✏📖
*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*RASHIDA ABDULLAHI KARDAM
(Rash Kardam)14
Ido Anti Safiya ta zaro."A ina kika ɗibi ruwan?.
Da ke bata gama fitowa da ga cikin bayin ba da hannu ta nuna mata kwamin kashi ido ta zaro tana tafa hannu.
"Kar dai ruwane Abdulmajid ya ke sha a falo."
Maganar kuwa bai sauƙa a ko ina ba sai a cikin kunnen Abdulmajid da ke ƙoƙarin shiga ɗakin Mamansa. Wani ihu ya saka da gudu ya yi ɗakinsa ya saka hannu a cikin bakinsa take ya soma kwara amai. Amai ya yi sosai har yaji bayajin ƙarfi a jikin shi buroshi da makilin ya ɗauka ya soma goge bakinsa ya yi ya ƙara sun na fida farin kumfa har ya fara haɗawa da jini. Ga zafin da ya ke ji amma shi yau kyan kyamin kansa ya ke yi. Yarinyar nan tagama cutarsa daga zuwanta ta sa ya sha ruwan bayi a bayinma na kashi Allah ya isa ya mata yafi a ƙirga.
Aunty Safiya ta zaro ido ta na kallon Kausar ta ce,
Wa ya ce miki wajen ne gurin ruwa yau kin ja ma kanki za ki sani a gun Abdulmajid ai."
Da sauri ta bi bayansa ɗakinsa ta ga baya ciki karan ruwa da buroshi ta ji a bayi da sauri ta buɗe ƙofar yanata wanke bakinsa sanin halinsa ya sa bata masa magana ta fito. Abduljalil ta gani a falo kallo ɗaya ya mata yaga damuwa a fuskanta.
"Anti Safiya mai ya faru?.
Cikin damuwa ta gaya mishi abunda ya faru dariya ya fara kyal ƙyala dariya yana faɗin.
"Kausar ba zaki kasheni ba."
Shi ba dariyar ruwanda Abdulmajid ya sha ya ke yi ba dariyar kwaɓan da Kausar tayi ya ke yi.
Zafin ba bakinsa ya ke masa sosai ya fito falo ya na ɗaga hannu sama ya na faɗin.
"Mai rabani da ke yau a gidannan sai Allah."
Cikin ɗaki ya koma ya kwaɓe dogon wandosa yasa gajeren wando iya gwuiwa da shimi na maza. Igiyar wuta mai ƙarfe a jiki ya ɗauko fuskan nan ta sa a turɓune tamkar bai taɓa karo da wani abu wai shi murmushi ba. Kwayar idanunsa sun kaɗa sunyi jajazur tamkar garwashin wuta kalo ɗaya za ka masa kaji baka kaunar ƙarawa sai dai ka ƙara don kyan fuskarsa.
Tafiya yanke yana rangaji a hanya tamkar namijin zaki fuskansa cike da kunci da bakin ciki wanda kalo ɗaya za ka masa bazaka iya tattace abubuwa da dama atattare da shi ba. Cikin falo ya nufo yana huci tamkar kububuwa da hanzari ya nufi ɗakin Anti Safiya Kausar ya tarar ta rakuɓe a gefe sai rarraba idanun take yi. Ta gama tsorota da yanayin da taga Abdulmajid kayan cikinta ne suka soma har gitsewa.
Ɗa kin ya tura ƙofar ya nufota gadan gadan ganin wata zanƙaleliliyar bulala yasa ta fara niman hanyar ɓuya. Cikin zafin nama ya kamato bulala ya ringa tsula mata tana ihu tana neman ce to.
Sosai ya ke dukarta tana jan jikinta harta isa ƙofar ɗakin ta buɗe da gudu ta fito falo bai barta, bayan kujera ta je ta ɓuya nan ma ya na dukanta.
Anti Safiya da gudu suka hauro da Abduljalil jin ihu da sauri suka nufo sa don kwace Kausar. Kalo ɗaya ya wurga ma Abduljalil sanin halinsa ya sa ya ja burki daga tsakiyar falo ya tsaya.
Anti Safiya tana masa magana bai saurarets ba Kausar da gudu ta sauko daga matakala duk wannan tsoron da ta ke ma hawa matakalan ta mance da shi ta na gudun ceto daga azaba. Duk iya iskancinta yau jikinta ya gaya mata yau ta gamu da gamota.
Da gudu Abdulmajid ya rufa mata baya suna sauƙa ganin za iya kamata ta soma zagaye gida yana binta da bulala. Duk iya gudun Abdulmajid ya raina kanda don yanda ya ga Kausar ke niman lailayasa ta fisa iya gudu amma hakan baiji zai kyaleta ba. Ganin ta gaji sai wani dabarar ya faɗo mata za tayi haukan da gan gan ko zai barta faɗuwa ta yi a ƙasa warwas ta na faɗin.
"Shikenan ta ƙare min ta ƙaremin na kaɗe na kaɗe har ganyena wayyo kauyenmu wayyo Salame da Aishalle wayyo Ummana wayo Malam ɗina."
Abdulmajid na ganin ta kwanta ya nufo ta da sauri.
Jeddy ne ya fito da ga bayan gidan da ɗan saurinsa jin hayaniya da ihu nan ya ga uban gidansa ransa a ɓace ya nufi gun Kausar nan ya ganr alamar yariyar ta ɓata masa rai ne tunda ga bulala a hanunsa kafin Abdumajid ya isa gurin Kausar Jeddy ya isa yana haushi da gurnanini.
YOU ARE READING
...YA FI DARE DUHU
General FictionLabarin ƙauna gamida cin amana da tausayi ga uwa uba soyayya.