'⋎´✫¸.•°*”˜˜”
..✫¸.•°*”˜˜”*°•.✫
☻/ღ˚•。*♥♥˚˚✰˚˛★*ღ˛°。*°♥。
/▌*˛˚˚.✰ •
/ ˚.★ *˛˚♥*✰。˚˚ღ。*˛˚♥。✰˚
❣ *ALK'AWARI*❣
_Bayan Rai_
~August 2017~
© *Hafsat Rano*
*Dedicated to* '''♡Anty Sis♡☆'''
_Vote and Follow mie on wattpad @HafsatRano, My facebook page @Rano Online Novels_
This page is for U Senior Sis *Fateema Kabeer Umar* Allah ya k'ara girma.
Aunty nah, Aunty Sis Allah ya baki lafia. Allah ya raya bby boy.
☆☆☆☆☆♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡☆☆☆☆
*54*
Dishi dishi take gani, lokacin da take kokarin bud'e idonta wanda sukayi mata nauyi, kwance take a gadon asibiti, Mama ce gefenta ganin tana kokarin tashi ne yasa ta ruko hannun ta,
"Amaan..! Ta kira sunanta, kallon Mama kawae take tana k'arema d'akin kallo, cikin dakik'a da bata fi uku ba abinda ya faru ya shiga yawo mata a k'wak'walwa. Wani irin kuka ta fashe dashi da sauri ta mik'e tana k'okarin zare drip dake hannun ta.
"Affan.. Affaan.. " ta shiga furtawa da karfi, rik'e ta mama tayi k'ak'am tana hawaye,
"Da gaske Affan d'ina ya rasu Mama? Da gaske ne?" kasa magana Mama tayi sae ma kokarin sake rikota da take. A haka Dr ya shigo ya samesu. Kuka kawae take tana kiran Affan, ita kawae akaita taga Affan, ganin haka yasa Dr kawae ya rubuta mata magunguna yayi discharging d'insu.
☆☆
Tun da suka shiga mota take kuka kamar ranta zae fita, Farhan dake driving shi kansa zuciyar sa tayi rauni sosae, ya tausaya ma Amaan don ba karamin rashi tayi ba.Tun da suka shigo link d'in gidan Mummy jik'in Amaan ya k'ara rawa, mutane ne tun daga farkon layin xuwa karshe, yan jarida kam abun ba'a cewa komae,. Daddy tare da wasu yan sanda ma sun iso, kallo d'aya xaka yi masa kasan yana cikin tashin hankali, kuka kawai yake yana danasanin rayuwar sa. Babu wanda ya tausaya masa don labari ya gama karad'e ko ina, sai ma yan jarida dake ta faman son suji ta bakin sa.
Kamar wata zararriya take bin mutanen da kallo har suka samu suka isa k'ofar gidan, hannun ta Mama ta kama ganin sam bata cikin hayyacin ta, a harabar gidan suka fara tarar da mutane, suna ganin Amaan suka shiga tausaya mata. Chan cikin bedroom d'in Mummy suka nufa still hannun Mama na cikin nata wanda take binta kamar jela tana kallon mutane.
Suna shiga d'akin ya k'ara rikicewa, idanun Mummy kamar gauta, hannun ta rik'e da charbi tana ja, a hankali a hankali tana share hawaye. Gefenta Nana ce itama cikin hijabin ba abinda take sae kuka. Gefen Mummyn Amaan ta zauna tana bin kowa na d'akin jin yadda suke mata gaisuwa. Ko d'aya bata amsa musu ba sae ma kallon rashin fahimta da take binsu dashi.
Suna nan zaune Kawu na k'iru yayi sallama abakin d'akin,
"An gama had'a shi kuxo kuyi masa addu'a.." Be jira amsar su ba ya wuce. Da kyar Mummy ta iya mik'ewa ta kamo hannun Amaan suke fita zuwa in da aka ajiye Affaan.
A hankali Mummy tasa hannu ta bud'e fuskar sa wadda ta rage baa rufe ba, wani kuka ne ya kwache mata ganin Affan d'inta kwance cikin Fararen kaya kamar zaka kirashi ya amsa,
Kawu dake tsaye gefe ya matsa kusa da ita, yace;
"Kiyi masa Addu'ah kinji.."
Gid'a kanta tayi kamar wata zararriya tace;
"Allah ya jik'anka Affaan, Allah ya gafarta maka, Allah ya jik'anka Affan..." kuka ne yaci karfin ta, ta
mik'e da sauri ta fita daka d'akin tana shasshek'a.Bin ta Amaan tayi da kallo sannan ta dawo da kallon ta kan gawar. Wani irin d'aci take ji a mak'ogaronta, kallon sa kawai take ta kasa koda k'wakk'waran motsi, ganin kamar ba a hayyacin ta ba yasa Kawu kiran Nana yasa ta rik'e hannun ta ta fitar da ita.
Waje aka fitar dashi akayi masa Sallah had'e da kai shi gidan sa na Gaskia. Allahu Akbar, Allah yasa mu cika da Imani ameenn..
☆☆☆
Rahmata, Nafi, Ishu da mutanen Mad'achi duk sun xo gaisuwa, Habu ma yazo cikin tashin hankali, sunyi kuka sosae kowa yana yabon halin k'warai irin na Affaan.Bayan k'wana uku su Ummy suka dira a Nigeria, mummunan labarin mutuwar Affaan ita suka fara riska in da suka ji mutuwar tasa sosae.
Ganin yanayin da Amaan take ciki ba k'aramin d'aga musu hankali yayi ba, kwata kwata bata magana da kowa sae kallo kawae da ido, duk abinda aka ce mata sae dai tabi mutum da kallo, abinci ma sae an matsa mata take samu tasha ruwan tea.
Ranar da Jalila da Omar suka iso ranar Amaan ta samu tayi kuka me tsuma zuciya, babu wanda ya hanata don shi kansa rashin kukan nata wata matsala ce.
Fav. Uncle ma kullum yana zuwa yana k'wantar mata da hankali, shirye shiryen komawa yake kuma a yadda ya tsara tare da Farhan da Amaan zasu koma, tausayin Mummy ne kawae yasa yayi delay na tafiar tasu.
☆☆
Bayan anyi arba'in ne Fav. Uncle ya bullo da maganar son tafiyar da yake da Amaan, Hajja da su Abba sun goya masa baya, takanas suka je gidan Mummyn saboda sanar da ita tare da kwantar mata da hankali.Da fara'a Mummy ta tarbe su, duk da ganin su haka ta tabbatar akan Amaan ne,
"Ammm Hajiya in bazaki damu ba..." Abba ya shiga furtawa kansa kasa, wani irin fad'uwa gaban Mummy yayi ,
"Muna son tafia da Amaan, amma ba chan gdan namu zata zauna ba, mahaifin ta keson tafiya da ita. Amma kiy hak'uri. Shiru Mummy tayi bayan wata k'walla me dumi ta sauko mata, a take mutuwar Affan ta dawo mata sabuwa fil. Ban baki da ban hak'uri suka shiga bata daga karshe ta hak'ura akan ana gobe tafiyar Amaan zata koma.
☆☆
Amaan k'wance akan gado bayan su Abba sun tafi, Nana na gaban wardrobe tana gyara kayan ciki.Juyowa tayi ta kalli Amaan wanda tayi nisa cikin tunani, cike da tausaya wa da dawo gaban gadon, hannayen ta ta kama cikin nata,
"Kukan nan ya isa haka Amaan, bruh baya buk'atar komi kamar addu'ah a halin ynxu."
Bayan hannun ta tasa ta goge hawayen sannan ta wuce xuwa bathroom d'on d'auro alwala.
Bayan sun idar da sallah Nana ta kawo musu abinci, d'an chakala kawai tayi ta koma kan gado ta sake k'wancia.
☆☆
Ignore any typing error, i jst manage to typ for u guys.. Lurv U all.Include mie in ur prayers
Rano💞
KAMU SEDANG MEMBACA
ALK'AWARI BAYAN RAI (Completed✅)
Fiksi UmumA story of a young girl who sees the bad side of the world from both angle.. Suddenly an angel came to her rescue.. Destiny will take it place.. Will he be able to rescue her? find out in this astonishing story