FIKRA WRITERS ASSOCIATIONRASHIDA ABDULLAHI KARDAM
(Rash Kardam)2
Tana gamawa ko wanka bata yi ba ta ɗauko kayan Islamiyarta da ya sha datti tasa, tare da zura mutacciyar silifas ɗinta cikin ƙafarta. Sai da ta lelleƙa ta ga ba kowa a tsakar gidan. Ko ta kan jakar Islamiyyan bata bi ba ta rantama a guje ta bar gidan.Bata zarce ko ina ba sai inda ta saba laɓewa duk lokacin da zata je makaranta. A rayuwan Kausar sam ta tsani makaranta mafi yawanci in an turata Makaranta yawo ta ke wuce wa, sai ta gama gararambanta da wasa kafin ta dawo gida. Tana isa gun yara suka fara sowa sun ga abokiyar wasansu ta iso. Kakkasuwa suka yi kamar yanda suka saba in zasuyi tambo yar gida. Basu jima ba gurin raba kawunan su suka fara fafatawa.
Yau dai wannan wasa ba sa'a don an cinye 'yan gidansu, nan rinto fa ya kacame wanda har ya ƙusa dawo musu faɗa. Kiran sallah magriba ya dawo da Kausar daga rikicin da suke yi. Ga gari ya soma *duhu* da sauri ta ɗibi gudu tayi hanyar gida ko ta kan ƴan rinton tambo bata bi ba don tasan mai zai biyo baya muddin ta ce zata tsaya faɗa. Ko da ta isa Malam baya ƙofar gida sun shiga sallah. Da sanɗa ta shiga ɗakinsu tashiga ta ta samu Umma na sallah sai ta ni mi guri ta zauna.
Umma na idar da sallah tayi azkar ɗinta kafin ta kalli Kausar ta ce.
“Ba za ki yi sallah ba ne? A ina ki ka tsaya har magriba ya same ki a waje?".
Idon Kausar ya yi tsuru-tsuru don bata da amsar tambayar da Ummanta tayi mata.
Sai da Umma ta maimaita mata tambayar.
“Umm da man mun tsaya share makaranta ne sabida gobe in mun zo bitan karatu zamu fara ba sai munyi shara ba".
Umma ta kalleta ba wai ta gama gamsuwa da amsarta ba ne don tasan halin kayanta.
“To sallah fa ko shima kinyi?".
Kiri kiri Kausar ba kunya ta amsa da.
“Eh nayi a makaranta bayan da muka gama shara".
Da sauri Umma ta ɗago ta kalleta tana tafa hannu gami da girgi za kai alamar mamaki.
“Muga kafarki Kausar in har kinyi sallah zan gane".
Dasauri Kausar ta shiga ɓoye ƙafarta don ta san bata da gaskiya.
Umma ta soma niman inda ta ajiye bulalanta.
Da sauri Kausar ta miƙ'e ta nufi waje ta ɗauko buta ta saka ruwa a ciki ta fara alwala ta leƙe taga ko Umma bata ganinta. Ruwa ta sheƙa a kafarta da fuska ta miƙe da zuman shigowa ɗaki tayi sallah Umma ta zaro ido ci kin mamakin ta ke kallonta.
“Lalle yau na ƙara tabbatar da rashin jinki yanzu alwala ki ke wasa da ita? Kin ɗauka bana kallo ki ne?, Kausar ki ji tsoron Allah! Shin ko kin manta da irin bayanin azabar da Allah ya ke yi wa masu wasa da ibada? Ko kin manta sallah ita ce abuna farko da ranar Al-ƙiyyama za'a fara dubawa a cikin ayyukan bayi. In har sallah ka tayi kyau to sauran aikin ma za'a samu da kyau. Kausar ki mai da hankalinki ki nutsu bana son abun da ki ke yi. Maza ina kallonki ki sake alwala tun kafin in sassaɓa miki yanzun nan".
Kausar ta sake sa ruwa abuta ta fara alwala mai kyau Umma na tsaye a kanta.
Inna Jummai kishiyar Umma ce ta fito daga ɗaki tana harare-harare tare da yin tsaki ta yi shewa tana watso harara a guri da Umma ta ke tsaye.
Umma bata tanka mata ba ko ta san da wata halitta ma a gurin bare ta kalli inda ta ke ba.
Ran Inna Jummai ya kara ɓaci ta yi shewa tare da guɗa. “Ehehehe ayyiriri da ba a san asalin angulu ba ai sai muce daga Misra ta ke. Kuma komai ya ke cikin ɗan tsako shaho ya sani. To mai za'a nuna mana? Dan gulma a ce ke kin fi kowa Addini ko me mtsww!".
YOU ARE READING
...YA FI DARE DUHU
General FictionLabarin ƙauna gamida cin amana da tausayi ga uwa uba soyayya.