page 15

3K 232 2
                                    

'⋎'✫¸.•°*"˜˜"


..✫¸.•°*"˜˜"*°•.✫


☻/ღ˚•。*♥♥˚˚✰˚˛★*ღ˛°。*°♥。


/▌*˛˚˚.✰ •


/ ˚.★ *˛˚♥*✰。˚˚ღ。*˛˚♥。✰˚

❣ *ALK'AWARI*❣
_Bayan Rai_

~August 2017~

© *Hafsat Rano*

Edited by;
Miss xoxo👑

*Dedicated to* '''♡Anty Sis♡☆'''

☆☆☆☆☆♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡☆☆☆☆☆

*15*
*Saudi Arabia*

Har bakin Mota Ummy ta rako Jalila da mijinta Omar tana k'ara jaddada mata tayi hak'uri komae ya kusa zama normal, ba tada bakin magana sae jijjiga kai kawae da take, a haka suka shiga mota, daidai zasu fita ne Ya Muhassin ya shigo hankalin nan taashe, duk abinda yake yana tsoron fushin Ummi matuk'a, hannu Omar ya d'aga masa ita ko Jalila ko kallon sa batayi ba suka wuce. Saroro yayi ganin irin kallon da Ummy ta watsa masa, ko baka fad'a ba kasan ranta a b'ace yake da ganin sa. Shigewar ta tayi ta barsa nan a tsaye kamar mutum mutumi, sae daya tattaro dukka courage nasa sannan ya k'arasa zuwa cikin parlon. Kowa harkar gaban sa kawae yake ba wanda ma ya nuna ya lura da presence nasa, matar Jalil ce kawae tayi k'arfin halin Yi masa sannu da zuwa.
"Yawwa sannu."
Cikin d'ard'ar yana yak'e ya sami gefen kujera ya zauna.
Aikuwa be gama d'osana mazaunan sa ba kowa ya fara watse wa d'aya bayan d'aya. Takaici goma da ashirin. A ranar haka ya k'araci zaman sa ya kwashe yan matan k'afafuwan sa ya k'ara gaba yana tunanin abunyi.

Ko daya koma gida a zaune ya tarar da Abby kan wasu fararan kujeru hankali kwance yana latse latse a wayar sa.

Har ya wuce shi sae kuma wani tunanin ya dawo dashi baya.

"Sannu Abby." Ya fad'a yana jan kujerar dake gefen sa.
"Yawwa Sannu Muhassin"Ya fad'a yana sauke wayar daka fuskar shi.

"Alfarma ce nake nema Don Allah Abby, kayi hak'uri in na bata maka rai, Amma ya kamata duk wannan k'abilanci da nuna wariyar launin fata da muke mu daena shi tun da ba wai a Alk'ur ani ko hadisi yazo ba. Ummi ta fimu gaskia. Ka gafarce ni in na fad'i ba daidai ba"

Sakon talatin Abby ya d'auka yana kallon Muhassin, wato shima yabi bayan uwarsa kenan. Ba komae shidae yana nan akan bakansa, babu wanda ya isa ya sauya masa ra'ayi.

"Tashi ka bani wuri." Ya ambata yana kallon Muhassin.
Jiki a mace murus ya mik'e yana ayyana wa aransa Ko yaushe Abby zae Chanxa? Allahu A'alam

☆☆
Lokacin da Hajiya Batool ta sauka a Nigeria Direct gidan k'awarta Anty Maijidda Musa ta wuce don zuwa gidansu sae ta shirya. Tare ta tawo da Zubaida wadda kaf cikin Yanmatan kowa ta kama gabanta sae Ita kad'ai wadda sam bata san kowa nata ba sae Hajiya Batool.

Turus Anty Maijidda tayi ganin Wadda bata tab'a tunanin gani ba. D'aki ta kaitsu aka shiga hirar yaushe gamo bayan ta cika musu gabansu da kayan motsa baki.

Sosae Anty Maijidda ta tausayi mata halin da ta shiga sae dae tayi farin ciki da nadamar data yi. Anan ta shiga nuna mata illolin irin rayuwar, Kasancewar mace me kaifin baseera, a cikin ruwan sanyi Hajiya Batool ta fuskanci Duk abinda Anty Maijidda take son ta fahimtar da ita.
Koda mijin Anty Majidda ya dawo ta sanar dashi game da Hajiya Batool, Farin cikin sa ya nuna sosae sannan ya Umarce data gaya mata tayi gaggawar zuwa neman gafara wajen Iyayenta..

Satin su d'aya gidan Anty maijidda suka fara shirye shiryen tafiya Maiduguri wanda zaayi tafiya harda Anty Maijidda. Babbar Mota Mijin Anty Maijidda ya basu suka d'auki hanya sae Maiduguri.

Tafiya sukayi sosae
Kafin sukai garin su Hajiya Batool, Wani kauye ne cikin Bama, tun daka kan hanya ta fara sharar Kwalla ganin irin yadda k'auyen nasu ya koma, habawa shekaru nawa da barin garin ai dole taga ya sauya.

Sosae garin ya chanja mata wanda sae da tambaya sannan suka gane gidan nasu.

Gidane madaidaici wanda kallo d'aya zaka masa ka tabbatar da akwae talauci sosae cikin gidan.
Wani tsoho ne ya fito rik'e da buta yana kuskure bakinsa, ganin Mota taja ta tsaya k'ofar gidan nasa yasa shi tsayawa yana kallon ikon Allah. Da kyar da ban baki Hajiya Batool ta fito daka motar tana rakub'e wa..

Sakin Butar yayi wanda yayi sanadiyar jawo hankalin wani tsoho shima dake zaune a gefe yana shan iska.

"Ko shekara nawa zakiyi batula bazan tab'a mancewa da fuskarki ba. Allahu gafurur Rahim, Allah me amsa Addu'ar bayin sa. Yau Allah ya dawo Mana da Batula." Shine kawai abinda tsohon ke nanatawa

Ba b'ata lokaci gida ya cika mak', ko ina zance ya karad'e batula ta dawo. Sae da kowa ya natsa aka gama koke koke da ban hakuri sannan Anty Maijidda tayi musu Bayanin komae. Ba wani wahala iyayen suka yafe mata, dama chan su suka jefe ta cikin wannan halin, nasiha me ratsa zuciya Anty Maijidda tayi Akan Amanar 'yaya da Allah yake bamu..

Sae da komae ya lafa sannan Anty Maijidda ta juyo zuwa Kano cikin d'umbin Nasarori.

☆☆♡
Lokaci d'aya Affan ya gama shirin sa na tafiya Ekiti, Addu'a kam ya shata wajen Mummy, Wanda har a lokacin Nana bata dawo ba sae dae waya kawae.

Tafiyar sa Ekiti ta d'an rage masa tunanin Aman saboda kullum suna busy a camp, Anan ya had'u da wani aboki, Babban likita ne Akan bangaren Liver, A shekaru zae girmi Affan sae dae karamcin Affan yasa suka k'ulla a bota da shi.

Satinsa Uku A Ekiti cif cif ya juyo zuwa gida bayan sun yi exchanging Number da Dr. Victor.

Farin ciki Fal zuciyar Mummy ta tarbi d'anta, ya rame kad'an sae dae yayi wani irin fari, shafa sumar kansa Mummy tayi tana sa masa Albarka.

Da dadadare Suna zaune Da Mummy, Daddy ya shigo, zama yayi aka d'an tab'a hira dashi, Lokacin Nana ta kirashi, magana sukayi a k'arshe yace ta k'ara hutawa in ma ta dawo gidan takura mata zaayi.

Mummy na jinsa kawae nata ido, ta rasa dalilin da yasa yake ma Nana irin wannan son na hauka, Affan shine d'ansa Babba kuma namiji amma sam baya ma nuna damuwar sa akan sa kamar ita Nanan.

"Mummy, Daddy, Bari na kwanta, sae da safen ku"

"Ok Son Allah ya tashe mu lafiya, karka manta kayi Addu'a kafin ka kwanta."

"In sha Allah. "Ya bata Amsa.

D'aga masa hannun kawai Daddy yayi yana cigaba da answering Wayarsa.

Rano❣

ALK'AWARI BAYAN RAI (Completed✅)Where stories live. Discover now