*ƊAN-ƊANO DAGA LITTAFIN ...YA FI DARE DUHU 2*
Na
Rash kardam
Cikin karaji da tsantsan tsana Aunty Aisha ta ce " ciki shege ki kayi!? Eeh lalle kam ga ribar karatun kasar waje wai ke ana kukuzaki ana yabonki mai ilimi ko? To ga ribar ƙasar wajenan ana miki kallon Saliha asai Magajiya ce. Kinje kin bude bariki fafa, daman rikon agola baiyi ba, ba kauye bai iya waye ba sai ya nuna halinsa a ko ina. Na kuma tausaya miki don ke ƙaramar alhaki ce a bariki ga rashin sa,a baki shiga da ƙafar dama ba. Maza ki tattara yanaki-yanaki kisan inda dare ya miki mu ba za mu raini ɗan maciji ya karmu ba. Ƴaƴanmu basu kawo shegu ba ke ƴar riƙo ba zamu goyaki da shege ba."
Alhaji Nasir ya kasa tabuka komai illa zuciyarsa da ke masa raɗaɗi wani irin baƙin ciki ya ke ji ga tarin kuci ya haɗu masa a ƙahon zuciyarsa ya kasa ɗaga ido ya kalli inda Kausar take. Abun ta masa yawa ga baƙincikin da Aure akanta take aikata zina "Inna lilahi wa inna ilaihi raji'un! Cikin shege harna wata huɗu da sati biyu da kwana shida, kenan ranar ɗaurin aurenta ta samu cikin ko a ƴan keanakin auren." Wani mugun tsanar Kausar ya ke huda duk wani ƙofofin gashin jikinsa take yaji baya kaunar sake kallon fuskarta. Miƙewa yayi ya haura sama yana jin gaba ɗaya duniyar ta saya masa cak!. Abun takaicinma iyayenta ya ke tunawa.
Kukan Kausar da ya cika ko ina tana rakuɓe a gefe ta haɗa kai da gwuiwa tana rera kuka mai ban tausayi.
Hankalin Kausar bai ƙara tashiba sai da taga Maman Abdulmajid ta nufota da akwatin kayanta ga hijab a hannunta. Tana zuwa ta jefa ma Kausar ta ce "Maza tashi ki kara gaba aje can kauye a haifa musu jikan turawa ba a gidanmu ba. Allah ya rufa asiri da baki tare ba da kin lanƙaya ma Abduljalal cikin shegenan da ke Allah ba azzalumin kowa bane kuma mu cikin zuri'ar Sarkin Fada Miri ba ɗan iska bare ɗan shege shiyasa Allah ya toni asirinki. Baƙar kaddara baƙar tsiya tirr! Da ke a zuri'armu."
Kausar iya rikicewa ta rike ta rasa mai ke mata daɗi tabbas wanda ya mata wannan illa baza ta taba yafe masa ba ya ɓata mata suna dana iyayenta ya jefa rayuwarta cikin garari da wani ido zata kalli Mahaifanta da cikin da ba'asan ubansa ba kuma ba a kan suna ba. Rarrafawa ta yi ta je ta riƙe kafar Maman Abdulmajid ta ce" Aunty dan Allah ki rufa min asiri kiyi haƙurk wallahi ba so na bane ni ba magajiya bane wallahi na kama kaina tsautsayine."
Buge hannunta Maman Abdulmajid ta yi ta saka shewa.
"Eeeh! Kam fa tsautsayi na ganshi ribar tsautsayin kenan to a ba anan ba, kiƙara gaɓa."
Ta faɗi tare da jayota tayi waje da ita ta ce.
"Matsiyaciya maras rabo kada na ƙara ganin ƙafarki anan gidan iko na gani kema kinsan sauran."
Ta ja ƙofar ta rufe, zama Kausar tayi dirshan! Tana kuka mai taɓa zuciya ita kuma kalar nata kaddarar kenan. Yanzu ina za ta nufa ƙauyensu Buzaye ko ta shiga uwa duniya, ina ma mutuwa zai ɗauketa a wannan lokacin...
Ɗan-ɗano daga Littafin *...YA FI DARE DUHU 2*Ina labarin Abdulmajid ne?.
Yaya Abduljalil da Abduljalal zasu ji in sun samu labarin cikin da ke jikin Kausar waya mata cikin?.
Yaya matsayin auren da ke kan Kausar da cikin da ke jikinta?.
Wani hukunci za'a yanke Kausar?.
Wai shin wanene Cow boy ɗinan?.
Dukan asoshinan ku biyo ƴar mutan Kardam littafi kashi na biyu.
Ga masu so ci gaba akan naira ₦300 kacal ku tun tuɓeni ta wannan number 08069420822 don samun ci gaban labari sannan ku samin sauran
YOU ARE READING
...YA FI DARE DUHU
General FictionLabarin ƙauna gamida cin amana da tausayi ga uwa uba soyayya.