sallah ta yi ta ɗan kishin giɗa a kujera zuciyarta cike da kewar yan uwanta wayarta ta jawo tasaka layinta ta kirasu su Anti Safiyya suka gaisa da ita da su Nana da Umaira, d
sai Abbba ma ta kirashi suka gaisa ta sanar masa ta iso lafiya ya yi murna kafin ya kara mata nasiha sosai. Dakin taji ana kwan kwasawa tashi ta yi ta buɗe mai kawo abinci ne ya kawo mata bayan ya ajiye ta masa godiya. Mikewa ta yi ta watsa ruwa kafin ta dawo ta ci abinci ta ɗan kwanta cike da tunane tunane kala-kala...

Washe gari Mr Adams ya kawo tama key an sama mata haya a wani gida da ke kusa da makarantarsu nisan ba sosai ba amma sai tahau tazi kafin taje ta makarantar.

Ya kuma sanya mata duk wani abu da zata buƙata na kayan masarufi dai dai na ɗan makaranta ya kuma sai da mata gobe za su je su banki zai mayar mata da sauran kuɗin da Gwamnati ta bata na kashewa da hidimar karatu zuwa akawun ɗinta godiya ta masa sosai kafin ya mata sallama ya tafi..

A haka aka kammala mata komai ta koma gidan da aka kama mata haya wanda dukansu yan makarantane mata ɗaya ce ke gefensu da mijinta suna haya ɓan garensu daban. Ranar litinin ta fara zuwa makaranta komai tana fahimta anan ne ta ga asai suna tare da wannan kyakyawar yarinyar wanda taji ana ce mata Suhana Sa'ad Khan. Kausar karatunta take ba ruwanta da kowa cikin ikon Allah komai ya ke tafiya Kausar tana da kokari sosai wanda hakan yasa Malamai da dama suka santa. Akwai watarana da Malami ya yi tambaya aka sara wanda ya amsa sai Kausar tunda ga wannan lokacin Suhana taji ta burgeta tana so suyi alaka don ta lura zata karu da ita ta ɓan garen karatu. Hakan yasa Suhana ta fara zama kusa da Kausar in ana darasi da hakan ta fara niman tana mata karin bayani a game da Karatun da aka musu sai ɗan yawan kyautar da take ma Kausar sam taki karɓa ta kuma ki sakewa da ita don ita ta sa himma ma abun da ya kawota sam bata son ƙawance. Suhana fushi ta yi da Kausar da farko ta shareta bata kulata ana cikin hakan sai Baban Suhana ya zo bayan ya bincika tana karatu sosai a makaranta nan ta kirawo Kausar ta gwada masa ita amatsayin kawarta wacce suke karatu. Cikin harshen turanci suka gaisa nan ya musu nasiha ya kawo kyautar ban girma ya bama Kausar  ya kuma roki da in sun samu hutu ko a karshen mako akan su kawo musu ziyara ita da Suhana. Hakan da ya faru a tsakaninsu yasa Kausar ta fara sakewa da Suhana. Wani lokuta Suhana takan zo ɗakin Kausar suyi karatu wataran ma kwana take yi a gun Kausar ɗin. Suhana ta kasance mai son rawa da waka kuma tana yawan zuwa club da gun hutawa amma sai dai duk hakan bata yar da kanta kuma ta tsani abun da zai shiga tsakanin mace da ba muharramar sa ba, ta kuma tsani mace da take harkan banza wacce bata kama kanta da dama wasu sun ɗauka ita watsatsiya ce ta gama zubar da mutuncinta amma i a abun ba haka ya ke ba, ta so suna zuwa da Kausar amma fir ta ki. Yau ta kasance jumma'a bayan sun tashi a karatu sunyi sallah isha'i Suhana ta yi shirin zuwa Friday Club ta kalli Kausar ta ce suje tare  Kausar ta ki cikin lallami da daɗin kalamai sai da ta jawo hankalin Kausar akan ita kallo za ta yi ba ruwanta da rawa Kausar ta yarda ta shirya cikin wani riga da wando rigar ya sauka har gwuiwar kafarta sai wando mai tsukeken kafa, ta yafa ɗan ɗan karamin gyale akanta bakaramin kyau tayi ba baran ita fara ce sosai barai yanzu da ta kara samun gyara tana cin mai kyau tana shafa mayuka sai ta saje cikin farare. Motar Suhana suka shiga suka nufi Friday Club.

                  ***
Namijine ya kai cikakken na Namiji jikinsa manne ya ke da zanen kunamana da wasu rubuce rubuce kunnensa manne ya ke da ɗan kunne farine dogo kakkarfa dashi karan sigarine a hanunsa yana busawa wannan shine Cow  Boy cikaken ɗan safaran miyagun kwayoyi da sata duk da bai daɗe sosai da shiga harkarba baifi shekara huɗu acikinta ba amma ya iya aiki sosai yami'an tsaro sun san da zaman yan kungiyarsu amma shine har yau basu gane shi ba don ya iya basaja Cow Boy ɗan kasar Najeriya ne   ya haɗu da abokan banza ya faɗa  harkokin da basu da ce ba. Cow boy yana son zuwa kasar Indiya don yana samun mata da suka dace a gurin yana hutawarsa. Yau ta kasance jumma'a kuma ya tashi da shirin son zuwa Friday Club don a gun yasan zai samu wacce za ta ɗan rage masa zafi kafin ya bar kasar ko kuma na ranan.
              ***
Abduljalal kullum cikin tunanin Kausar ya ke son ta kuwa ba adadi a ransa hakan ya sa in har ya samu zama tunanin irin rayuwar da zasu yi ya ke yi. Ya tara makudan kuɗi wanda ya ke son turo su Najeriya a cire masa gida na gani na faɗa wanda ya san Kausar za ta yi farin ciki, hatta iyayenta yana da burin in ya dawo zai gina musu gida mai kyau su dawo ciki da zama su bar zaman kauye ya kuma buɗe ma babanta shago. Kamar kulum yau ya shiga kasuwa nan ya yi karo da wata sabuwar waya Nokia Sumbian mai layi ɗaya, guda biyu ya saya mata ita da Suhana yana yi madannan wayar kamar na kwamfiyuta hakan ya burgeshi kuma tana Whatsapp nan ma za su na yawan gaisawa da Kausar duk da ko yaushe yana cikin kiranta da sakonnia ya kuma tanada mata kanshi ya ki kula matan turawa masu jajayen kunne a na shi burin Kausar ce kaɗai ta cancanci ya mallaka mata kansa. Bayan ya dawo ya adana wayar a gurin sayyar da ya saba musu in yaga abu mai kyau, haka kurum yaji yana son ganin Kausar ya yi kewarta zai je Indiya ya mata hutun karshen mako daga gobe jumma'a zuwa ranar Litinin sai ya dawo. E fasfo ɗinshi da sauran visa shi yatattara nan ya je ya yi booking ɗin jirgi sai dai bai samu na zuwa indiya kai tsaye ba sai ya bi Dubai daga nan ya shiga kasar India. Abduljalal bacci sama sama ya yi don yana kewar ganin Kausar ya kira mamansa ya shai da mata zuwanshi kasar ta yi murna ta ce ya gaisheta. Wa she gari cikin ɗauki ya shirya ya nufi filin sauka da tashin jirage basu jima ba jirgin su ya ɗaga zuwa Dubai a can ma ya musu yan sayya kafin Jirginsu ya sake ɗagawa zuwa India.
                    ***
Suhana suna zuwa Friday Club suka zauna a baki suna ɗan hira Kausar duk a tsorace ta ke kasancewar bata taɓa shiga irin wannan guraren ba zuciyarta cike take da tsoro ga wani faɗuwar gaban da ta ke ji. A wajen shan lemu suka tsaya Suhana ta saka aka kawo nus mai sanyi suka soma sha suna ɗan hira sun jima a guri har sai da suka soma jin sautin kiɗa yana tashi kafin suka mike suka shiga gurin ya ƙawatu sosai Maza da Mata ne aguri wasu na rawa ya yi da wasu ke can gefe suna kallo wasu kuma shan lemu suke wasu masoya ne suna hira kowa dai da abun da ya ke yi. Kausar guri ta samu ta gaba gaba ta zauna tana kallo. Suhana ma zaman ta yi don in za ta shiga fili ba da kowa ta ke shiga ba sai da masu aji. Sun ɗan daɗe kamin aka sallami wa yanda suke rawar a ka kira Suhana. Cikin takun yanga da isa ta mike tare da ɗan kaɗa kanta gashin kan ya motsa ya kara kwanciya a gadon bayanta. Cikin salo mai ɗaukar hankali ta ke tafiya har ta haura saman gurin ta ke guri ya kauraye da ihu ana sowa ana mata kirari. Sai da guri ya ɗan lafa kafin wani kyakyawan matashi ya hau gurin ta ke aka sake musu kiɗa...

Cikin isa ya ke tafiya ko da ya iso kofar Friday Club zuciyarsa cike ta ke da fatan samun abun da ya ke so. Tun daga in da ya ke yaji ana kiran Suhana ana ihu  hakan ya sa Cow Boy ya faɗa cikin   da sauri dai dai lokacin da idonsa ya dauka akan wacce ta ke rawar..

Suhana wayar Kausar ce a hannunta ganin kirar Abduljalal ne ya sa da sauri ta tsaya ta nufi gurin Kausar da niyar kaimata.

Coy boy bin Suhana ya ke da kallo ganin ta sauƙa ta nufi inda mutane ke a hankali ya ke kallon in da ya nufa ta ke gabansa ya wani irin faɗuwa wa zai gani a guri tabbas dole ya samu abun da ya ke so yau ɗinnan abun da ya jima ya na mafarkin samu cikin sauri ya soma ta kawa...

...YA FI DARE DUHUWhere stories live. Discover now