page 9

3.2K 268 0
                                    

'⋎´✫¸.•°*”˜˜”
..✫¸.•°*”˜˜”*°•.✫
☻/ღ˚•。*♥♥˚˚✰˚˛★*ღ˛°。*°♥。
/▌*˛˚˚.✰ •
/ ˚.★ *˛˚♥*✰。˚˚ღ。*˛˚♥。✰˚
        

                  ❣ *AKAWARI*❣
  _Bayan Rai_
     

~August 2017~

© *Hafsat Rano*

*Dedicated to* '''♡Anty Sis♡☆'''

☆☆☆☆☆♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡☆☆☆☆☆

           *9*

Ringing biyu ta d'auka.
Sae da suka fara maganar su ta k'awaye sannan Mummy tace "Alfarma nake nema k'awata"
"Haba Alfarma ai kin wuce haka wajena, fad'i kome ne ne na miki Alk'awari zan miki shi"
Sauk'e ajiyar zuciya Mummy tayi ta kwashe komi ta gaya mata kasan cewar tsakaninsu ba sirrin da suke boye ma juna
"Shine nake neman Alfarmar kawo miki ita gidan ki har Allah yasa taga dangin nata"
Ba musu Hajiya Atika ta yarda. A take suka tsara yadda komae zae tafi..

Mamaki ne ya kama Affan bayan ya gama jin duk abinda Mummy tace. Be tab'a tunanin Rashin kirkin Daddy ya kai this Far ba. Ga Nana ma kamar wata shaid'an yarinya sam bata ji, komi nata kamar yar daba haka take yi, ko da yake tarbiyar da Daddy ya d'ora ta akai kenan. Wani mugun Son Aman da tausayin ta ne ya k'ara kamashi..
A take ya d'au *Alk'awari* Ko *Bayan Ransa* Bazae tab'a bari wani abu ya sameta ba..


A Kitchen Affan ya tarar da Talatu tana jera abinci akan tray bayan ta gama jera masu nasu anan tsakiyar parlo shida Mummy, Al'adar Mummy ce bata cin abinci a dinning ko kuma da spoon, duk wani table manners yadda addini ya koyar shi take bi.
"Wannan abincin kuma fa?!"hajiya talatu ya fad'a yana jan tray d'in.
"Abincin bak'uwar Hajiya ne zan kai mata"
Dad'i ne ya kamashi, opportunity yazo da zaeyi magana da ita.
"Ba damuwa dama Mummy ta sa na kai mata wasu kayan bari kawae na tafi da abinci in yaso sae ki k'arasa aikin ki"

Talatu bata kawo kamae ba ganin cewa Affan d'an gaban goshin Mummy ne duk kuwa da warning d'in da Mummy tayi mata akan maganar Aman.

Dauka yayi ya fice zuciar sa fal farin ciki. A bud'e yaji koafar dama tana jiran zuwan talatu shisa ma bata rufe k'ofar ba.
Kamar daga sama taga mutum d'auke da tray, mik'ewa tayi zaune tana kallonsa har ya k'araso ya ajiye tray d'in..
Komawa yayi ya sa key a kofar sannan ya dawo ya samu saman sofa ya hakimce yana mata kallo ciki da tsantsar So..

☆☆☆☆☆
*Saudi Arabia*
Kwanan Ummi Uku a asibiti aka sallame ta bayan likita ya bawa Ya muhassin da Abby concrete Warning akan kula da lafiyar ta, kar ayi abunda zae b'ata mata rai. A ranar kuma Mummy Jalila da mijinta Alhaji Omar suka sauka k'asa mai tsarki don Amsa kiran Ummi na gaggawa..

Ganin Jalila yasa jikin Ya Muhassin ya d'anyi sanyi, Abby kuwa ko a jik'in sa, baya ma tuna wata Aman balle shirginta. Ya rabu da abun kunya ai shikenan. Anasa tunanin

Da gudu ta k'araso ta rungume Ummi tana kuka ganin yadda lokaci d'aya ta fad'a.

Bayan yan gaishe gaishe ne, Ummi tasa Aka had'a meeting na gaggawa aka sanar da dukka family d'insu. Hankalin Jalila sam baya jik'inta, burin ta d'aya taga Aman d'inta. Duk sanda sukayi waya baa tab'a bata suyi magana sae ayita bata excuse. Yau gata Allah ya kawo ta ita zata ga yarta farin cikinta. (ALLAH SARKI 'D'a da maihaifi kenan)..

Yan addu'oi akae kafin Ummi ta fara magaana.
"Inaso ku sani, a matsayi na, na mahaifiyar Muhassin, ina umartar sa dayayi gaggawar bin bayan Aman ya nemo ta duk inda ya kaita, in ba haka ba, na yafe masa ya nemi wata mahaifiyar bani ba"

Tashin hankali kowa ya shiga, wad'anda basu masan abunda ke faruwa ba kansu ya k'ulle.
Ummi ce ta bada labarin komae tun daga kan Haihuwar Jalila har zuwa Tafiar Aman.

Kuka sosae Jalila take, "wannan wacce irin k'iyayya ce?? "Abby kuwa shiru yayi kamar ruwa ya cinye sa, gani yake Ummi ta gama ci masa fuska ta tozarta shi. Abinda ya d'inga b'oyewa  tsawon shekera goma sha shida yau a cikin second biyar ta tona kowa yaji. Kallon ta kawae yake yana jin zuciyarsa na tafasa.

Muhassin kuwa yafi kowa shiga tashin hankali, duk nadamar abinda ya aikata yake.. Kuka harda shashek'a yana rik'e da k'afar Ummi karta tsine masa. Sam bata bashi fuska ba sae ma umartar d'aya daka cik'in yaranta tayi akan zata koma gdansa da zama..
Har a lokacin Abby beyi magana ba sae dayaji tana neman tafia, abun ya k'ara k'ular dashi. Sae a sannan ya mik'e a zafafe.
"Me kike takama dashi ne? Kina tunanin zaki wulak'anta ni a gaban kowa sannan in kyale ki?!wlhi baki isa ba, inason sanar miki in kin tafi karki dawo na sake ki"

Ihu gidan ya kaure, ko a jik'in Ummi don dama ta riga tayi making mind d'inta, tisa jalila tayi a gaba suka fice daka gidan in da suka bar Ya Muhassin Yana ta rizgar kuka yana dana sanin biye ma Abby...

Idea ce ta fad'o masa, yayi saurin jawo wayarsa ya shiga dialing number Farhan.

Farhan na xaune Office yaji kira, a yanga ce ya jawo wayar, number Ya Muhassin ya gani.
Daga wa yayi ya kara a kunnen sa da Sallama.
Ba wani b'ata lokaci Ya Muhassin ya shiga tambayar sa Akan Aman,  shi sam yama manta da wata Aman da shirgin ta. Kai tsaye yace shi rabon sa da ita tun a airport. Zaman yan bori Ya muhassin yayi wayar na kunnensa Amma ya kasa magana. Jin shiru yasa Farhan ya katse wayar ya cigaba da aikin sa cikin kwanciar hankali..

Gida ya wuce direct byan ya tashi don yana sa ran zuwa k'asar Malaysia nan da sati d'aya..
Direct part nasu ya wuce be lura sam da motar dake ajiye parking lot ba. Wanka yayi ya sauya kaya sannan ya fito don zuwa part d'in Mama. Yau ma kamar kullum maganar Bikin Farida kawae suke.. Tun a kofa yaji hayaniyar tayi yawa kawae sae ya fasa shiga ya wuce part d'in Hajja.

To his must suprise Fav Uncle d'insa zaune kasan carpet kusa da Hajja yana cin Tuwon Semo.

A sukwane ya k'arasa gaban sa, "Uncle saukar yaushe?"Ya fad'a yana washe baki.

"Ban jima ba My son daman so nake nae suprising naka, ya aiki ya kwana biyu?"
"Lafia lou Uncle wlhi munyi missing naka, hope Zaka jima kafin ka koma"
"Umm like 3 month haka"
"Wow Uncle M so much Happy Ina Small Mammy Nah? "Tana part d'inta."Ya bashi amsa
Da sauri ya wuce don zuwa ganin Mammy. Tabe bak'i Hajja tayi ganin ko ta kanta bebi ba
_(Fav Uncle d'in Farhan shine last born d'in hajja, matar sa d'ya da yaya biyu Abdouljalal takwaran Abban su Farhan sae Jalila. A Embassy d'in Nigeria Dake London yake aiki, part d'insa shima yana cikin Apartment d'in amma baya zuwa sae sau d'aya a shekara.)_

ALK'AWARI BAYAN RAI (Completed✅)Where stories live. Discover now