page 49

2.3K 191 7
                                    

'⋎´✫¸.•°*”˜˜”
..✫¸.•°*”˜˜”*°•.✫
☻/ღ˚•。*♥♥˚˚✰˚˛★*ღ˛°。*°♥。
/▌*˛˚˚.✰ •
/ ˚.★ *˛˚♥*✰。˚˚ღ。*˛˚♥。✰˚
        

                  ❣ *ALK'AWARI*❣
  _Bayan Rai_
     

~August 2017~

© *Hafsat Rano*

*Dedicated to* '''♡Anty Sis♡☆'''

_Follow mie on wattpad @HafsatRano, My facebook page @Rano Online Novels_

☆☆☆☆☆♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡☆☆☆☆☆

           *49*

Nana na katse kiran Affan, ta shiga neman layin Farhan, ringing uku ya d'aga a dakile,

"Hello Dear." Ta fad'a sounding not ok, jin muryarta da yanayin ta yasa yayi figuring out dat somtin is wrong,

"Me yake faruwa." Ya tambaya yana gyara zama, kasa boye masa damuwar ta tayi ta sanar masa abin da ake ciki, da sauri ya mik'e yana ambaton Aman ba tare da ya san me yake cewa ba

"U mean Aman tana ckin risk amma shine baki sanar mini ba, ki fito layn ku ki rakani gidan, i hav to take her kafin su mata illa." Kallon wayar take har ya dire tana mamaki, gaba daya ya manta a matsayin matar wani Aman take ya rud'e daka jin cewa tana cikin matsala.

Tana nan zaune tana tunani kiran Farhan ya shigo wanda sam basu fi minti biyar da gama wayar ba har ya karaso, mik'ewa tayi bayan ta amsa mishi ta sauko zuwa falo, ba kowa a falon sae karar tv da Daddy ya bari a kunne, kashe wa tayi sannan ta fita.
Kallon ta yake har ta karaso, ita da shi d'in duk abun tausayi ne, shiga tayi bayan ta gaishe shi. Amsawa yayi a gaggauce yaja motar bayan ta sanar dashi direction d'in.

☆☆
Zama tayi tana kallon apple d'in, sam bata da appetite amma yanda cikin ta yake juyi dole ta nemi wani abun..
Basmala tayi ta yanka apple d'in takai bakinta. Kamar paracetamol haka take tauna shi, har ta cinye apple d'in sae wani d'an karami data rage, leaning back tayi a little bit a kan couch d'in, a hankali ta fara jin kanta na wani mugun sarawa, dishi dishi ta fara gani, dafe kanta tayi ta shiga addu'a don yadda take ji kamar cikin ta yana boiling, amai ta shiga kwararo wa babu kakkautawa, wani irin kalan amai take tana rik'e da cikin ta tana kiran sunan Allah, kafin wani lokaci har numfashin ta ya fara sama sama..

☆☆
Gateman suka tarar rik'e da kankana yana sha yana yan wake waken sa, zama Farhan yayi a gefen kujerar mai gadin ita kuma Nana ta shige ciki, sae da yaga shigar ta sannan hankalin sa ya dawo jikin sa,
"What am i doing? Ya tambayi kansa yana mik'ewa.
"Aman tayi aure, she's married to sumone nt u, shi yake da ryt na kula da ita ba kai ba, u have to accept dat." Wani site na zuciyar sa ya kara tunasar dashi. A'uziyya yayi ya mik'e ya nufi karamar door en jikin gate en zae fita, ihun Nana ne ya dakatar dashi ya juyo har suna kokarin bangaje juna da gateman, a rud'e ta fito tana nuna musu kofar falon
"Aman!.. Aman!!.." kawae take nanata wa chest enta yana beating so heavy, wuce ta Farhan yayi da sauri without a second thought ya kutsa kai falon, wani irin super yayi ya isa gaban ta ya d'ago ta ganin babu numfashi a tare da ita sae wani white mucos da yake fitowa daka bakin ta, kallon ragowar Apple d'in yayi data bari yaga har ya fara wani kumfa ya kumbura, a take yaa gano poison ne a kasa ka,

"Haayat! Hayaaat!! Wake up, dan Allah ki tashi," ya shiga girgiza ta, ganin bata masan yanayi ba yasa shi saurin kinkimar ta ya fito Nana na biye dashi gate man yana tsaye shima totaly speechless ya bud'e mota ya saka ta, karbar key d'in Nana tayi taja motar.

Emergency suka wuce da ita direct, Nana na kuka shima Farhan yanayi, ji yake zae iya loosing life nashi, rik'e sa wani Nurse yayi ya tura shi Office d'in Dr Bilal ganin zaa yi biyu babu.

Taimakon gaggawa aka shiga bata using activated charcoal to stop the poison from being further absorb into the blood stream,bayan sun gano cin poison d'in tayi ba inhaling ba, Ventilator machine suka yi amfani saboda har lokacin babu numfashi a tare da ita.

☆☆
Tafia kad'an sukayi suka isa wani tangameman gida, shidae Affan kawae bin Barde yake da ido har aka bud'e makaken gate d'in gidan, sae da yayi parking sannan ya umarce shi da ya fito still yana pointing masa gun, ba musu ya fito yana karewa compound d'in gidan da ido,
"Wuce muje." Barde ya fad'e yana nuna masa hanya. Wani babban falo suka isa, tsaye Affan yayi nan ma yana d'an dube dube, fitowar Alhaji Na'aliya ce tasa ya maida hankalin sa wajen, har ya karaso in da yake,
"Wellcome Son." Ya furta yana kokarin hugging Affan d'in. Ja yayi da baya da sauri, wani shu'umin murmushi Na'aliya yayi ya sami waje ya zauna,

"Barde uban aiki, a russunar dashi mna." Gefen bindigar hannun sa Barde yasa ya bigi Affan a kafad'a, cikin azaba ya saki kara ya durk'ushe a wajen,

"Haba haba Son, dan wannan somin tabin? Gaskia ka badani." cikin jin zafi Affan ya d'ago yana kallon Na'aliya,

"Me kake so dani." Ya tambaya yana runtse idon,
"Ywwh Son gwra ayi komae da wuri, abun da nake so ba wani abu bane, evidence daka samu don tarnishing image namu nake bukata. As simple as dat." ya karashe yana d'age masa gira.

"Bani da wani evidence wajena." Ya amsa kai tsaye, daria sosae Na'aliya ya shiga yi ba tsaywa. Wayar sa ya jawo ya shiga video, mik'a ma Affan yayi yana cigaba da Daria,

"Videon ne tun daka kan lokacin da Sukayi injecting poison cikin apple, har lokacin da aka bawa yaron Barde , zuwa lokacin da ya bawa mai gadi,  da sauri Affan ya saki wayar
"Noooo Amaaaaan, dnt eat dat Apple!" Ya fad'a da karfi yana kokarin mik'ewa,

Sake kai masa wani dukan Barde yayi a d'ayan shoulder nasa

"We are not yet done Man, Aman ta riga taci Apple saboda munyi yadda bazata iya resistin nasa ba, jst hand over komae ni kuma na baka assurance zan kyale ka, and nothing ll happen to ur beloved wife."

Kuka Affan ya saka aa kama kafar Na'aliya,

"Don Allah dnt drag my wife in to this, nayi alk'awarin handing komae wajen ka, amma dan Allah kar ka saka matata a ciki." Wani shu'umin murmushi Na'aliya ya saki yana kallon Barde,

"Ashe dae yaron romeo ne Barde, baza mu wani sha wahala akan sa ba."

Da sauri Affan ya shga gid'a kai, yana sharbe hawaye, tunanin sa gaba d'aya yana wajen Aman.

"Shikenan Son karka damu, tunda bakayi taurin kai ba komae zae xo da sauki."  Daria daria, kuka kuka Affan yake kallon Na'aliya,

"Nagode sosae Alhaji, zan iya tafia ko? I want to see my wife."

"Ah haba Son, so soon kuma? Ai ziyarar bata kare ba." Kallon Barde yayi, yayi masa wani sign sannan ya mik'e ya fice.

☆☆
A hankali take jan jikin ta har ta kawo wajen wani glass daya fashe kolacin da Daddy ya bige shi da karfi, hannayenta tasa ta dunga gurzawa a jiki, jini sosae ya shiga zuba, bata fasa ba ganin igiyar na warware wa, har sae data samu igiyar na kunce gaba d'aya.

Manage👌🏼 I Lurv U All😍

Rano❣

ALK'AWARI BAYAN RAI (Completed✅)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora