'⋎´✫¸.•°*”˜˜”
..✫¸.•°*”˜˜”*°•.✫
☻/ღ˚•。*♥♥˚˚✰˚˛★*ღ˛°。*°♥。
/▌*˛˚˚.✰ •
/ ˚.★ *˛˚♥*✰。˚˚ღ。*˛˚♥。✰˚
❣ *ALK'AWARI*❣
_Bayan Rai_
~August 2017~
© *Hafsat Rano*
Edited by; Mss xoxo👑*Dedicated to* '''♡Anty Sis♡☆'''
'''U guys made mie laugh sosae,Nasha daria sosae wlhi..😹 wasu na Affan wasu na Farhan. Thanks alot for ur warm comments, i feel beyond blessed to have u guys. One lurv'''😍
*Happiest birthday Faty Axland, wishing u many more fruitful years to come.*
☆☆☆☆☆♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡☆☆☆☆☆
*33*
Cikin dare Fav. UNCLE ya kasa barci, juyi kawae yake yana tunanin abinda Omar Mijin jalila yace masa, yana da 'ya babba tare da jalila, wani sanyi yaji yana ratsashi tare da son yar tasa da bai taba gani ba, mesa basu neme shi a lokacin ba, mesa zasu wulakanta masa 'ya haka? Haushi da tsanar Abby yaji ta kamashi, zae iya karfin sa ganin ya nemo inda yar sa take, zae bata duk wani gata data rasa..Da gari ya waye duk sukuku yaje jin sa, sun shirya tsaf suna jiran fitowar Jalila da Omar wanda zasu kaisu Airport, ita kanta jalilan barcin da tayi kad'an ne jia don ba karamin karfin hali take ba tun daka lokacin data je gida taji abinda Abby yayi,.. Da kyar Omar yayi convincing nasu sukayi breakfast suka wuce UMT.
Kwanan su d'aya da rabi a hanya suka sauka a nijeria, tun kafin suk'araso Farhan na zaune wajen jira. Mammy na gama rik'e da yayanta, Fav. UNCLE na bayansu jikin sa yayi sanyi sosae, da sauri Farhan ya nufe su, yana zuwa yayi hugging Fav. UNCLE, sannan ya dawo kan Mammy."Son kai ko Farhan?, sae daka fara xuwa wajn Babanka sannan ni." Mammy ta fad'a tana murmushi.
Murmushin sukayi gaba d'aya sannan suka nufi gida.
☆☆☆
"Wai kuwa Maman ku ta gama alkubus d'in?" Hajja ke tambayar Farida tana kokarin fita daka falon."Ban sani ba gaskia, kije da kanki ki gani."
Tsaki Hajja tayi ta karasa ficewa tana sababi. Taci atamfarta me kyau d'an auta zaexo. Sae data je ta tabbatar an gama alkubus d'in sannan ta fito ta sami waje a compound d'in tana jiran karasowar su. Shigowar motar yasa Hajja ta nufi motar da sauri, Farhan na ganinta yayo kanta da mota kamar zae taka ta, batayi wata wata ta kwasa da gudu tana jan kafa, wata irin dariya suka saka dukka banda Fav.Uncle wanda gaba d'aya hankalinsa baya wajen. Gefen d'akinta ta tsaya tana huci, gaba d'aya suka fito da sauran yan gidan don tarbar su.."Nayi kewarki da yawa Hajja tah." Fav. UNCLE ya fad'a yana hugging nata, gaishe gaishe akayi sannan suka shige ciki, kayan abinci kala kala aka shiga jera musu, shidae Fav. UNCLE kawae so yake ya kebe da Hajjan sa da Abba, damuwar ta masa yawa besan ya zae yi ba. Hidima sosae Hajja take dasu tak'i barinsu ma su huta, sam ta manta da rashin fitowar Aman.
Tun shigowar su cikin gidan Aman d'in kejin wani irin tashin hankali, gabanta fad'uwa kawae yake, haka yasa ta koma d'aki ta kwanta tana jin wani yanayi.. Fav. UNCLE be sami zama da Hajja ba, dole ya hak'ura sae gobe.
Da daddare Affan yaxo, magana sukayi akan zuwansa saudia, address ta bashi sannan sukayi sallama don ita ma gobe take son tafiya mad'achi.
Da safe Aman ta fito d'auke da yar karamar jaka, Hajja ran nan a bace, sae wani basar wa take.
"Hajja naga kamar baki son na tafi, kwana biyu kawae zanyi in sha Allah."
Uhum kawae Hajjan tace, sae data yi ta rarrashi sannan ta sauko tana mata Allah ya kiyaye. Na'eem na zaune a cikin mota yana jiranta, yasan rigimar Hajja ce ta rik'e ta shisa ma be damu ba.
YOU ARE READING
ALK'AWARI BAYAN RAI (Completed✅)
General FictionA story of a young girl who sees the bad side of the world from both angle.. Suddenly an angel came to her rescue.. Destiny will take it place.. Will he be able to rescue her? find out in this astonishing story