page 14

3.2K 249 2
                                    

'⋎´✫¸.•°*”˜˜”
..✫¸.•°*”˜˜”*°•.✫
☻/ღ˚•。*♥♥˚˚✰˚˛★*ღ˛°。*°♥。
/▌*˛˚˚.✰ •
/ ˚.★ *˛˚♥*✰。˚˚ღ。*˛˚♥。✰˚
        

                  ❣ *ALK'AWARI*❣
  _Bayan Rai_
     

~August 2017~

© *Hafsat Rano*

Edited by;
Miss xoxo👑

*Dedicated to* '''♡Anty Sis♡☆'''

☆☆☆☆☆♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡☆☆☆☆☆

           *14*
*mad'achi-Rano*

Wata mahaukaciyar yunwa ke addabar ta, gashi dae abinci sae ta xab'a amma sam babu kalar cimar ta a ciki. Rahmata ce ta shigo d'auke da k'warya guda d'aya an rufe sa ruf da murfin saki. Akan k'waryar ta dora wani kwano na langa wanda aka rufe  shi shima da murfin langar
Zama tayi gefen Aman wacce ke takure akan gadon k'arfe wanda aka shinfid'a masa tabarmar kaba. Kana ganinta kasan bata saba da yanayin ba sae dae ya ta iya?

"Sannun ki dai"Rahmata tace tana zama a gefen tabarmar dake ajiye a tsakar d'akin

Murmushi kawae Aman tayi ba tare da ta amsa sannun ba.

"Sauko kizo kisha Madara da duminta yanzu aka tatso ta"Ba musu ta zuru k'afafuwanta. Jan k'waryar tayi ta bud'e, madara ce lafiyayya da ludayi a ciki, kofi ta nemi a bata da sauri Rahmata ta jawo wani kofi akan sip d'in gaji ta girgije shi ta mik'a mata. Kwanon dake rufe ta bud'e mata, soyayyen k'wan zabi ne yasha albasa. Hamdala tayi ba shiri ta fara ci tana godiya ga Allah tana kuma jinjina karamci irin na mutanen.
Duk abinda suke Gaji na zaune tana yan addu'o inta, mace ce me tsantsani wajen rik'o da addini, duk da tawayar da take da ita hakan besa ta fitar da rai daka Rahmar Allah ba..

Tatas Aman ta shanye Madarar nan sannan ta cinye k'wan. Kuskure bakinta tayi sannan ta mik'e tabi bayan Rahmata wadda ta jiyo maganganun su a bakin turmi suna dakan Fura..

☆☆☆☆☆
A b'angaren Farhan da Nana kuwa duk inda ta ajiye k'afarta anan yake maida tasa, ganin bashi da niyyar daena binta yasa ta zarce gida, tana danna horn yana bayanta kamar tsohon maye, sae data gama parking d'inta sannan shima ya fito, tafia suke a jere kamar dama tare suke har cikin Parlon, ganin yana neman zak'ewa gashi bata son masa magana yasa taja ta tsaya ta shiga k'wala wa Ruth me aikin ta kira.
A guje Ruth ta fito ta zube gaban uwar d'akin nata..

Ganin Farhan yasa tasan mak'asudin kiran, ba bata lokaci ta cika gaban sa da kayan marmari sae ruwa da juice. Zama yayi a d'aya daka cikon kujerun parlon ya hard'e kafa yana kare ma parlon kallo.
Sae data gama yangar ta sannan ta fito lokacin har ta sanja shiga cikin wata gown maroon me dogon hannu.

Chan nesa dashi ta samu waje ta zauna, ta jawo remote ta shiga sanja tasha.
"How may i help U?!"Ta fad'a kamar bada shi take ba.

Daria taso ta bashi amma tunowar da yayi wannan shine oppurtunity nasa yasa shi gyara zama yana sipping tamarin juice

"Friendship! I just want us to be friends dats All"

"Ohh, friendship kake nema shine kake ta chasing nawa haka kamar na maka sata?"

"No ba haka bane, kece tun farko kika ki bani dama, ni kuma mutum ne me naci ma abinda naga yayi mun, abubuwa da yawa basu damen ba, infact bana ma da lokacin yan mata, but u in person naji kawae kinyi mun, kawae naji we have to be friends."

"Save the long Story, wannn bayanin sae ya sani headache, kawae kaje straight to the point." Ta fad'a tana cigaba da kallon Tv.

Kunya ce ta kamasa, Amma gaskia babe d'innan muguwar yar latsi ce. Hhhh
K'in magana yayi don a ganinsa ta gama dashi. Ganin ta mike tana alamun barin parlon yasa shi saurin katse ta.

"Am sorry bansan baki son surutu ba. Buh I ll take note"

Bud'e Dial pad d'inta tayi ta mik'a masa.
"Kasa digits naka"
Da sauri ya karb'a ya matsa number sa ya mik'a mata. Dialing tayi, jin ringing a aljihunsa yasa ta katse kirann
"Ga digits d'ina nan banda flashing, banda please call mie, just text mie duk time da kake son magana dani, i ll call"

"Jar Ubanchan." Lalle ma yarinyar nan yr latsi ce. Kafin yakai ga magana har ta shiga ciki.
Dafe goshin sa yayi yana wani shu'umin murmushi, ganin bata da niyyar fitowa ya sashi mik'ewa yaja yan matan k'afafuwansa yayi waje.

Yana shiga mota ya shiga danna mata kira, ringing d'aya kawae tayi ya kashe, haka yayi tayi har sae daya mata flashing sau 20 sannan ya kyale, shima don ya kira yaji switch off ne. Daria yayi yaja motar sa yayi gaba.
Koba komae itama yasan taji haushi.

☆☆☆
B'angaren Affan kuwa yana zaune shiru a d'aki yana tunanin Aman, marok'a ne a cikin gidan suna ta sana'ar tasu kasance war Daddy yana gari.
Jin an bud'e k'ofa yasa shi d'ago kansa.
Mummy ce d'auke da tray na abinci
"Affan ga abinci don nasan ba zuwa zakae kaci ba"Ajiye masa tayi a gabansa ta shiga serving nasa, murmushi kawae yake yana imagining life d'insa without her, Mummy uwa ce ta gari sae rashin sa'ar miji da tayi.
Sae data tabbatar ya ci sosae sannan suka shiga hira wadda duk rabi akan abinda ya faru ne. Kwantar ma juna hankali suke in da Mummy ta fad'a masa tasa ayi mata add'ua akan Nana, ta gaji da ganin ta haka dole ta d'au mataki. Na'am yayi da maganar sannan yayi addu'ar fatan alkhairi da samun Nasara.
"Affan son Aman kake ko?" Mummy ta jeho masa tambayar.

Sosa k'eya ya hau yi yana sunne kai. Murmushi tayi irin na manya. "Allah ya bayyanata", yarinyar tayi mun kuma ina matuk'ar sonta, jinta nake a raina sosae wlhi.
"Ba komai Mummy nasan ko ba dad'e ko ba jima zamu had'u, Kaddarar Allah ce ta had'amu tunda dah bamu san juna ba. Nayi *Alk'awari* ko  *bayan Raina* , zan zame mata komae na rayuwa, Mummy ki taimaka ki tayani cika wannan *Alk'awarin*"
"In sha Allah Affan. Allah ya taimaka."
"Ameen Ameen Mummy."

"Ya maganar Service naka kuwa? Lokaci yana tafiya."
"An yi posting nawa Ekiti, zanje nayi three weeks a Camp sae na nemi transfer zuwa north, san samu nama a barni a kano haka ko wani local government ne."
"Ok hakan yayi kyau, Kaga zakaji dad'in karatun, shisa lokacin da ka damu sae ka dawo bayan ka gama degree naka nace ka bari kai Masters , in ka dawo gaba d'aya kawae sae kayi service ka fara aiki."
"Eh wlhi Mummy, ai kin bada shawara me kyau, shisa nake k'ara sonki sosae."

Hira kamar bazata k'are ba, da kyar dai Mummy ta yak'ice ta fice don tasan Daddy daf yake da tashi daka barci.

Da yamma ya shirya cikin kaftan Dark Ash, hula da takalminsa sau ciki duk kalar aikin dake jikin Kaftan d'in. Ba k'aramin Kyau yayi ba, Affan kenan, simple guy with a simple life, kud'i da siyasa basu wani damesa ba. A kitchen ya tarar da Mummy cikin yan Aiki suna shirya Dinner.
"Zan d'an fita wasa kafa Mummy."
Tsaywa kallon sa tayi, godia kawae take ma Rabbil Izzati for this beautiful creature wai kuma d'anta ne da ya fito daka cikin ta.

"Allah ya kiyaye, Allah ya tsare. "
"Ameen Mummy."

Tafiya kawae yake a k'afa hannun sa rik'e da Ipad , da wayar sa. Kallon yanayin unguwar yake yana d'an tunanin Ta ina ma zae fara neman Aman. A daidaita sahu ya tsayar, Buk Old site ya umarce shi daya kaishi, direct Nugga Sport Field ya wuce ya tarar ana match tsakanin Yan Old site da New site. Kan wani block ya samu ya zauna yana kallon wasan gwanin ban sha'awa. Yana zaune har kusan magrib lokacin aka tashi daka wasan bayan Buk Old site ta cinye New site 5-0.. ( *Lol su o'o yan New site*😝😜).

Masallaci ya shiga yayi sallah magrib ya zauna jiran Isha, anan suka had'u da wani long time friend nasa aka shiga hira, sae da sukayi sallar Isha sannan yayi shirin tafiya gida..

Ya labarin Abby kuwa da Ummi? Yanayin cikar garin saboda yan aikin Hajji yasa na kasa zuwa na gani ya suke ciki😄

*Ba jan aji bane matsala ne yake damun wayana wlhi,  ta zama yar k'waya. Bear wit mie pls. K'awa and rest.*

Rano❣

ALK'AWARI BAYAN RAI (Completed✅)Where stories live. Discover now