page 36

2.6K 212 1
                                    

'⋎'✫¸.•°*"˜˜"


..✫¸.•°*"˜˜"*°•.✫


☻/ღ˚•。*♥♥˚˚✰˚˛★*ღ˛°。*°♥。


/▌*˛˚˚.✰ •


/ ˚.★ *˛˚♥*✰。˚˚ღ。*˛˚♥。✰˚

❣ *ALK'AWARI*❣
_Bayan Rai_

~August 2017~

© *Hafsat Rano*

Edited by; Miss xoxo👑

*Dedicated to* '''♡Anty Sis♡☆'''

☆☆☆☆☆♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡☆☆☆☆☆

*36*

"Whats wrong with U son?" Fav.Uncle ya fad'a yana kallon Farhan dake ajiyar zuciya irin ta bacin rai.

"Babu komae." Ya amsa.
"Banson karya son, tell mie me faru? Mood d'in ka ya sanja haka gaba d'aya."
"Ba komae My uncle, jst dat i dnt get along with that guy,"
"Wa kenan, i dnt get U?"
"Affan yake kowa? Ni sam beyi mun ba." Baki bude F.Uncle ke kallon sa, abun mamaki,
"Haba Farhan, laifin me ya maka? Karfa ka manta alkhairin sa garemu, inason ka ajiye wani abu a ranka ka kyautata masa,he deserve koma mene from us." Shiru Farhan yayi yana jin wani kunci, Fav.uncle ma ya fara siding da Affan kenan,
"Banji kace komae ba son." Fav.uncle ya kara maimaita wa
"I ll try." Ya amsa yana bata fuska, juyawa yayi ya fice yana ayyana abubuwa da yawa game da yanayin Farhan d'in.

Kan sofa ya fad'a yana rik'e da kansa, tsaki ya shiga yi yana juye juye, Na'eem ne ya shigo ya tarar dashi a haka,

" Lafia dae bruh? Ya tambaya yana kare masa kallo. Banza yayi masa kamar ma bada shi yake magana ba, tabe baki yayi ya wuce ciki. Kamar an tsikare shi ya mik'e da sauri ya fice, part d'in Hajja ya nufa kai tsaye, ba kowa a falon sae Ummi dake waya da Jalila akan zuwan su gobe, har kasa ya durkusa ya gaisheta sannan ya nufi bedroom d'in Hajjan.
Kwance take ta d'aga kafa sama tayi ruf da ciki tana tunane tunane, tsayawa yayi akanta yana kallonta, jin kamar mutum a kanta yasa ta juyo, da sauri ta mik'e zaune tana gyara kafarta,.

"Sannu Ya Farhan." Ta fad'a tana kallon sa. Amsawa yayi kasa kasa yana dube dube a d'akin kamar me neman abu, Hajja ce ta fito daka toilet tana rik'e da k'ugu, da sauri Farhan ya mak'ale bayan labule

"Huh... Gaskiya na fafata, ji kike kuuuuu ciki ya kad'a, wannan banzar miyar ganyen da mama tayi ne nasan." A cewar Hajja tana kallon Aman, bata lura da Farhan dake labe yana murmushi ba, kunya ce ta kama Aman, ta d'an saci kallon Farhan dake makale yana kallonta shima, ido d'aya ya kashe mata yana taune lips d'insa na kasa, da sauri ta d'auke kanta. Ficewa Hajja tayi, hakan yasa Farhan ya fito yana kallonta,

"Ke baki iya fafatarwar bane? Ko baki ci miyar ganyen bane?" Ya fd'a yana karaso wa gaban gadon, kan drawer na gefen gado ya zauna yana kallonta. Banza tayi masa don tasan neman magana ne ya kawo shi, ganin ta d'auko waya yasa shi saurin karbe wa

"Wlhi baki isa ki kira firgitaccen saurayin nan naki ba, me kalar yunwa, ni banga abinda kika gani ba sam." Ya fad'a yana tabe baki, murmushi tayi me kyau tana kallonsa,

"Ashe kaima ya kamata ayi maka wannan tambayar, don nima banga abinso a Nana ba, don kamar su d'aya da Affan d'ina, kaga itama bata cancanci so daka wajen ka ba." Tamke fuska yayi yana wani kallon ta;

"Yarinya karki nemi zagar min Matata, kinsan tafi wannan me kafar langa langar" wani sabon murmushin tayi tana sauka daka gadon, sae data kai kofar toilet sannan ta fad'a da karfi,

"A haka na gani naji inaso." Da gudu ta shige ta saka key tana numfashi. shafa sumar kansa yana murmushi, ya mike ya fice yana takun kasaita.

"Auw ta ina ka shige ban ganka ba?" Hajja ta tambya tana mamaki, kasa yayi da kansa ba tare daya amsa ba ya fice da sauri.

☆☆☆
Cikin dare Affan ya kasa barci, juyi kawae yake, ganin kwanciyar bazata amfana mishi komae ba yasa shi mik'ewa ya d'auro Alwala. har aka kira Asubah yana tsaye yana kaiwa Allah kukan sa, sae da yaji ya sami nutsuwa sannan ya koma ya kwanta. Sae wajen 10 ya farka yana jin kansa yayi masa nauyi, wanka yayi ya sakko. A tsaye ya tarar da Daddy fuska ba walwala yana kokarin karba hula daka hannun Mummy, har kasa ya durk'usa ya gaida iyayen nasa, kallon sa Daddy yayi na d'an sakonni,
"Lafiyar ka kuwa?" Ya tambaya yana kallonsa sosae, banbarak'wai yaji maganar don sam be saba samun wani kulawa daka wajen Daddy ba,
"Ba komae, Daddy." Ya amsa yana murmushi, kad'a kansa yayi ya fice yana Allah ya sauwak'e. Sae da Mummy ta raka shi har balcony sannan ta dawo ciki.

☆☆
Dakin Nana ya shiga ya sameta gaban mirror tana kwalliya, hannun ta rik'e da waya tana selfie a snap, murmushi yayi yana garasawa gaban mirron.
"Ina kwana bruh?"
"Lafia lou Nana yar gayu, ta Farhan."
Dariya ta saki jin ya ambaci Farhan, kallon ta yae cike da tausaya wa,

"Wanne irin so kike ma Farhan?"
"Hmm." kawae tace tana gyara kayan make up d'in dake kan mirron.
"Ina son Farhan sosae ya Affan, bansa ya akae ba, kawae haka naji, i cnt bear losing him.

"Amma ya kike ganin relationship d'in naku? As in yana sonki kamar yadda kike sonsa?" Murmushi tayi irin wanda yafi kuka cio,
"Farhan baya mun half of son dana ke masa, i failed tun farko, and the worst part of it, Aman is his cousin sis, and i hurt her, i hurt him too sanda ya kusa loosing eyes nashi, all this crimes cant be forgttin ta sauk'i." Shiru Affan yayi yana kallon ta, lokaci d'aya tausayin su ya kara kamashi, yasan Aman tana sonshi amma yana tsoron kusancin su da Farhan. Calming nata yayi akan ta cigaba da Addu'a.

☆☆
Next day Jalila da Omar suka iso, sake zama akayi aka tattauna sosae. Kowa ya gamsu da kowa, kwanansu biyu suka juya, a ranar ma su Ummi suka koma saudia cike da kewar Hajja.

Rayuwa me dad'i Aman take, kowanme bangare kokarin bata kulawa yake, Abba na nan akan kudurinsa na son had'a Aman da Farhan. Sosae bakin Aman ya bud'e, duk maganar da Farhan ya fad'a mata tana maida masa daidai shi.. Duk after two week, tana zuwa mad'achi tayi weekends, Rahmata da Habu sun kulle da juna, Is'hu d'an k'walisa yana nan kara baza ra'ayinsa a kauyen.

Zabe yana ta matsowa, duk evidence komae Affan ya ajiye, zuciyar sa ta kasa tsaya masa waje d'aya, anyi primary election an tsaida Daddy takarar Governor, murna kamar me. Bangaren Nana da Farhan suna nan kamar dah, rabi hirar su akan Aman ce, tun tana jin haushi har ta hak'ura don bata ga alamar zae daena ba.

☆☆
Ranar wata saturday Affan ya shirya ya tafi kiru, mahaifar Daddy, ya sami yan uwansa ya sanar dasu yana son suje nemar masa aure, murna sukayi ganin ya girmamasu, don sam Daddy baya wani jansu ajiki, *Alk'awari* sukayi akan zasu zo sati na sama, da haka ya juyo bayan yayi cika musu aljihu da kud'i..

Yeeehooooo Na fara jiyo kamshin biki aradu, nice babbar kawa.. 💃🏻💃🏻💃🏻

I lurv u All my fans, rano na kaunar ku lodi lodi, bazan iya lissafa ku ba a wannan dan karamin page d'in, amma ina son ku sani, ina alfahari daku sosae.
Ur warm comments counts💞

Rano❣

ALK'AWARI BAYAN RAI (Completed✅)Où les histoires vivent. Découvrez maintenant