'⋎´✫¸.•°*”˜˜”
..✫¸.•°*”˜˜”*°•.✫
☻/ღ˚•。*♥♥˚˚✰˚˛★*ღ˛°。*°♥。
/▌*˛˚˚.✰ •
/ ˚.★ *˛˚♥*✰。˚˚ღ。*˛˚♥。✰˚
❣ *ALK'AWARI*❣
_Bayan Rai_
~August 2017~
© *Hafsat Rano*
Edited by; Miss Xoxo👑
*Dedicated to* '''♡Anty Sis♡☆'''
☆☆☆☆☆♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡☆☆☆☆☆
*44*
"Subhanallah ya furta da sauri yana kallon bedside clock da ya buga 6dot.. Mik'ewa yayi yana istigfari ganin ya makara ya fad'a toilet da sauri, alwala ya d'auro ya fito, Aman zaune kan gadon tana murza idonta, murmushi ya sakar mata me kyau ya nufi in da pray mat take ya tada ikama. Har ta fito yana tsaye yana karatu, hijabi ta saka da sauri ta bi bayansa suka yi sallah a tare, addu'oi masu shiga jiki ya ringa k'wararowa tana amsawa da Ameen.
Toilet ta fad'a shi kuma ya fice don zuwa d'akin sa, wanka yayi kawae ya jawo doguwar rigarsa ya sauka zuwa kitchen, tuna macroni d'in jia da chips yayi warming a microwave sannan ya dafa ruwan tea bayan yayi warming kaza ma ya fito dashi tsakiyar falon, table mat ya ciro ya shinfid'a kamar yadda Mummy ke musu ya jera breakfast d'in yana kare musu kallo yana smilling shi kadai. Jin takun tafiya yasa shi juyawa da sauri, Aman ce cikin lace purple d'inkin riga stonework da wrpper 6pieces tayi bala'en kyau. Saroro ya tsaya yana kallonta har ta karaso tsakiyar falon cikin girmamawa ta tsuguna har kasa tace;
"Sabahal khair Habeebty." Da sauri ya karaso ya d'agota yana kallon ta up and down, turo baki tayi ganin be amsa ba kamar zata yi kuka tace;
"Wannan kallon fa?" Yake yayi yana shafa kansa ya shiga gid'a kai kamar agama lizard;
"Sabahal Nurr Bby, u look awesome, kinyi kyau kamar wata bby moon, from now henceforth bari kiga irin gaisuwar danake so." Hugging nata yayi firmly yace;
"Goodmorning Swthrt." Then sae ki amsa da swtvoice d'inki da
"Morning Habeebty." Kunya ce ta kamata ta sunne kanta tana daria kasa kasa. Dariar shima yayi yaja ta zuwa gaban breakfast d'in. Zama sukayi tare yin bismillah sannan ya shiga feeding nata yana feeding kansa har suka gama, mik'ewa tayi zata tattare kayan yayi saurin dakatar da ita,
"U r a Princess Bby, i ll do anytin for u." Kwashe kayan yayi tatas tana binsa da kallo, zuwa yayi ya hure mata ido ya nufi bedroom d'insa. Sauya shigar sa yayi zuwa sabuwar shadda d'inkin threequarter ya fito yana bulbula kamshin turare. Gefenta ya samu ya zauna ganin ta zurfafa cikin tunani,
"Me kike tunani haka?" Ya tambaya yana riko hannun ta, yake tayi kawae tana sake sa hannun ta cikin nasa. Doorbell suka ji hakan yasa ya mik'e ya nufi kofar, Nana ce tsaye da Hanan sae warmers manya guda biyu a hannunsu, hanya ya basu suka shigo yana amsa gaisuwar su. A tsakiyar falon suka dire warmers d'in suka sami d'aya daka cikin set of kujerun dake falon me mazaunin mutum biyu suka zauna,
"Ina kwana auntynmu?" Nana ta furta tana murmushi. Da sakin fuska ta amsa sannan suka gaisa da Hany wadda take ta wani basarwa. Bayan kamar minti biyar suka mik'e sukayi musu sallama suka tafi.Daukar warmers din tayi ta nufi kitchen dasu, mamaki ne ya kamata ganin Affan tsaye jikin sink yana wanke wanke, da sauri ta karasa ta karfe plate d'in hannunsa tana masa kallon me zan gani, kafin tayi magana yayi saurin rigata ta hanya cewa;
"Ya ina duty na zaki zo ki karbe mun?" Hararar sa tayi cikin wasa ta matsa gaban sink d"in tana kokarin d'aukar sosan, hannayensa biyu ya had'a waje d'aya ya d'aga ta tsam sama yayi waje da ita, zillo take tana bubbuga masa chest akan ya sauketa yaki, sae daya dangana da kan kujerar sannan ya dire ta tare da jawo remote ya kunna tv, sunkuyo wa yayi daidai forehead d'inta ya pecking nata,
"This is where u belong, bari naje na karasa aikin ranki ya dade akwae hirar dana ke so muyi." Kasa magana tayi tana kallo ya shige kitchen d'in yasa key.☆☆
*Hospital*
Farhan zaune bayan sa jingine da pillow yana shan tea a hankali, yayi mugun rama ga uban suma daya tara, fuskar nan tayi fiyau, Fav.Uncle zaune gefensa yana amsa waya da wani Dr.Aryan, sae da ya gama sannan ya maida kallonsa ga Farhan wanda ya kafe shi da ido,
"Ya akae Son?, akwae inda ke maka cio ne?" Girgiza kai yayi alamar babu sannan ya soma magana a hankali murya kasa kasa;
"Is dat necessary Uncle?"
"What?" Ya tambaya yana kallonsa,
"Naga kana ta waya ne akan rashin lafia na, sae nake ganin kamar is of no use, na sami sauki Alhamdulillah, and na d'au lessons kala kala." Girgiza kai Fav.Uncle yayi
"Dat isnt enough, karka manta Dr Bilal yace problem d'in a wajen heart d'inka ne, and anytime komae zae iya faruwa, bazan iya barinka haka ba, we have to take proper treatment."
"Shikenan Uncle, am greatful."
"U dont have to. Mu d'an fita ka d'an zaga cikin hospital din, ana discharging namu zamu bar kasar ma gaba d'aya." Mik'ewa yayi a hankali suka fita daka cikin ward d'in suna d'an taba hira.☆☆
*Next day*
Sosae Affan yake nuna ma Aman so mara misaltuwa, jinta take on top of the world, mamakin yadda yake mata abubuwa kawae take, be damu da karbar hakkinsa ba sam, kamar ma be san yana existing ba, sosae ta saki jikinta dashi, soyayyar su suke sha like no tomorrow, su Rahmata sunzo sun wuni, daka nan suka tafi inda zasu koma washegari, abubuwa da yawa ta had'a musu su kaiwa Gaji, wasu sabbabin kaya kala biyu Affan ya d'auko ya basu su kaiwa Is'hu, kallonsa kawae Aman take, kashe mata ido d'aya yayi yana murmushi.Da daddare suna zaune kiran Mummy ya shigo wayarsa,
"Hello Mummy nah."
"A ah Affan banson yaudara, ka manta dani zaka wani yimun dadin baki." Daria kawae yake suka gaisa sannan ta tambaye shi ina Aman, mik'a mata wayar yayi suka gaisa da Mummy cikin jin kunya, karba yayi ta cigaba da yi mishi bayani akan Daddy yana son ganinsu gobe, amsawa yayi suka yi sallama.
"Gobe zamuje gida mu gaida Daddy." Ya fad'a yana karantar ta, mummunar faduwa gabanta yayi, wannan ranar take tsoro, kusa da ita ya dawo sosae daya lura da yanayin data shiga,
"Calm down wife, ba abunda zae faru." Shiru tayi tana tunani a ranta, sosae ya shiga kwantar mata da hankali har ya samu ta saki jikinta. Labarai masu dadi ya ringa bata tana daria har lokacin barci yayi suka je suka kwanta.☆☆
Cikin shigar shadda kala d'aya suka shirya, shi ya d'auko mata veil da takalmi ya yafa mata, ja da baya yayi yana kallonta, takowa yayi a hankali har gabanta ya d'aga fuskarta yana kallo,"Ke ta dabance, komae naki is unique, I lurv U."
"I lurv U too." ta furta kasa da murya. Hannun ta ya kama suka fita compound d'in gida, gaba ya bud'e mata ta shiga yaja suka nufi gidan Mummy.Tunda aka nufi gidan gabanta ke fad'uwa , yana lura da ita, lokacin da suka karaso gate d'in gidan fitsari ne kawae bata saka ba, hannun ta ya rike cikin nasa yana kallon kwayar idonta,
"U have to be strong Bby, nothing ll happen kinji?" Daga kanta tayi tana murmushi. Fitowa sukayi hannun sa cikin nata suka haura balcony. Mummy zaune cikin falo tana amsa waya, da sauri ta katse kiran tana musu sannu da zuwa, Aman kamar ta nutse don kunya, kamata Mummy tayi ta zaunar da ita gefenta. Mik'ewa tayi ta haura sama don sanar da Daddy, a tare suka sauko yana gaba tana take masa baya, zama yayi cikin kujerun wanda yasa Aman tayi saurin zamewa kasa tace;
"Ina kwana?" Da fara'a ya kai kallonsa inda take, lokaci d'aya annurin fuskar sa a d'auke ya mik'e tsaye, take lokacin data sauke masa hannayenta akan fuskar sa ya shiga yawo masa a a ido. Nuna ta yayi da hannu baki bud'e,"Kar kuce mun yar iskar yarinyar nan ce matar Affan, no it cant be." Ya fad'a da karfi, da sauri Affan ya mik'e, Mummy ma ta mik'e tsaye, duk basuyi tunanin abin zae zo haka ba, cikin karaji ya sake tambaya, Mummy ce tayi kokarin calming nasa, sam yaki tsayawa ma ya fuskanta, kofa kawae yake nuna mata,
"Fita mun daka gida. Get out!." Kuka kawae Aman take ta rasa ina zata sa kanta, hanyar waje tayi da sauri Affan ya bita,
"Karka kuskura ka bita Affan, na tsani yarinyar nan sosae, ina son ka sakar musu yarinya right now." Wani kallo Affan yayi wa Daddy yayi saurin ficewa yana kwala mata kira, Nana ce ta karaso falon fuskar ta fal hawaye.Rano❣
CZYTASZ
ALK'AWARI BAYAN RAI (Completed✅)
General FictionA story of a young girl who sees the bad side of the world from both angle.. Suddenly an angel came to her rescue.. Destiny will take it place.. Will he be able to rescue her? find out in this astonishing story