page 31

2.9K 230 4
                                    

'⋎´✫¸.•°*”˜˜”
..✫¸.•°*”˜˜”*°•.✫
☻/ღ˚•。*♥♥˚˚✰˚˛★*ღ˛°。*°♥。
/▌*˛˚˚.✰ •
/ ˚.★ *˛˚♥*✰。˚˚ღ。*˛˚♥。✰˚
        

                  ❣ *ALK'AWARI*❣
  _Bayan Rai_
     

~August 2017~

© *Hafsat Rano*

Edited by; Miss xoxo👑

*Dedicated to* '''♡Anty Sis♡☆'''

_This page is for U Sweetest Dota *Billy S Fari* words cnt express how happy i'm to have u back, Ur kindness is beyond.. Allah ya bar zumunci_
☆☆☆☆☆♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡☆☆☆☆☆

           *31*

Kallon wayar yayi yana mamakin waye wannan da yake neman kawo masa cikas? Duk yadda yaso yayi tracing number abu yak'i,

Mik'a ma PA d'in sa wayar yayi ya fice daka wajen yana ayyana irin abunda zaeyi ma duk wanda yake masa irin wannan. Affan na zaune cikin mota daka chan baya yana kallo suka fito, daka gani hankalinsu sam ba akwance yake ba, danna send key yayi, already dama ya gama typing abinda zai turo;

*MUNA KUSA MUNA KALLON DUK WANI MOVES NAKU, DAKA GANI FUSKAR KA ALHAJI KANA CIKIN ZULUMIN WAYE ME MAKA WANNAN KO? BA KOMAI IN KUN SAUKA ZAMUYI MAGANA. ALLAH YA KIYAYE HANYA*
Waiwaye kawae Daddy keyi bayan ya gama karanta messges d'in, da sauri ya fad'a mota sauran suka mara masa baya. Gda ya wuce yana zancen zuci, ko takan Mummy dake masa sannu da zuwa be bi ba ya haura sama da sauri, number wani babban yaron sa ya shiga nema, sun dade basuyi magana ba dama amfanin irinsu in zabe ya kusa. Kiran layin nasa yayi sukayi magana me tsawo sannan ya ajiye wayar yana murmushin mugunta.

"Kabi komai a sannu Affan, kaga Daddyn ku fa idonsa ya rufe, kawae duk ma yadda zaeyi yaci zabe yake nema, ranar nan da daddare naji yana waya kasa kasa, magana suke akan kayan da sukayo order wanda bazasu zo ba sae bayan zabe, duk yadda akayi in har be zarce a zaben nan ba kayan zasu salwanta, daka nan kuma komae zae iya faruwa, ciki harda karyewar arzik'insa."

Jinjina kai Affan yayi yana me gamsuwa da bayanin Mummy, gwara ace irin su Daddy su d'and'ani rayuwa ko zasu zama masu godiya ga Allah.

"Bakomai Mummy, Allah yayi mana mganin koma mene, zanje Kibiya gobe, zan yi k'wana biyu haka daka nan shikenan sae nayi musu sallama. Akwae wani aiki danayi applying online, naji ance sun fara recruitmemt, zan ma Daddy maganar."

"Owk Allah ya taimaka."
"Ameen."

☆☆☆
Bayan sallah isha'i Mummy ta shiga d'akin Nana don tana son suyi magana, danne danne ta tarar da ita tanayi a wayar ta, ganin Mummyn yasa ta ajiye ta maida hankalin ta akanta.

"Kinsan me nake so kiyi mun Nana?"
"A'ah," ta furta tana kallon Mummyn.

"Kud'i zaki nema wajen Daddy, akwae Bussines da nakeson mu fara kinga rayuwa bata da tabbas, in ni nayi magana be zama lalle ya bani ba, kin dae san halin Daddyn naku."

"Owk tom shikenan, zan karba miki In sha Allah." Hira suka yi kad'an duk akan rashin zuwan Nana wajen Services nata, sannan ta tashi ta fice.

☆☆☆
Computer ce gaban sa yana ta faman aiki, duk ya gaji kasance war yawanci aikin Na'eem shi yake barwa, yayi nasa, yayi nasu Abba. Ringing d'in wayar sa ce ta katse mishi abinda yake,
"Fav Uncle! Ya furta da murmushi yana kara wayar, daka d'ayan bangaren ya kira sunansa,;

"My son kana lafia?"
"Lafiya klou Uncle." Ya bashi amsa cikin zumud'i.

"Guess what? Yanzu muke shirin baro birnin london zuwa nigeria." Wani ihu Farhan ya saki yana ture computer gabansa,

ALK'AWARI BAYAN RAI (Completed✅)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora