page 38

2.8K 218 3
                                    

'⋎´✫¸.•°*”˜˜”
..✫¸.•°*”˜˜”*°•.✫
☻/ღ˚•。*♥♥˚˚✰˚˛★*ღ˛°。*°♥。
/▌*˛˚˚.✰ •
/ ˚.★ *˛˚♥*✰。˚˚ღ。*˛˚♥。✰˚
        

                  ❣ *ALK'AWARI*❣
  _Bayan Rai_
     

~August 2017~

© *Hafsat Rano*

Edited by; Miss Xoxo👑

*Dedicated to* '''♡Anty Sis♡☆'''

'''It is not necessary to argue over sumtin so insignificant, our journey together is so short''' Thanks for ur warm du"a. Lurv U all.

☆☆☆☆☆♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡☆☆☆☆☆

           *38*
Gaba d'aya suka mik'e a tare suka nufe shi da sauri, Na'eem ne yayi saurin rik'o shi jikin sa ganin yadda jiri ke shirin kaishi kasa, cikin tashin hankali yace;

"Lafia bruh! Me ya same ka?" Kin magana yayi sae juye kansa kawae yake da yake jin kamar zae rabe gida biyu, kokarin kwace jikin sa yake daka rik'on da yayi masa, Abba ya fito ya samesu, da sauri ya karaso wajn yana cewa;

"Subhanallah! Me yake faruwa?"
"Wlhi muma bamu sani ba, kawae muna maganar bikin Aman sae ya tashi da jiri." A cewar Fareeda dake tsaye Aman na bayanta. Dafa kafad'ar shi Abba yayi, dama yasan zaa rina, 
"Karku damu, wuce muje Farhan." Ya fad'a yana rik'o hannun sa. Jiki a sanyaye suka juya cikin falon,kowa da abinda yake sakawa a ransa.

Gefen kujera Abba ya zauna, ya d'auko ruwa me d'an sanyi ya siyaya masa a cup, kafa kansa yayi sosae yana sha, ajiyar zuciya ya sauke bayan ya dire cup d'in daga bakin sa. A hankali ya bude idonsa da ya rine zuwa jaa yana duban Abba,

"Mesa kayi nauyin baki Son? Kana son abu da befi karfin kaba, amma ka boye har yazo yafi karfin ka." Da sauri ya d'ago yana kallon Abba,
"Yes kana son Aman, Son.. Amma ka kasa gasgata kanka, har sae da wani yazo ya shiga, na dade da sani amma ganin baka ce komae ba, yasa na zuba maka ido, bazan bari wani personal interest d'ina yasa na takura wa Aman ba, karka manta mune yanzu gatan ta, wanda ta rasa a baya." Zugi sosae zuciyar Farhan keyi ya kasa cewa komae, gaba d'aya be taba jin irin wannan tashin hankalin ba tunda yazo duniya, lalle sae yau ya kara gasgata ransa akan cewa son Aman yake.

"Why? Why??" Ya shiga fad'a jijjiga kansa, cikin tausaya wa Abba ke kallon sa, da yana da yadda zaeyi daya dawo da hannun agogo baya, amma ina, bazae iya wannan son kan ba.

"U have to be strong Son, ka sani most of the time ba komae mutum yake nema ya samu ba, wani hanin ga Allah baiwa ne, watakila ba Alkhairi bane tsakaninku, kayi hak'uri."

"Yanzu Abba babu abinda zaa iyayi?" Ya tambaya yana sauke kansa.

"Babu gaskia for now, kowa yana farin ciki da wannan abun, don haka dole ne kaima ka d'auke damuwa ka cire komae a ranka, beside karka manta irin dunbun alherin Fav. Uncle d'inka gareka, be taba bari kayi maraicin uwa ba, mesa bazaka kokarin faranta ran yar da yake so yake jinta cikin ransa sosae ba? Karka zama butulu kaji Son."

"But Abba bazan iya ba, am very weak, zuciyata tana zafi, tana mun wani irin bugu Abba, pls help me." Ya had'e hannayen sa waje d'aya.

"Zaka iya Son, You have to, ko nace you most, kayi ta karanta *Innalillahi wa inna ilaihi raji'un*, shine kad'ai taimakon ka da zan iya." Shiru Farhan yayi yana jin wata k'walla me zafi tana saukowa kad'an kad'an a kunchin sa,

"Promise me dat Son, promise me dat bazaka taba bari kowa yasan damuwar ka ba." Cikin murya me ban tausayi yace;

"I promise Abba."
"Good." Abba ya fad'a yana mik'ewa.
"Am very proud of U Son, zan tayaka da addu'a." Yasa kai ya fice.

ALK'AWARI BAYAN RAI (Completed✅)Where stories live. Discover now