'⋎´✫¸.•°*”˜˜”
..✫¸.•°*”˜˜”*°•.✫
☻/ღ˚•。*♥♥˚˚✰˚˛★*ღ˛°。*°♥。
/▌*˛˚˚.✰ •
/ ˚.★ *˛˚♥*✰。˚˚ღ。*˛˚♥。✰˚
❣ *ALK'AWARI*❣
_Bayan Rai_
~August 2017~
© *Hafsat Rano*
Edited by; miss xoxo👑
*Dedicated to* '''♡Anty Sis♡☆'''
Am so sorry for the disappointment, na gama typing sub ena ya kare, afwan please👏🏻
☆☆☆☆☆♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡☆☆☆☆☆*29*
Karasowa yayi falon yana kallon Mummy,
"Me sami Daddy, Mummy?" Ya tambaya yana zama gefenta.Abun da ya faru ta fad'a mishi, shiru yayi ba tare da yace komae ba, mik'ewa yayi ya nufi d'akin Nana,
"Mesa kika fad'a ma Daddy maganganu haka Nana? Kinsan girman maihaifa kuwa?" Ya tambaye ta yana kallon yadda ta rik'e kanta.
Bata amsa ba, hakan ya bashi damar cigaba da magana,
"Duk abinda iyaye zasuyi ma mutum, still dai suna nan amatsayin iyayen sa, biyayyar nan in dai ba akan sabon Allah bane ta zama wajibi, dnt try it again kinji?"
"Am sorry." Ta furta a hankali.
"Dats my sis, yanzu ki kira shi ki bashi hak'uri,"
Ba musu ta jawo wayar ta tayi dialing number Daddy, hak'uri ta bashi, abinka da yar gwal sam be nuna yana san tayi wani abu ba, hira suka d'an taba sannan ta ajiye wayar.
Kallon ta kawae Affan yake, dole akwae abinda yake damun ta, gyra zama yayi ya tambaye ta cikin sigar wasa,
"Yawwa little sis, niko ina saurayinki nan me hancin karas?"
Daria ta sa tana kallon shi, sosae daria yake mata kyau ko dan bata saba ba,
Hany ce ta bud'e kofa ta shigo,
"Laaa Ya Affan ashe kana nan," ta fad'a tana karasowa ciki.
"Ina nan muna sirri da little sis, amma tunda kin dawo bari na wuce," ya fad'a yana mik'ewa.
"Laa pls ka d'an kara zama mana, inason nima ayi sirrin dani,"
Nodding kansa yayi yace;
"May be next time, sae anjiman ku." Be jira amsar su ba ya fice daka d'akin.
Juyo da kallonta tayi wajen Nana bayan fitar Affan,
"Sis Am in lurv with Ya Affan, tun ina karama ta nake jinsa so special, sae zuwan nan danayi, sannan nayi realising ashe son sa nake, amma naga shi sam his attentions wasnt with mie, kamar yadda ya d'auke ki haka ya d'auke ni." Tun da ta fara bayani Nana ta zuba mata ido, sae data kai karshe sannan ta sauke ajiyar zuciya tace,
"Lurv baya kyauta mana, mesa yake had'a mu da wad'anda basu sonmu, kinsan kuwa Ya Affan yana da wadda yake so?"
Gabanta ya fad'i tace
"Ban sani ba."
"Hmm toh bar kiji....." labarin abun da ya faru ta bata, cikin tsananin tashin hankali Hany take sauraron ta har ta kai karshe,"Am dead." Ta furta a hankali,
zamewa tayi a wajen ta zauna tana jujjuya kanta, most abunda yake faruwa a zamanin nan kenan,"Ina masu fatan Alkhairi, zan koma gefe naga yadda abubuwan zasu kasance, in Allah yayi shikenan."
Cikin tausayin kansu gaba d'aya Nana take kallan ta, su kuma haka abun nasu yazo, zata taya Hany Addu'ah Allah sa ya hak'ura da Aman sae ta shige mata gaba.
VOCÊ ESTÁ LENDO
ALK'AWARI BAYAN RAI (Completed✅)
Ficção GeralA story of a young girl who sees the bad side of the world from both angle.. Suddenly an angel came to her rescue.. Destiny will take it place.. Will he be able to rescue her? find out in this astonishing story