*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*RASHIDA ABDULLAHI KARDAM
(Rash Kardam)9
Bayan sun gama kowa ya miƙe ya nufi ɗaki domin watsa ruwa da shirin kwanciya. A ɓan garen Abdulmajid shima wankan ya yi, kayan baccinsa yasa ya kwanta rigin gine tare da lumshe idonsa ba abunda ya dawo kwanyarsa sai abun da faru ɗazu tsakaninsa da Kausar."Mtsssw."
Ya ja gutun tsaki tare da ɗaura ɗaya filon a saman kansa...
Washe gari bayan sun tashi kowa ya yi nufi wajen cin abinci amma banda Abdulmajid. Ganin Abdulmajid bai fito ba Abba da kansa ya leƙa ɗakin ya ganshi ya na bacci ƙofar ya jawo masa ya koma wajen cin abinci cike da kaunar juna wannan Iyalai suna matuƙar burgeni gurin ƙauna da haba haba da junarsu.
***
Su Kausat ba su tsaya ko ina ba sai da suka soma hango cikin kauyensu kafin suka nimi ƙasar wata bishiyar maina suka zauna suna haki. Bayan sun huta ne suka ciro mangwaron da suka tsinko ko wankewa basu yi ba suka fara sha. Sai da suka sha iya shansu tukunna suka miƙe suka nufi hanyar cikin kauyen buzaye. A hanya sai da suka k'ara sana'arsu wato niman tsokana tukunna suka shigo cikin kauyen gidansu Aishalle suka fara nufa. Suna leƙawa suka ga Ummanta tana bacci cikin sanɗa Aishallae ta ɗauko musu kwanon abincinta suka fara ci... Ko da suka gama haka suka nufi gidansu Salame daga nan suka nufi gidansu Kausar yankowarsu kwanan gidan Salame da Aishalle suka hango cin cirindon mutane ana kumfar baki daga alama karar Kausar aka kawo wa Malam.Jiyowar da Malam Muhammad zaiyi idon sa ya sauka kan Kausar da ta zazzaro idanunta alamar rashin gaskiya. Hannu ya mata alamar ta karaso, ta ke ƴan hanji cikinta suka muɗa tare bada sauki kululu! Duk ta rikece bata taɓa ɗauka za a kawo k'ararta yau ba tabbas kashin ta ya bushe Allah kaɗai zai kwaceta a hannun Abbanta. Tana isowa Malam Muhammad ya mik'a hannunsa ya rik'eta da kyau. Kalo ɗaya ta yi ma fuskar Malam ta ji wani tsoro ya ƙara shigarta. Cikin ɓacin rai ya kaima Kausar duka ta ke ta maƙale a jikinsa ta saki kuka ta soma haɗa shi da Allah tana kurma ihu tamkar an mata jina jina ne. Duka sosai Malam ya mata sai da wani abokin Malam ya riƙeshi yana bashi haƙuri. Malam Muhammad ya koma ya zauna tukun ya kalli iyayen yaro da kausar ta yi sanadiyar gurɗewa haƙuri ya ƙara basu kafin ya ciro dubu ɗaya kuɗin ɗauri ya ba su da lemun da za'a saya ma yaron yana sha. Iyayen Dije ma haƙuri ya basu ya juya yana kallon Kausar.
Wasu muta ne ne suka nufo gunsu ga Abulle da Saude cikin halin maye Karime da Laure Kuma suna kwakwuisa kamar waƴanda suka yi hauka suna gantsarewa.
Malam Muhammad yana ganin haka ya miƙe ya isa garesu cikin tashin hankali. Salame da Aishalle na ganin haka suka soma ja baya suna dana sanin abunda suka aikata don sun san yau Kausar ta gama kaɗeawa daga ita har ganyenta.
Cikin firgici Malam ya soma faɗin.
"SUBHANALLAH! Mai ya faru haka asha! Asha!! Maiya same su haka? Garin yaya?
Karime sai birgima take a ƙasa tana kwakwuisa tana hawaye. Laure kuma rigarta ta cire ta je jikin bango tana goga bayanta tana susa ta ko ina.
Abulle ta kalli Malam ta ce,
"Yau zan hau sama sama can."
tana maganar tana layi tana nuna sama.
Cikin tangaɗi irin na mashaya wanda suka bugu ta soma takowa zuwa tsakiyar abokan Malam kan ɗaya ta taka nan suka watse wai sune makalarta. Saude kam ɗankwalinta ta nan ta fra nuna su da yatsa tana layi ta na ce wa.
"Yau sai na ci.. mutunci.. ɓerayen nan, za ku sa sikari.. a ciki kunu.. brodi da shayi.. ku zo na..."
Tana maganar tana nufar mutane duk inda suka yi sai a watse a bar musu gurin.
Mutane da suka kawo su ne suka yi bayani wa Abban Kausar akan sun samesu ha hanyar rafi suna buge wannan kuma suna susa cikin ɗaurewar harshe wannan mai susar take ambatar sunan Kausar da Salame da Aishalle.
Kai Malam ya dafe yana jin wani ƙunar rai ya rasa Kausar wacce irin yarinya ce mara jin magana. Cikin zuciyar shi ko ya na tunanin alƙawarin da ya ɗauka gashi gobe ne anya zai iya cika wannan alƙawarin kuwa?.
Godiya ya musu nan ya saka a ka shigo dassu cikin gida. Ya juya da niyar ya damƙi Kausar kafin ya ankara tasa gudu,
"Kutare ta kutare ta."
Ya ke faɗa ma waƴanda suke gurin Kausar na ganin haka ta shiga ta kasan Malam Sule ta arce a guje ƙiris ya rage Malam sule ya faɗi kasa.
Da sauri suka shiga gida don taimaka ma su Abulle, Malam na zuwa kansu ya gane zaƙami suka sha Karime da Laure kuma ƙarara. Da sauri yasa aka kawo masa ruwan zam zam da madaran shanu wanda ba'a da fa shi ba, da manja take aka basu suka sha, Karime da Laure kuma zam zam aka basu suka sha, sannan aka haɗa zam zam da manja aka shafe misu jikinsu da shi.
Ba'a ɗau lokaciba su Abulle da Saude suka soma kwarara amai cikin ikon Allah bacci mai nauyi ya ɗebesu Karime kai kayin ya ɗan ragu da ikon Allah.
Malam ya miƙe ya shiga cikin gida don a gyara inda za'a kwantarsu kafi zuwa lokacin da za su farka. Tun daga soro na biyu ya soma jiyo hayaniya ya isa samu Inna Jummai da Maman Saude sun tasa Umma gaba sai zuba mata ruwan bala'i da zazaga mata masifa suke yi ita ko ba ta tanka ba sai niman tsari da sheɗan da ta ke yi acikin zuciyarta.
Malam ne ya musu tsawa nan take kowa ta nutsu. Umurni ya bama Maman Abulle akan ta gyara ɗakin su Abulle a kawo su....
Malam da kanshi ya samu iyayen yaran ya basu haƙuri sosai da ke iyaye Mazan masu sauƙin kaine Matanne fitinanu...
***
Kausar bata tsaya a ko ina ba sai da ta bar cikin kauyen ta hau kan bishiya Mangwaron da ke han hanyar shiga cikin Buzaye. Ƙafafunta ta saƙala su akan wasu manyan reshe ta tsisiki mangwaro ta ci gaba da sha tana hawaye yau ta jibgu ta san muddin inta koma gida yau sai dai wata ba ita ba. Da haka aka kira sallah la'asar ga fitsari ya matseta sai da ta leleƙa taga ba kowa ta sauko tayi fitsari tare da tintar duwarsu ta koma kan bishiya...Kausar na kan bishiya duk wanda ya zo wucewa sai ta saita kanshi ta wurge shi da dutsi ko mangwaro wasu kan ɗauka mangwaro ne ya faɗo in taga yanda suke yi ita kaɗai tayi ta dariya. A haka tana kallon abokan Abbanta ƙara lafewa ta yi a bishiya tana ji suna mayar da abunda ya faru...
Sai bayan sallah magriba ta sauƙo cikin sanɗa ta nufi gida, tun daga nesa ta hango Abbanta s ƙofar gida suna zaune.
Da rakuɓe rakuɓe harta iso ƙusa da gidansu ta gefen da su Abbanta suke ta yi kwanta rub da ciki yanda ba za su ganta ba. Ja da ciki ta ke yi a hankali tamkar wata macijiya, da ke gurin duhu ne a hankali ta wuce ba tare da sun ganta ba. Tana shiga soron gidanau ta miƙe bata damu ta kaɗe kayarta ba, cikin sanɗa ta shiga ta shiga cikin gidan Inna Jummai ta gani ta fito afujajan komawa ta yita rakuɓe ajikin garu sai da ta wuce ta shiga da gudu bayan rubunsu ta je ta ɓuya yanda za ta iya ganin duk mai shiga da fita...
Malam ta gani da Inna Jummai ta leƙo ya shigo gida da sauri bayanta ya bi suka nufi ɗakinta, sun ɗan jima Malam ya fito yana faɗin
"Alhamdulilah tunda sun farka ayi sa'a ma yini suka yi suna bacci suka farfaɗo."
Nan ta gane su Abulle ne suka farka sai ta ɗanji dama dama don taji tsoron ganin yanda ran Abbanta ya ɓaci. Abba ne ya sa akai musu ruwa suyi wanka Inna jummai ta zo ɗaukan bokitin wanka da ƴar tocilanta tana haska gefen rubu dall hasken to cinta ya sauƙa akan Kausar cikin ɗaga murya tamkar wacce ta ga wani abin tsoro ta taƙarkare ta kwala wa Malam kira.
"Malam! Malam!! ka zo gatanan gatanan jin haka ya sa Umma ta fito da saurin ance gatanan kalo ɗaya za ka yi ma idonta kasan taci kuka sosai.
Da sauri Malam ya nufi gun ya haska toci ya hango Kausar sai ra ba ido ta ke yi. Da sauri ya nufi gunta Inna jummai na ganin haka itama ta zagaya ta ɗaya gefen ta tare masa Kausar wai don karta gudu. Kausar ganin Abba ya nufo ta tana son tayi gudun tsira da yi gun Abbanta gwara ta je gun Inna Jummai tasan za ta iya tserewa. Itama da gudu ta nufi gun Inna Jumai ciki sa'a Inna Jummai ta damƙe ta ganin haka ta cukwuikuye ina jumma suka zube a ƙasa tare.
*'YAN UWA MUNA BARAN ADDU'ARKU KU SANYA MAMANA A ADDU'ARKU BATA DA LAFIYA SOSAI KWANA BIYUNNAN ALLAH YA BATA LAFIYA TARE DA ƘARFIN IMANI DA SAURAN MARASA LAFIYA AMIN.*
*FWA*
YOU ARE READING
...YA FI DARE DUHU
General FictionLabarin ƙauna gamida cin amana da tausayi ga uwa uba soyayya.