'⋎´✫¸.•°*”˜˜”
..✫¸.•°*”˜˜”*°•.✫
☻/ღ˚•。*♥♥˚˚✰˚˛★*ღ˛°。*°♥。
/▌*˛˚˚.✰ •
/ ˚.★ *˛˚♥*✰。˚˚ღ。*˛˚♥。✰˚
❣ *ALK'AWARI*❣
_Bayan Rai_
~August 2017~
© *Hafsat Rano*
Edited by; Miss Xoxo👑
*Dedicated to* '''♡Anty Sis♡☆'''
'''Ina zaune a bank sanyin AC yana kad'ani, tunanin swt Affan ne ya fad'o mun, ya kamata na lek'a naga ya ake ciki da shagalin biki. Amma fa masoyan Farhan kuyi hakuri dani don kam heart attack na gaf da kamasa'''🏃🏿♀🏃🏿♀🙊🙊💃🏻💃🏻💃🏻
☆☆☆☆☆♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡☆☆☆☆☆
*40*
Aman zaune kusa da Umminta Jalila, waya take kasa kasa da Affan, wata mata ta shigo d'akin,"Taso muje Aman, Farida na chan tana jira." Had'e rai tayi don ita sam bata son wannan gyaran jikin, ta cigaba da wayarta tana d'aga mata hannu alamar tayi shiru, kamar ingiza Jalila tayi ta shiga magana;
"Na rasa mesa baki son gyaran jikin nan Aman, its for ur own good kuma." Da sauri ta toshe bakin ta alamar bata son Affan yaji,
"Bby me naji Ummi tana fad'a ne wai??" Ya tambaya yana daria kasa kasa,
"Bakomae." Ta amsa da sauri tana mik'ewa.
"Umm kamar gaske, pls kice ayi gyaran nan sosae zan bada tukwuici." Da sauri tayi hanging wayar tana buga kafa,"Kinga ko Ummi, yanzu shikenan Affan yaji fa." Juyawa tayi tabi bayan matar Jalila nata daria a hankali, komae yana tafia yadda take so, gata ga yarta abar sonta, matsalar d'aya taso ace ba aure tayi soon haka ba ta tafi da ita Malaysia su kara sanin juna, amma kuma ba yadda ta iya tunda dai ta riga ta sami farin ciki.
Text message ne ya shigo wayar,_"Pls Bby ki tsaya ayi gyaran jikin nan fa, umm har na hangoki, i will lurv it_."
Murmushi ne ya subuce mata, duk abinda take Farida na kallon ta, tabe baki tayi tace,
"Kwana nawa ne mutum in yayi hak'uri ma,sae wani farin ciki ake." Kallon ta Aman tayi da sauri, d'auke kanta tayi kamar bada ita take ba, murmushin ta karayi ta cigaba da danna wayarta.
☆☆☆
Next day thursday aka fara events, Kamu aka shirya na gani na fad'a, wani bangare daka bangaren gidan daya kasance katoton gaske aka shirya akayi ma decoration, kujeru ne had'addu na alfarma tare da round tables. yanmatan Amarya sunyi kyau cikin material Orange and black, suko amaren pink and Ash suka sa iri d'aya, manyan manyan yan kasuwa da masu kud'i ne ke juyi ko ta ina, Rahmata da Nafi ma sunyi kyau abunsu. Hajja kam baa magana ansha lace d'an ubansu d'inkin nan me B-curve. Anyi event lafia an gama, wanda anan aka yi introducing Aman a wajen family friends nasu. Nana ma ba'a barta a baya ba, tayi kyau sosae har ta gaji da had'uwa, Hany na gefe tana murmushin yak'e. Tun daka nesa Na'eem ke kallon su, ganin su a gefe sunk'i shiga cikin yanmatan amarya, wajen su ya karasa yana murmushi, gaisawa sukayi da Nana cikin sakin fuska, kamar ta tambaye shi Farhan sae kawae ta fasa, wuce su yayi yaje sukayi pics da amaren sannan ya nufi part d'insuFarhan yana kwance a d'aki duk one beat na speakers d'in jinsu yake kamar a cikin zuciyar sa ake bugawa, yaye curtain d'in d'akin yayi yana lek'en wajen event d'in, hango Aman yayi tana ta blushing, fuskar nan ta ta kamar farin wata don haske, yana nan tsaye Affan da yan tsirarun abokansa suka karaso don d'aukar pics, wani abu me kamar kaho ne yaji ya tok'are sa, a hanzarce ya jawo troly d'insa ya shiga had'a kaya da sauri yana rik'e da kansa, Na'eem ne ya shigo ganin abinda yake yasashi karasawa wajen sa da sauri,
"Wat are u trying to do bruh?" Ya tambaya yana kokarin d'auke jakar daka gaban sa, durkushe wa kawae yayi yana jin hawaye me zafi yana sakkowa, duk dauriyar Farhan ranar sae ya kasa controling kansa, rik'o shi Na'eem yayi yana buga bayansa,
"U hav to be strong bruh, u have to b, be kamata kasa kanka a wannan yanayin ba, beside kana da right na samun abinda kake so, amma why kake hurtng kanka haka? Why?""Bazan iya ba Na'eem, Abba ya kawo k'wakk'waran hujjojinsa, i cant go against his words, tafiya kawae zan, I ll hav to leave, far away from here." Tapping bayansa kawae Na'eem yake yana jin mugun tausayin d'an uwansa, fita yayi ya duba ko ina, ganin babu wani ido a waje yasa shi dawowa da sauri, ya rik'e hannun sa suka fito, mota yasa shi yaja ya bar unguwar, wani karamin gida a cikin gidajensu ya kaishi, ruwa me sanyi ya bashi yayi calming nasa da maganganu masu sanyi sannan ya tafi ya barshi yana kudurce wa a ransa na ganin ya ceto d'an uwansa daka wannan masifar.
☆☆☆
Washegarin rana wanda ya kama saturday akayi Mothers Eve, Hajja an baza raayi iyakar bazawa😅, rabo kawae take na atampopi da lace lace, yan Kurfi sun kwashi rabonsu, gefe na hango fans d'in Affan da Aman suna ta kwasar gara, wasu harda masu karbar abubuwa sau biyu irinsu o'oh, harkar girma kawae take a matsayin ta na mahaifiyar *Millionaire Abduljalal Kurfi*.. Su Ummi da sauran yan uwansu sun jinjina aure irin na Nigeria, abun ya matukar burgesu, sun shirya ma amaren Arabian night washegarin da aka kaisu gidajen mijinsu.*Wedding bells*💃🏻💃🏻💃🏻
Cikin shigar shadda Fara k'al Affan ya fito, gaba d'aya gida ya kaure da gud'a, murmushi kawae yake yana wucewa har ya kai gaban Mummy dake tsaye tana bada order, tana ganin sa ta sallami masu aikin ta wuce gaba yana binta abaya, zama tayi shi kuma ya tsuguna har kasa yana jin wata masifar kunyar ta,
"Girma yazo maka Affan, girma me wahala, sae ka daure ka jajirce kaji tsoron Allah,ka rik'e amana, ka....... Nasiha sosae tayi mishi me kashe jiki duk akan rayuwar aure, yana tsugunne har ta gama, wata nutsuwa sosae yakeji tana shigarsa, no one like mom a duk duniyar nan, dafa kansa tayi ta sa masa albarka sannan ya fito zuwa wajen abokansa, tsokanar sa suka shiga yi yana daria, daka karshe suka shiga motoci suka nufi wajen d'aurin auren...*Ignore any error. Dnt frgt to includ mie in ur pryes*
Manage pls 🙏🏻....
YOU ARE READING
ALK'AWARI BAYAN RAI (Completed✅)
General FictionA story of a young girl who sees the bad side of the world from both angle.. Suddenly an angel came to her rescue.. Destiny will take it place.. Will he be able to rescue her? find out in this astonishing story