BABI NA BAKWAI

1.8K 110 2
                                    


*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

   RASHIDA ABDULLAHI KARDAM
               (Rash Kardam)

7
Sannu a hankali su Kausar ke tafiya, Dije na gaban su, sun tasa keyarta tamkar wacce ta musu laifi. Da gan gan Kausar ta zo ta bangaje Dije, tana aika mata da harara. Cikin tsiwa ta ce“ ji yanda ki ke tafiya kamar wacce kwai ya fashe mata a ciki. Kamar kin manta da wasu na bayanki ko? Ko kin samu tsakar gidan ku ne?.

Dije shiru tayi da bakinta ba ta tamka musu ba, don in ta amsa tasan sauran. Cikin sanyi murya ta ce.

“Ku yi hakuri ba da gan gan nayi ba".

“Mtssw! haka za ki ce ai" cewar Salame tare da dangwarin kanta ta tura keyarta su ka ci gaba da tafiya, hirarsu irinta yaranta suke yi da haka su ka iso rafi.

Kayan Abulle suka fara karo dashi ta wanke su ta shanya, ga na Karime a gefe itama tayi shanyar. Kausar ta kunto laidar karara ta saka bakin ta ta hura iska take ya sauka akan kayan. Ta juyo tana kalon su Salame ta ce
“Mu duba inda suka saka kokon su, koma nawaye muka gani mu suba a ciki".

Gaba suka kara sai a lokacin suka hango su Abulle suna wanka ko wacce da ɗan fatari a jikinta duk sun jike da ruwa.

Ashalle ne ta lakato su Salame da Kausar ta nuna musu kwanon sha, da alamar na su Abulle ne. Cikin sanda Aishalle ta isa gun sai da tasan dabarar da tayi ta zuba zaka mi a ciki. Kafin ta dawo suka juya suka kalli Dije Kausar ta ce,

”Maza je ki ɗibo ruwanki ko ke ma ki samu naki rabon".

Cikin sauri jikin Dije har rawa yake yi ta nufi gun rafin ta sunkuya tasa Tulunta. Sai da ta tabbatar ya cika kafin ta ɗago jikinta a muce tana  addu'ah niman tsari da sharrin su Kausar, ba wai don sun fi karfinta ba sai dan ba abinda zata iya yi musu.

Ge fensu ta dawo ta tsaya tana jiran taji mai kuma za su sake ɓullo mata dashi.

Abulle da Saude ne su ka iso gurin da su Kausar su ke tsaye. Sai aika mu su sakon harara su ke yi masu Kausar tamkar idonsu zai ɓallo ya faɗi a kasa. Kausar ta rausayar da ido, cike da izza da tsananin tsana ta juya idonta tace.

“Nan gani nan bari ɗumamen mayya, mun tsole idon makiya ba dai su iya da mu ba, don mun musu nisa. Sai gani sai hange".

Ta kara she maganar tana juya idanu da murguɗa baki. Cikin salo da rashin tsoro tamkar  wata babba.

Salame ta chafe da “Hmmm! ai wutsiyar Rakumi tai ne sa da kasa, mun riga mun dawo Aholo ciwon ido".

Cikin fusata Abulle tayo kan Salame ta kai mata damka da niyar ta fara dukanta. Kukan Kura Kausar tayi ta ɗale wuyar Abulle tana yakushinta da mutsuni.
Dije kam tana gefe tana kallon ikon Allah.

Aishalle da gudu ta shiga faɗar. Saude ma ta shiga dambe suke yi sosai. Duk da kankantar su Kausar amma su Abulle basuyi nasara akan su ba. Sai raunin da suka ji musu ma.

Karime da Laure suna can bakin gaɓa, jin hayaniya yasa su fitowa karaf idonsu ya sauka ga kokawan da ake. Wata uwar ashar suka narka suka nufo a guje.

“Kai Kai Kai wannan wane irin abune haka? Kuna ta faɗa da junanku".

Cewar wani Bafulatanin da ya kawo Shanunsa shan ruwa, da hanzari ya isa ya raba su Kausar yana musu faɗa. Da kyar ya shiga tsakanin su Abulle sai ruwar ashar suke suna zagin su Kausar da Ummanta. Kausar alama tayi masu Salame su bar guri kama hanya suka yi kamar abun ya wuce.
Bafulatanin na tafiya Kausar ta dawo cikin sanɗa gun kayan su Karime da Laure ta je ta ƙara musu ƙarara akai ta juya tana rawar da kwakuisa tana dariya.  Ta lallaɓa zuwa gun kwanon shan kununsu ta juye musu sauɗan zakami aciki. Da hanzari ta bar gurin, sai a lokacin suka bama Dije izinin ta tafi tare da kashe mata gargaɗi akan karsuji maganar agun wani. Cikin tsoro jikinta na ɓari ta amsa da ba mai jima. Hanya suka nuna mata cikin sassarfa ta nufi cikin gari.
Kausar kuma bishiya suka ɗalle suna jiran ganin abunda zai faru.

Bayan tafiyar su Kausar Abulle suka za ge su tass! Kafin suka ɗiɓi ruwa suka yi wanka. Gindi bishiya suka dawo, kunshin kayansu da ke gefe suka warware tare da ciro yar battan mai. Suka shafe jikinsu, bayan sun shafa su ɗauko fodarsu buɗa jaka shuka shafa tare da kwaliya irinta kauyawa masu ji da gayu. Sai da suka gama komai Karime da Laure suka nufi gun saka kaya, yayinda Abulle tace.
“Ni fa yunwa nake ji don haka koko zan fara sha kafin na sanya kaya". Saude ma tace“ Nima koko zan fara sha". Saude ne ta ɗauko musu ta mika ma Abulle cikin zalama ta kafa kai, sai da ta kurɓa da yawa ta miko ma Saude.

Karime tana isa gun kaya ko kaɗewa ba tayi ba, ba Bissmilla bare addu'a saka kaya ta sanya a jikinta. Tsiirrrr!! Taji abu na mata a jiki ta ko ina sai ta ɗaure. Dai  dai lokacin Laure ta zura nata. Karime kuma sai mutsu mutsu take. Bayan shuɗewar da kika biyar Karime ta kasa jurewa ta saki kara.

Abulle da ta kai kwanon koko bakinta ta dakata sabida jin ihun su Karime ko da ta dago, hangon su tayi suna kwakwuisa hade da hawaye. Saude kam tun da ta kafa kanta a bakin kwanon koko sai da ta kusa rabi kafin ta dago. dai dai lokacin da Karime ta ruga da gudu tayi gun wasu busassun ciyayi ta fara tubukewa tana gurzawa ajikinta tsabar kaikayi. da sauri Abulle ta ajiye kwanon ta nufi gunsu tana tambayan su. "Lafiya mai ya faru naga kuna susan jikin ku kamar wasu masu kazuwa ko kirci ajiki?.

Ba wacce ta iya cewa kanzil acikinsu, illa susar da suke yi. ganin abun nasu bana kalau ba yasa ta tattara musu sauran kayansu suka nufi hanyar gida.


Su Kausar da ke sama suna kalon duk abunda ke faruwa. suna ganin su Abulle sun bar gurin suka sauko suna ta kyakyata dariya tamkar ma haukata. sai da suka yi mai isar su kafin suka bar gurin suka nufi gun Bishiyar mangwaro domin kadan wanda zasu sha.
            *****
Abulle sun yi tafiya sosai  Tsirrrr!! Taji wani abu ya zarga mata acikin kai take ta fara ganin raurari suna mata yawo sanu a hankali gurin ya fara juya mata. Take idonta ya riki de izuwa launin ja. Take fara tangaɗi tana raba hanyar. A gun Saude ita ma haka abun yake, sai layi take yi tana raba hanya kamar tababiya har tana gware da Abulle. Karime da Laure su kuma na su susa ne suna gantsarewa abun gwanin ban dariya ta wani fuskan kuma gwanin ban tausayi. Gaba kadan suka kara Saude ne ta fara zubewa a kasa a gun a hankali idon ta ke rufewa ruf bata kara buɗe su ba. Karime iya kiɗima ta kiɗima ga susa ga Saude ta zube ko suma tayi kome oho gashi ta rasa yanda zata yi taje gunta, don susa ba zai barta ba. Bata idda wannan tunanin ba Abulle ta zube a gun ita ma take hankalinta ya kara tashi sosai.

             *******
Su Kausar suna isa gun tsinkar Mangwaro su ka samu Yaran gidan Malam Jauro sun tsinke Mangwaro tari guda a gefe, da sauri suka yi kowacce ta jidi iya yanda su keso.

“Ke! ke!! Kausar miye haka?". 

Cewar Sagir kenan Da ga Malam Jauro.
Sai a lokacin ma ya hango sauran yan barandarta.
Yana da ga kan Bishiya ya ce.
“Ku mayar min da kayana tun kafin na sauko katsa za ku fuskanci matsala.
Wani guntun murmushi Kausar tayi tare da gatsa Mangwaron a bakinta.

“Ai da ka sauko ne sai mu fuskanta da kyau".

Cewar Kausar ta bashi amsar maganarsa.

“Tam shikenan lalle yau za ku gane kurenku za ku gane ku Yan iskan karya ne".

Sagir ya mayar ta da amsa.

Kausar ta kara dibar Mangwaro tana sawa a riganta. Cikin zafin nama Sagir ya zo dirkowa cikin rashin sa'a wata Reshe ta tokatesa take ya buga kansa. Ya fado kasa bakinsa na fitar da jini, gashi ya kwanta akan hannusa na hagu. Wata gigitacciyar kara ya saki yana niman agaji. Su Kausar suna ganin haka suka arceda gudu ,  ko tsayawa basa yi bare daman gwanaye ne a fagen gudu.

*FWA*

...YA FI DARE DUHUWhere stories live. Discover now