✏📖
*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*RASHIDA ABDULLAHI KARDAM
(Rash Kardam)22
Kowa murna ya ke yi da tafiyar Kausar a kauyen Buzaye sabi da za su samu salama da fitinarta. Abban Kausar cike da jimamin rabuwa da yar sa ya koma gida tare da fatan na sara Allah kuma ya bata ilimi mai amfani.Umman Kausar ita ma ta yi kewar Kausar kulum cike take da tunanin tilon yarta ɗaya a birni. Ɓan gare ɗaya kuma in ta tuna mai ya kaita birni sai ta yi farin ciki ta mata fatan Allah ya shirya ta ya sa ta samu abun da ta ce nima.
Salame da Aishalle sun yi kewar kawarsu hakan ƴyasa suka ɗau alkawari duk ranar aikin Umma sukanje su mata aikin da suka san Kausar na mata. Wani lokacin in sun gama ayyukansu na gids sukan zo su tambayi Umma ko tana da aika sai su je mata. Hakan da suke yi bakaramin daɗi yake yi ma Umma ba. Hakan da suke mata ya kan rage mata yawan tunanin Kausar.
Inna Jummai kuwa ta tasa Umma da habaice habaice akan tafiyar Kausar zagi iri da kala da baƙaƙen magan ganu Umma tana shansu, toshe kunnuwan kawai take yi. Wataran sukan zagi Kausar da suce an kaita aikin bara da sayar da DARAJARTA. Ran Umman kan sosu baran in taji sun anbaci akai Kausar birni ne don sayar da DARAJARTA, ko sun manta da cewa DAJA DAYA CE in har ta rasata bata da wata sauran kima da mutunci a idon duk wani ɗa namiji. Ta dawo tamkar fankon ashana ne a cikin tsakiyar damina lokacin da itace ya zama ɗanye sharaf ga ruwa ga abun haɗa wuta babu, lokacin da kafi tsananin bukatar ashanan ya zama fanko. Ina hakan Inshaa Allah ba zai kasance da tilon ɗiyarta ba kausar ba.
A haka kwanaki suka tafi Umma cike da kewar ɗiyarta kulum zuciyarta na tuna mata da Kausar tare da mata fatan nasara. Abba ma hakane shima kullum cikin mata addu'a yake yi da fatan nasara.
Aishalle da Salame kuma duk da tafiyan Kausara basu bar niman tsokana suna taɓawa sai dai ba kaman lokacin da Kausar ta ke nan ba, don ita haka kurun ma takan ja su suje niman tsokana in ba su samu ba kuma sayi faɗa ko ba da su bane sukan saya ayita.
Abulle da Saude da Larai da Karame suma sun ɗauko saran rashin ji duk gidan da suka je in har matan tayi wawan ajiya to zata nimi kuɗi ta rasa. Hakan yasa ake yawan kawo karansu abun na damu Malam sosai amma bai isa ya nuna ma Inna Jummai za ta kama masa tijara da fitinan ita sam bata yarda ba sharri ake ma ɗiyarta don an tsane su.
Abulle kuma bata bar har ɗakin Umma ba ita ma bata tsira ba duk salon da za ta yi sai ta je ta ɗauke mata abunta kuɗi ko abinci.
Malam Nasir kuwa yakan yi aike ma Abba wani lokacin da kansa zai zo ya gaida Abban Kausar ya kai masa kayan abinci da ɗan kuɗi. Hakan ba karamin daɗi ya ke ma Abba ba duk da yafi bukatar ya sanya ƴarsa a kwayan idonsa. Sabida kawaici da karamci ya kasa magana. Sai fatan na sara da alkairi ya ke ma ɗiyarsa, don addu'ar tafi bukata a gunsa. Sannu a hankali rayuwa ke ta fiya komai ya na tafiya kamar yanda nufashinmu ke fita muna rage yawan kwanakinmu suna karewa suna matso da mu kusa da gidanmu na gaskiya gidanda ba filo bare gado gidan da ba iskar fanka bare talabijin din kallo. Haka komai ke shudewa tamkar ba'ayi ba sai labari.
✏📖
*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*RASHIDA ABDULLAHI KARDAM
(Rash Kardam)23
*BAYAN SHEKARA BIYU DA RABI*
Umman Kausar ne ke faman wanke kayan Malam tana shanyasu, Maman SAude ne ta shigo da sallamanta, ganin umma ne take aiki a tsakar gida ta saki wani tsaki ta galla mata harara. Umma sai da taji kirjinta ya ba da rass! cikin zuciyarta kuwa ce wa ta ke,
"Zakaran dawaki kukan ka bana alkairi ba, wannan matar ba alkairi bace don ina tsoron zuwanta cikin gidan nan ta zama fitina a gidan nan inta shigo fitina da zage zage ke biyo baya."
Tana da ga inda ta ke tana jin shewarsu nan suka fara sana'arsu suna zaginta da Kausar duk bata kulasu ba. Hakan ba ƙaramin kular da Inna Jummai ya yi ba kasa hakuri ta fito ta kalli Umma ta ce,
'Ke uwar kilaki wacce ta kakare aka kaita birni ma tsohon banza tsohon na jadu, ko da ya ke ba abun mamaki bane tunda ita uwarma a layi aka dauko ta, daga gidan wannan Malamin sai gidan wannan bokan."
Tunda Umma ta ke bata taba jin maganar da ya tunzurata har ta ji wani bakin ciki ya tokari zuciyarta ba irin na yau wai ita ke kira da karuwa ita da ɗiyarta cikin bacin rai Umma ta ce.
"Umm! Jummai kenan ai duk wanda kika ga ya ki tsotse hannu to bai ji za kin miya bane, kinga arashin samu miya mai tsaki ya sa ki fadin haka, kuma ki sani da mugun nufi ka dinki lifidi. Ni kam na fi karfinku wallahi ni da ɗiyata kam mun muku nisa duk mugun fatan ku Inshaa Allahu ba zai kama mu ba kausar kuwa sai kunci albarkacinta da yardan Allah. Jummai wanda Allah ya so ya ke kaishi inda mutum bai yi tsammani ba, kuma wanda Allah ya zuba wa garinsa nono to ba zai sha da tsamiya ba. Kausar ta je yin karatu za kuma ta samu abunda ta je nima da ikon Allah don hassada takice a sannu wataran zaki gane hakan."
Umma ta wuce ta ki ta fara share hawayenta don abun ya soma isanta har ya soma komawa kanta gashi yau su janyo ta tanka musu ta ke ta fara danasanin hakan sam bata son ta yi sa in sa da su.
Inna Jummai suman tsaye ta yi na wasu mintuna sam bata taba tsammanin cewa Amina ta iya magana haka ba. Maman Saude ta ce,
"umm lalle wannan matar ta soma samun kanta yau ita ta ke fada miki magana haka cab.'
Ta riqe haba tana jijjiga kai.
Inna Jummai ta ce,
ki barni da ita dole na dau mata ki akanta. Maman saude ta mike ta ce,
"barin je duk yan da kuka yi zanji."
Har ƙofar gida Inna Jummai ta rokota suka yi sallama ta tafi.
****
Abdulmajid yana zama akujera da sauri ya mike ya saki kara tare da saka hannayensa duka biyu ya rike mazauninsa ya na fafin.
"Auuuchh! Washh!."
Tare da runtse dukkanin idanunsa. Sosai ya ke mulmula gurin don wani irin azaban da ya ke ji. Don ba zato ba tsammani ya zauna allurar kuma ta shgesa sosai.
Jin karansa ya sa kowa na falon juyowa da sauri. Maminsa ne ta tambayesa.
"Abɗulmajid lafiya? Mai ya same ka agurin miye?."
Kausar na ganin haka ta fara dariyar mugunta ta ke wani fatin ciki ya mamaye mata zuciya tabbas dole ta kuntata mishi kafin tafiyarsa kasan waje ya yi.
Abdulmajid a hankali ya buɗe idonsa bai sauke sa ko ina ba sai akan Kausar da ta ke dariya kasa kasa, da sauri ya yunƙura zai nufi gunta.
"Washhhh!.
Ya sake faɗa tare da kara dafe gurin don wani irin azaban da ji kamar ta fi na da. Cikin kiɗima Maminsa ta karaso tana kara tambayarsa don duk ta gama ruɗewa.
*FWA*
YOU ARE READING
...YA FI DARE DUHU
General FictionLabarin ƙauna gamida cin amana da tausayi ga uwa uba soyayya.