page 30

3K 223 2
                                    

'⋎´✫¸.•°*”˜˜”
..✫¸.•°*”˜˜”*°•.✫
☻/ღ˚•。*♥♥˚˚✰˚˛★*ღ˛°。*°♥。
/▌*˛˚˚.✰ •
/ ˚.★ *˛˚♥*✰。˚˚ღ。*˛˚♥。✰˚
        

                  ❣ *ALK'AWARI*❣
  _Bayan Rai_
     

~August 2017~

© *Hafsat Rano*

Edited by; Miss xoxo👑

*Dedicated to*
'''♡Anty Sis♡☆'''

☆☆☆☆☆♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡☆☆☆☆☆

           *30*

Gudu yake sosae kamar zae tashi sama, d'aukin ganin ta kawae yake, shi kadai sae maganganu yake. Da ya shigo cikin kano duk in da trafic ya tsaidashi ji yake kamar ya tashi sama, da haka ya karasa unguwar tasu, kallon jerin gidajen yake har yaxo kan nasu me lamba 142, samun kansa yayi da tsayawa yana karema gidan kallo, babban gida ne estate guda, kallon yanayin gate d'in yake, a hankali ya sauke ajiyar zuciya ya fito daka motar, gate d'in ya nufa yasa hannu ya k'wank'wasa, zafi yaji saboda girman gate d'in, key ya zaro ya shiga knocking yadda zaa ji. Ta wani d'an opening gate man d'in ya leko da kansa, cikin gurbatacciyar hausar sa yace;

"Wa kike nema?"
"Naxo ganin Alhaji ne." Ya amsa don besan wa zae ce ba.
"Alhaji wacce? Babba ko karami?" Ya kara watso mishi tambayar. Kafin ya amsa suka ji horn a bayansu, da sauri gateman d'in ya shiga bud'e gate.

Na'eem ne cikin motar ya dawo, tsayawa yayi bayan yasa kan motar tasa cikin gidan yana kallon gateman,

"Waye wanchan?" Ya fad'a yana nuna Affan dake tsaye, jin haka yasa Affan karasowa ya mik'a ma Na'eem hannu, da fara'ah suka gaisa yace yana son magana dashi,

"Ba damuwa shigo daka ciki." ya amsa mishi yaja motar shi.

Affan shiga yayi yana karema gidan kallo, sae da Na'eem yayi parking sannan ya fito ya nufi Affan dake tsaye,

"Bismillah." Yace ya nufin part d'in su. Bin bayansa Affan yayi har cikin falon nasu, wajen zama ya bashi ya bud'e fridge ya ciro ruwa ya ajiye masa akan wani karamin table dake tsakiyar falon.

"Thank U." Affan ya furta bayan ya zauna.

"Pleasure." Ya amsa yana fuskantar shi.

"Am nazo nan akan wani important abu, i dnt know how u ll take it, am here to see Aman, please kayi mun wannan taimako."
Jinjina kai Na'eem yayi yace;

"Amma bansan waye kai ba, and mene dalilin da yasa kake son ganin Aman ba, inason karin bayani."

"Ok." Affan yace ya shiga yi mishi bayani yadda zae gane,

"And if u r doubting ka kirata anan gaban ka, amma please karkai turning nawa down, i really wants to see her."
Shiru Affan yayi yana tunanin maganganun Affan, mik'ewa yayi ya fita bayan yayi excusing kansa. Part d'in Hajja ya nufa, a zaune ya samesu cikin bedroom d'in Hajjan suna mata tsifa,

"Ranki ya dade." Ya furta yana zama gefen Hajjan.
"Yawwa maigida, sannu da aiki ashe ka dawo?"

"Eh na dawo yanzu ba dade wa."
"Sannu da dawowa, Shi kuma wanchan ina ya tsaya?"
"Eh achan na barshi yana karasa wani cike cike, nasan nan bada jimawa ba zaki ganshi." Tabe baki tayi ta cigaba da jera carbinta a jikin zare. Ganin taki tsai da kan nata waje d'aya sa Farida tace;

"Ki tsaya waje d'aya Hajja." Banza tayi mata taci gaba da abin da take.
"Zan cika maki kanki wlhi, wannan ai wahala ne." Ta kuma maimaita wa a karo na biyu,
"Toh barshi mana, mtsw."

ALK'AWARI BAYAN RAI (Completed✅)Where stories live. Discover now