page 35

2.8K 236 2
                                    

'⋎´✫¸.•°*”˜˜”
..✫¸.•°*”˜˜”*°•.✫
☻/ღ˚•。*♥♥˚˚✰˚˛★*ღ˛°。*°♥。
/▌*˛˚˚.✰ •
/ ˚.★ *˛˚♥*✰。˚˚ღ。*˛˚♥。✰˚
        

                  ❣ *ALK'AWARI*❣
  _Bayan Rai_
     

~August 2017~

© *Hafsat Rano*

Edited by; Miss xoxo👑

*Dedicated to* '''♡Anty Sis♡☆'''


☆☆☆☆☆♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡☆☆☆☆☆

           *35*

☆☆
Lokacin da suka gama a haduwa a falon Hajja, anan Fav. Uncle ya fara bayanin tun had'uwar sa da Jalila zuwa dawowar sa gida, sake had'uwarsu a malaysia da kuma had'uwar sa da Affan wanda bazae taba manta wa dashi a rayuwa ba, jin haka yasa Mummy da Affan farin ciki sosae jin ashe ma Aman tana tare da iyayenta. Hak'uri sosae Ummi ta basu, basu wani kulle ci abinba, aka shiga hira kamar an san juna. Ana cikin haka ne Aman da Farhan suka shigo..

☆☆
Dauke wa kwakwalwarta tayi na wuce gadi, tayi saroro tana kallon Fav. Uncle, hannun ta ya rik'o ya kaita har gaban Hajjan, wani irin Farin ciki ne lullube a fuskar Hajja,

"Na yarda Aman jinina ce Auta, shisa tun farkon gani na da ita naji ina sonta sosae, a lokacin ji nake kamar ni na haife ta, ashe dai soyayyar tana da dalili." Hajja ta fad'a tana murmushi. Sakin hannun ta yayi ta nufi wajen Ummi ta fad'a kanta, kuka ne na farin ciki, Allah kenan, duk yadda yaso sae ya tsara al"amuransa,

"Ummi ashe dama ni yar gata ce? ashe nima ina da dangi?"

"Sosae kuwa Aman, ke yar Gata ce ta gaske." Muryar Abba ta katse ta, sujjada tayi tana mai godia ga Allah cikin kaskantar da kai.
Daki aka ware ma su Ummi akan sae sun jira zuwan su Jalila sannan zasu koma Saudia.
Sallama Mummy da Affan sukayi musu ana kara godia da jaddada kulla zumunci me inganci tsakanin su..

☆☆
Tana kwance ta d'ora kanta akan cinyar Mammy tana jin wani sanyi a ranta, Fav. Uncle ne  suka shigo tare da Farhan suna tattauna wa, maganar duk akan Aman ce da Affan da yake jin sa har ransa, d'aurewa kawae Farhan yake amma baya son ana ambaton Affan ana kuma nuna yayi kokari akan Aman.

"A'ah, Mammy and her daughter," ya fad'a yana kallonsu cikin kulawa.
"Eh mana , kaima ga d'an ka nan gefen ka." Mammy ta amsa masa tana daria.
Mik'ewa tayi ta nufi wajen Fav. Uncle tayi hugging nasa, dama su d'abi'ar su ce, dafa kanta yayi yana murmushi tare da sa mata albarka. Daki ya wuce, Mammy ta bi bayansa ya rage daka ita sae Farhan.

"Allah,Allah kenan. Idan aka so wulakanta ka sae Allah ya duba ka, wani yana hura hanci gidansu gidansu, ashe muma muna da waje babba a gidan." Aman ta fad'a tana kallon tv.
Da sauri Farhan ya kalle ta don yasan da shi take,
"Dawa kike?" Ya fad'a cikin dakewa.
Banza tayi masa tana gyara zamanta sosae bayan tayi crossing kafarta.

"Dawa kike?" Ya kara maimaita wa, ganin ya nufo ta yasa ta kwasa da gudu tana kiran sunan Mammy. Daria ya saki yana shafa kansa.

"So childish, Ashe tana da baki dama?" Ya furta yana sake murmushi.
Daga murya yayi yanda zata jiyo shi,

"Zan kamaki kine, Silly girl." Ficewa yayi yana smilling shi kadai. Number Nana ya kira ya sanar mata yana hanya. Shiryawa tayi sosae ta fito suka sha hirarsu wadda rabi duk akan Aman ce., ganin irin damuwar da yayi akan Aman d'in shisa itama ta ringa sako mishi maganar ta. Da haka tayi prolonging hirar sam be san dare yayi ba.
Hak'uri ta kara bashi akan abinda tayi ma Aman sannan sukayi sallama ya tafi yana jin wani irin nishad'i, tun sanda ya fuskanci wacece Aman.

ALK'AWARI BAYAN RAI (Completed✅)Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon